lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Mujallar sautul kazimaini 222-221 watannin muharram mai alfarma da safar hijira ta shekaru 1439 wacce tayi daidai da 2017

shekara ta ishirin da bakwai da samar da wannan mujalla mai albarka (mujallar sautul kazimaini) tun da muka fara wannan motsi na addini da nishadi na sakafa cigaba daga majma’a tablig wal’irshad islami a’lami  cikin shekarun da suka shude munyi bakin kokarinmu har zuwa yanzu bamu gushe ba cikin karfin Allah da dabararsa babu karfi babu dabara sai da tallafin Allah madaukaki mai girma ta yanda cikin kowanne lokaci muke samar da sababbin abhbuwa masu alfani cikin wayar da kan al’umma, musammam ma ga matasa gwargwadon iko koda kuwa bai kasance yadda ake bukata ba dari bisa dari cikib maudu’ai daban daban da mafhuman sakafa  daga akidu da akhlak da irfani kan hasken fahimtar kur’ani da tsatso tsarkakka da tare da alkalumma da bayanan manya manyan malamanmu da sakafaffu daga ma’abota tunani cikin muslunci cikin fagen ilimi da addini daga wadanda suka gabata da wadanda suka rage Allah ya tsare su da tsarewarsa, amma yanzu muna begen mu kifu kan tafiya muna kuma fatan halartarku tare da mu da hallararmu tareda ku don hidimta muku  cikin wannan fagen na ilimi da sakafa kari kan kari da yawa kan da yawa hakan zai tabbatu da taimakonku na zahiri da na badini musammam ma addu’arku da nema mana dacewa da damdagatar Allah ya saka muku da Alheri.

Shugaban lura da rubuce-rubuce.

 

Tura tambaya