lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Muna ta’aziyya ga daukacin al’ummar musulmi bisa munasabar tunawa da wafatin sayyada Fatima `yar imam Musa Alkazim (as) wacce akewa alkunya da (ma’asuma) amincin Allah ya kara tabbata gare ta.

 

1-kadai dai ta cimma wannan mukami madaukaki da wannan matsayi mai daukaka cikin gidaje da Allah ya yi izinin `daga su a wajan Allah da manzon Allah da zuriyarsa tsarkaka masu shiryarwa sakamakon ma’arifarta da iliminta  da kariyarta mai tsarki ga alfarmar wilaya, da narkewa cikin sha’anin Allah cikin mukamin wilaya da halfancin mafi girma da take misaltuwa cikin imamin zamaninta `dan’uwanta imam rida (as) da kuma cewa lallai ita tana kamanceceniya da `yar;uwarta sayyada Zainabul kubra cikin bada gudummawa ga yunkurin `dan’uwanta shugaban shahidai Husaini bn Ali (as) haka lallai iata tana kamanceceniya da babarta Fatimatul zahara cikin girmanta da tsarkakuwarta da kyawunta da kamalarta, mene ne yafi kyawu daga abin da imam komaini yake fadi cikin darajarta da falalarta da mukaminta mai girma zan kawo muku tarjamar ba’arin baitocin da ya raira, yana cewa: hasken Allah ya yi tajalli- hasken sammai da kasa – cikin manzon Allah (s.a.w) sannan sarkin muminai ya yi tajalli cikinsa zakin Allah mai kai bara (as) sannan ya bayyana cikin Fatima, sannan ya yi tajalli cikin Fatima ma’asuma `yar Musal Alkazim ibn Jafar (as) kadai dai duniyar imkani ta kasantu a hakika da wannan haske, ba da ban shi ba da dukkaninsa ya kasance karya, zamani bai samar misalin wadannan mata biyu ba Fatimatul zahara da Fatima ma’asuma zahara ita ce mafarar kumfar ilimi, sannan `diyar Musa Alkazim tushen kumfar hakuri, waccan ta kasance kambun sarauta kan kawunan annabawa, ita kuma wannan kasance garkuwar waliyyai, sannan waccan ta kasance ka’abar duniyar girmama, wannan na bayyanar da mulkin girma, kai ba da ban fadin Allah madaukaki (bai haifa ba kuma ba a haife shi ba) ya yiwa bakina takunkumi ba da nace Fatimatu zahara da Fatima ma’asuma `ya`yan Allah ne, waccan Zahara sarauniyar kan mulkin mara gushewa, wannan kuma Fatima ma’asuma sarauniya ce kan al’arshi girma, waccan ita ce ta kayata birnin madina munawwara, wannan kuma ta haskaka kasar Qum mai tsarki wannan ta sanya turbayar kasar Qum cikin daukakar aljanna, waccan ta sanya ruwan madina matsayin kausara, waccan kuma ta sanya ruwan ta lullube aljannonin kasar Qum daga gareta ne aljanna take.

2- kadai dai ana sanin girman sayyada da girmamarta karkashin nassoshi da suka kan hakkinnta daga A’imma ma’asumai (as) kamar misalign fadin kakanta imam Sadik (as)   

«بضعة منّي من زارها وجبت له الجنّة»،

Tsoka daga gare ni duk wanda ya ziyarce ta aljanna ta wajaba gare shi.

Haka ma kamar misalin fadin imam Musa Alkazim (as)

«فداها أبوها»،

Babanta ya fansheta da ransa.

Haka ma fadin `dan’uwanta Rida (as)

 «من زارها كمن زارني»

Duk wanda ya ziyarceta kamar ya ziyarce ni ne.

Da fadin `dan `dan’uwanta imam Jawad (as)

«من زار عمّتي وجبت له الجنّة».

Dukkanin wanda ya ziyarci gwaggona aljanna ta wajaba gare shi

Dukkanin wadannan maganganu misalinsu ya zo cikin shugaban matan farko da matan karshe Fatima zahara tabbas ita tsokar manzon Allah (s.a.w) ce kuma ya fanshe ta da ransa kuma duk wanda ya ziyarce ta aljanna ta wajaba gare shi.

3- abin da ya gangaro game da sananniyar ziyararta  da ta zo daga imam Rida (as) da sasabawar tasbihinta  cikin farkon ziyarar ta re da tasbihin babarta Fatima zahara (as) da gabatar da fadin (subhanallah) kan fadin (Alhamdulillah)  bayan gabatar da kabbara, a nazarina banbanci yana bayyanuwa cikin wannan mukami tsakankanin tasbihan guda biyu na zahara da Fatima ma’asuma, cewa cikin tasbihin Fatima ma’asuma mai ziyara zai fara da yin kabbara (Allahu akbar) sau 34 bayan bismillah da ambatonsa da kuma cewa shi Allah shi ne mai girma madaukaki, bayan nan kuma ka da yayi guluwi lokacin da yake karanta abin da ke cikin ziyara  yana shaida girma da siffofi madaukaka, sai yya yi kabbara  ga Allah madaukakin sarki matsarkaki har ya san cewa wannan mukamai da masaukai na waliyyai da zababbun bayinsa dukkaninsu kadai dai daga girman Allah wanda girmansa ya girmama, lallai shi ne mai girma madaukaki daga abin da suke siffantawa. sannan daga ma’alul ne ake isuwa zuwa ga illa daga babin (burhanul inni) ma’ana sai ka fara ganin hasken rana kake kaiwa ga yakinin hudowar rana haka kashin rakuma ke nusantar da kai zuwa ga giftawar rakumi, haka daga yawa ake tsallakawa zuwa ga dayantuwa, daga siffar korewa ake tukewa ga siffar tabbatuwa, haka ma zai fara tafiya daga halittu zuwa gaskiya tare da gaskiya, daga girma da sanin girmama zuwa ga kyawu  da sanin kyawunta, sai ya fara  da tasbihin (subhanallah) kafa 33 ya tsarkake ubangijin talikai daga dukkanin tawaya da nakasa kamar yadda suke a cikin halittun Allah, (sabuhun kuddusun)  shi Allah shi mudlakul kamal kuma shi ne kamalul mudlak, wamda ya tattaro dukkanin siffofin kamala dayantacce daya babu wani abu kwatankwacinsa, sannan ya isu da ma’arifarsa zuwa ga  wannan kyawun nasa mudlaki lallai shi ne wanda ya cancanci dukkanin yabo da godiya sai ya fadi (Alhamdulillah) kafa 33 dukkanin godiya ta fuskanin gamewa ga Allah matsarkaki… amma cikin tasbihin Fatima zahara bayan kabbara yana farawa ne da fadin (Alhamdulillah) kafa 33 sannan tasbihi (subahanallah) kafa 33  ma’ana tafiya daga gaskiya zuwa halittu tare da gaskiya daga dayantuwa zuwa yawaituwa daga babin (burhanul lummi) sanin ma’alul ta hanyar illa, wannan sirri da wannan ishara ta irfani sun wadatar ga wanda ya kasance daga Ahlinsu.

4- daga cikin hakkin Fatima ma’suma nuna mata soyayya, lallai ita tana daga makusantan manzon Allah (s.a.w) ya kamata a nuna mata soyayya a karramata a girmamata a raya haraminta da kabarinta madaukaki a taimaketa a kowanne muhalli  

قال رسول الله|: «إنّي شافع يوم القيامة لأربعة أصناف ولو جاءوا بذنوب أهل الدنيا: رجلٌ نصر ذرّيتي، ورجل بذل ماله لذرّيتي عند الضيق، ورجلٌ أحبّ ذرّيتي باللسان والقلب، ورجلٌ سعى في حوائج ذرّيتي إذا طردوا أو شرّدوا»

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: tabbas ni mai ceton mutane hudu ne ranar kiyama ko da kuwa sun zo da zunubin dukkanin mutane duniya: na farko shi ne mutumin da ya taimaki zuriya, da mutumin da ya sadaukar da dukiyarsa saboda zuriyata lokacin kuntata, da mutumin da ya so zuriyta da harshe da zuciya, da mutumin da fafutika cikin biyan bukataun zuriyata yayin da aka kore su ko akai wurgi da su

5-ismarta ta aiki, da wannan take kasantuwa abar koyi da kwaikwayo cikin sairi da suluki zuwa ga Allah matsarkaki.

6- imani da cetonta gamamme da kebantacce, tabbas za ta ceci dukkanin mutane da yardar Allah matsarkaki

«مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إلاَّ بِإذْنِهِ»

Wane ne wanda yake ceto a wurinsa face da izininsa.

Lallai ziyararta tana jawo cetonta, kadai manzo da wasiyyi da malami da shahidi ke yin ceto, kuma sayyaa tana dauke da wadannan siffofi, lallai ita daga gidan wahayi da annabta da ma’adanar ilimi da imamanci ta fito

قال الإمام الصادق×: «تدخل بشفاعتها شيعتنا الجنّة بأجمعهم».

Imam Sadik (as) ya ce: za ta shigar da baki dayan shi’arta aljanna da cetonta.

7- tabbas tana da wani mukami a wurin Allah daga cikin mukamai yanda yake ga manzo da tsatsonsa (as) shi ne ilimin ladunni (ilimi daga Allah) tana kuma da ilimin ilhama wanda yake yana daga kasha-kashen ilimin ilhama, lallai ita tana daga marawaitana hadisai madaukaka, lallai iata tana daga magadan annabawa da wasiyyai.

8- kiyaye ladubba halarta da kamewa daga `daga murya, kamar yadda ba ‘a `daga murya a halarar manzon Allah (s.a.w) a lokacin da yake raye haka ma a kabarinsa.

9- kada mai ziyara ya cutar da ita da munana ladabi da aikata zunubi  

قال رسول الله|: «والله لا تشفّعت في مَن آذى ذرّيتي».

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: wallahi ba zan ceci wanda ya cutar da zuriyata ba.

10- ziyartarta tana daidai da aljanna kamar yadda ziyarar ma’asumai ta kasance saboda ziyararsu it ace ziyarar Allah, liyafarsa cikin al’arshinsa kadai dai liyafarsa ce cikin sunayaensa kyawawa da madaukakan siffofinsa kan teburin walimar irfani da ruhaniyanci daga iliman kur’ani  mai girma da sunna madaukakiya.

11- hakika ya zo cikin madaukakin hadisi cewa lallai birnin Qum mai tsarki wata sheka ce ta alu Muhammad, ita kuma mafakar fadimawa ce da alawiyyawa da shi’ar sarkin muminai Ali (as) babu wani jabberi da ya nufe ta da sharri face ya halaka, lallai daga cikin hauzarta malamai ke filfilawa zuwa ga saman falaloli da da darajoji da karamomi.

Suna yada ilimi gabas da yamma, hakika birnin Qum kafin bayyanar hujjatul muntazar (as) za ta kasance hujja kan mutane kamar yadda ya zo cikin madaukakin hadisi, duka wannan na daga albarkar sayyada ma’asuma, kamar yanda ya zo cikin ziyararta da ake faraway da ziyartar annabawan Allah ulil azmi daga cikinsu  sannan a gangaro kan A’imma tsarkaka don a yiwa mai ziyara ishara cewa ita Qum shekar annabawa da wasiyyai baki dayansu abin da ke misalta hanyarsu cikin Ahlin Muhammad  (s.a.w) kamar yadda baki dayan  kasar Qum harami ce ga Ahlin Muhammad (s.a.w) dukkanin inda mai gangara ya zauna a birnin Qum to lallai shi yana cikin shekarsu yana cikin kariyarsu da haraminsu. Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai. Idan kana bukatar bayani dalla-dalla filla-filla sai ka komawa abin da sayyid ya rubuta cikin littafinsa mai suna (shahadul Arwahu)

 

Tura tambaya