30 January 2018: Tunawa da zaluncin da akaiwa Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata gareta wacce itace farko wacce ta fara riskar manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata gareshi tare da-alkalamin sayyid Adil-Alawi

Zaluntar sayyada Zahara (as) tare da alkalamin sayyid Adil Alawi(h)
الحديث : أمالي شيخنا المفيد 1 بسنده قال : «لمّا حضر النبي 6 الوفاة بكى حتّى بلّت دموعه لحيته ، فقيل يا رسول الله ما يبكيک؟ فقال : أبكي لذريّتي وما تصنع بهم شرار أُمّتي من بعدي ، كإنّي بفاطمة بنتي ، وقد ظلمت بعدي ، وهي تنادي يا أبتاه يا أبتاه ، فلا يعينها أحد من أُمّتي ، فسمعت ذلک فاطمة فبكت ، فقال لها رسول الله 6 لا تبكين يا بنيّة ، فقالت لست أبكي لما يصنع بي من بعدک ، ولكن أبكي لفراقک يا رسول الله، فقال لها: أبشري يا بنت محمّد بسرعة اللّحاق بي ، فإنّک أوّل من يلحق بي من أهل بيتي
Daga littafin Amali mufid da sanadinsa ya ce: yayin da wafatin ya halartowa annabi (s.a.w) ya fashe da kuka har sai da hawaye ya jike gemunsa, sai aka tambaye shi aka ce ya manzon Allah (s.a.w) mene ne ya sanyaka kuka? Sai ya ce: ina kuka ne saboda zuriya da abin da ashararan cikin al’ummata zasu aikata kansu bayan wafatina, kai kace ina ganin `yata Fatima gabana an zalunceta bayana tana halin kira ya babana ya babana, babu wani daga cikin al’ummata da yake kai mata `dauki, sai Fatima ta ji wannan magana sai ta fashe da kuka, sai manzon Allah ya ce: kada kiyi kuka yake `yar karamar `yata, sai tace bana kuka kan abin da za a aikata kaina bayanka sai dai cewa ina kuka ne kan rabuwa da kai ya manzon Allah, kiyi bushara yake `yar Muhammad cikin gaggawa zaki riskeni, lallai ke ce ta farkon wacce zata fara riskata. ... cigaba Labare daban-daban

6 January 2018: Mujallar kausar adadi na 33 ta samu fitowa

1-Kalmarmu.

2-rumbun sakafa
3-wani daga siffofin annabi cikin kur’ani- tare da alkalamin 4-Rahim umid
5- halifan Allah-tare da alkalamin sayyid Adil-Alawi.
6- halifanci na Allah asali daga asalan addini-tare da sayyid Muhamad Husaini Musawi.
7-daga wa’azuzzukan annabi-tare da sayyid Ali kamna’i
8-mashahadin husaini da ingantaccen take-tare da sayyid Muhammad rida jalali ... cigaba Labare daban-daban

1 January 1970: Shin lazimtar wasu ba’arin Azkaru ba tareda ƙayyade adadi da niyyar samun biyan bukata keɓantacciya shi yafi ko kuma ƙayyadewa da ciyakance adadi?

Salamu Alaikum samahatus Sayyid
Bayan addu’a gareku da neman Allah ya tsayanta rayuwarku ina son Akaramakallahu ya bayyana mini shin lazimtuwa kan wasu ba’arin Azkaru ba tareda iyakance adadi ba da niyyar neman biyan bukata keɓantacciya shi yafi ko kuma kayyadewa da iyakance adadi? Idan ya kasance yin wani adadi shi ake bukata shin rashin iyakance adadin yana da wani tasiri mai kyau ko mara kyau.
Tambaya ta biyu: akwai wasu Azkaru da nake lazimtuwa kansu kowanne lokaci ina son in san ra’ayinku kan waɗannan Azkaru misali yin salati ga muhammad da iyalensa, sai kuma zikirin ya Allahu ya huwa, da zikirin ya wahhabu da istigfari ... cigaba Labare daban-daban

1 January 1970: Ta ƙaƙa za mu iya karɓa ko dogaro da masdarin hadisi tareda cewa kwafin asalin masdarin wasu ba’arin malamanmu sun karɓe shi ne da kyautata tsammani ba tareda sun san asalin marawaicin hadisin ba ku sun taɓa ganinsa

Salamu Alaikum samahatus Sayyid mubarak ustaz sayyid Adil-Alawi
Ta yaya zamu iya karɓa ko dogaro da masdarin hadisi tareda cewa asalin masdarin wannan hadisi malamanmu sun karɓe shine kyautata tsammani ba tareda sun san asalin marawaicin ba, misali littafin uyunul mu’ujizat wanda ake danganta shi ga shaik Husaini Abdul-wahab, wannan littafi daya daga masdaran da mai littafin biharul Anwar ya dogara da su ne sannan ga littafin nan an buga a yanzu cikin mujalladai bakwai tareda cewa hatta shi kansa Allama majalisi mawallafin littafin biharaul Anwar bai san wane ne takaimaiman mawallafin littafin uyunul mu’ujizat ba, amma tareda haka munga wasu ba’arin malamanmu Allah ya ƙara musu yarda suna dogaro da ba’arin wasu abubuwa da suke cikinsa, saboda haka me su Akramakallahu zasu ce kan wannan al’amari? ... cigaba Labare daban-daban

1 January 1970: Ku tashi tsaye domin Allah

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Lallai sharadin jarraba zurfin dukkanin iliman dan Adam, ilimi da Akhlak….Shi ne sanin daidaikunsa da dokokinsa, shi ilimn Akhlak shi daya daga cikin wadannan iliman ne wadanda suke kebantar janibin ma'anawi cikin `yan Adamtakar mutum, ... cigaba Labare daban-daban

1 January 1970: Jarrabawar Allah mai girma da `daukaka ga wasiyyan annabawa cikin rayuwar annabawa (as)

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

حدثنا أبي ومحمد بن الحسن (رضي الله عنهما) قالا: حدثنا سعد بن عبد الله قال: حدثنا أحمد بن الحسين بن سعيد قال: حدثني جعفر بن محمد النوفلي، عن يعقوب بن يزيد قال: قال أبو عبد الله جعفر بن أحمد بن محمد بن عيسى بن محمد بن علي بن عبد الله بن جعفر بن أبي طالب قال: حدثنا يعقوب بن عبد الله الكوفي قال: حدثنا موسى بن عبيدة، عن عمرو بن أبي المقدام، عن أبي إسحاق، عن الحارث، عن محمد بن الحنفية «رضي الله عنه»، وعمرو بن أبي المقدام، عن جابر الجعفي، عن أبي جعفر قال:
أتى رأس اليهود علي بن أبي طالب× عند منصرفه عن وقعة النهروان، وهو جالس في مسجد الكوفة، فقال:
يا أمير المؤمنين، إني أريد أن أسألك عن أشياء لا يعلمها إلا نبي أو وصي نبي.
قال: سل عما بدا لك يا أخا اليهود؟
Babana da Muhammad bn Hassan (rd) sun zantar da ni sun ce Ahmad bn Husaini bn Sa’id ya ce: Jafar bn Muhammad naufali ya zantar dani daga Yakub bn Yazid ya ce: Abu Abdullah Jafar bn Muhammmad Isa bn Muhammad bn Ali bn Abdullah bn Jafar bn Abu dalib ya ce: Yakub bn Abdullah kufi ya ce: Musa bn ubaida ya zantar da mu daga Amru bn Abu Mikdam daga Abu is’haku daga Harisu daga Muhammad bn hanafiya (rd) da Amru bn Abi: jagoran yahudawa ya je wajen Ali lokacin da yake juyawa daga yakin naharawan lokacin da yake zaune cikin masallacin kufa sai wannan bayahude ya ce ni ina son tambayarka wasu abubuwa da babu wanda ya sansu sai annabi ko wasiyinsa, sai ya ce masa: tambayi abin da kake son tambaya ya kai dan’uwa bayahude? ... cigaba Labare daban-daban

1 January 1970: Sakon ziyarar arba’in cikin iraki-tattaunawa tare da samahatus sayyid Sami badari.

Yaya zaku kimanta sakon ziyarar arab’ain?

Amsa: a hakikashekara bayan shekara wannan ziyara tana ta kara habbaka al’umma suna motsi da dukkanin samuwarsu, lokacin da kaso mafi tsoka ya kasance ga irakawa cikin wannan ziyara wannan wani fifiko ne kebantacce, bushara ta kusanto ga irakawa ga galibin wannan al’umma ta iraki wadanda suke fuskanto husaini (as) cikin godiyar Allah wannan ziyara bata takaitu ba ga iya shi’a kadai ba yanzu ahlus’sunna masu yawan gaske sun fara fahimtar wannan ziyara ta arba’in kai hatta wadanda ba musulmi ba sun fara rungumar wannan ziyara mai albarka, wannan ziyara ta zama wani lamini ga sake gina ba irake da dukkanin al’ummar araki gini kan hanyar husaini (as) na haifar da ruhi mabayyani, na’am wani akanyi tsokacikan wasu ayyukan masu ziyara daga samari da wasunsu wadanda wadannan ayyukan basu dace da wannan biki na husaini ba, to ina cewa: ku dan jirace su zuwa shekara mai zuwa, lallai akwai wata habbaka da cigaba mai zurfi cikin al’ummar ballantana na ma jama’ar shi’a wadanda suke zuwa daga sassan duniya. ... cigaba Labare daban-daban
اَللّهُمَّ کُنْ لِوَلِیِّکَ الْحُجَّةِ بْنِ الْحَسَنِ صَلَواتُکَ عَلَیْهِ وَعَلى آبائِهِ فی هذِهِ السّاعَةِ وَفی کُلِّ ساعَةٍ وَلِیّاً وَحافِظاً وَقائِداً وَناصِراً وَدَلیلاً وَعَیْناً حَتّى تُسْکِنَهُ أَرْضَکَ طَوْعاً وَتُمَتِّعَهُ فیها طَویلاً
gurin daya kunshi abubuwa daban-dan Fayal-fayal na karshe na ji da gani
Fayal-fayal din da akafi budewa
Wasu fayal-fayal
Hutona