lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Mukalolin da akaranta dayawa.

Wasikar haske da yaye duhu daga wilayar Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata garesu

daga Abu Hassan Ali bn Ahmad dallal alkummi: muna cewa cikin imamanmu  wannan ba zai taba yiwu ba ace sunyi halitta sun azurta? Sai wasu mutane suka ce: yace: wasu jama’a daga shi’a sun sassaba  cikin cewa lallai Allah mabuwayi mai girma ya fawwalawa A’imma halitta da azurtawa ya fawwala musu hakan sai sukai halitta suka azurta, sai jama’ar shi’a suka saba da juna cikin hakan sabani mai tsananin gaske, sai wani mai magana yace: menene ya sameke ne da ba zaku koma ga Abu Jafar Muhammad bn Usman ba ku tambaye kan mas’alar sai ya bayyana muku gaskiyar lamari cikinta, lallai shine hanya zuwa ga sahibul amri (as) sai wadannan jama’a suka yarda da Abu jafar suka sallama suka mika wuya ga zancensa, sai suka rubuta mas’ala suka zartar da ita zuwa gareshi, sai takarda daga sa hannunsa ta fito zuwa garesu wacce cikinta aka rubuta: lallai Allah shine wanda ya halicci jikkuna shine kuma ya raba arzuka, sai dai cewa tunda lallai shi ba gangar jiki bane baku wani hali bane a jiki babu wani abu misalinsa shine mai ji mai gani, Amma A’imma lallai su suna rokon Allah madaukaki sai yayi halitta ya azurta sakamakon rokonsu da girmama hakkinsu.

Sannan faifaice zance shine abinda babban malamin wannan fanni babban malamin hadisi Allama majalisiAllah ya jikansa cikin littafinsa biharul anwar mai kima, yace: ka sani kadai yana kasancewa daga gullanci cikin annabawa da A’imma Imani da Allantakarsu ko kuma tarayyarsu da Allah madaukaki cikin kasantuwarsa abin bauta ko kuma cikin halitta da azurtawa, ko kuma fadin cewa Allah ya sauka cikinsu ko ya zama daya da su, ko kuma cewa su sun san gaibu ba tareda wahayi ba da ilhama daga Allah madaukaki, ko kuma fadin cewa su sun kasance annabawa, ko Imani da nasakin arwahu sasshensu ga sashe,ko Imani da cewa saninsu na wadatarwa daga komai daga da’a da barin sabo,

Imani da dukkanin wadannan abubuwa kafirci ne da ilhadi da fita daga addini, kamar yadda dalilan hankali da hadisai da ayoyi da suka gabata suka shiryar zuwa garesu,

Hakika A’imma sun barranta daga garesu, sun hukunci da kafircinsu, sunyi umarni da kasha duk wanda yayi Imani da wannan, idan wani abu daga hadisan wahami suka kwankwashi kunnenka daga wani abu daga wadancan abubuwa, to su hadisan ko dai masu karbar tawili ko kuma daga kagen gullatu suke, sai dai cewa wasu malaman kalam ilimin sanin akida da malaman hadisi sun wuce gona da iri kan gullanci, sakamakon takaitawarsu daga sanin A’imma da gazawarsu daga riska da fahimtar barabuwan halayensu da sha’anunnukansu masu ban mamaki, sai suka raunana riwayoyin sikatu masu tarin yawa sakamakon sun kunshi da nakalci wasu ba’arin barabuwan mu’ujizozi, har wasu daga cikinsu ya kai su da cewa yana daga cikin gullanci kore mantuwa daga annabawa da imamai (as)ko kuma fadin cewa sun san abind aya kasance da abinda zai kasance nan gaba da makamantan haka, tareda cewa tabbas hakika hadisai sun zo masu tarin yawa da cewa:  

«لا تقولوا فينا ربّآ، وقولوا فينا ما شئتم ولن تبلغوا»،

kada kuce mu ubangiji ne amma ku fadi dukkanin abinda kuka so ba zaku taba kaiwa ba.

Haka hadisi ya zo cewa:

«أنّ أمرنا صعب مستصعب لا يحتمله إلّا ملک مقرّب أو نبيّ مرسل أو عبد امتحن اللّه قلبه للإيمان »،

Lallai al’amarinmu  nada wahala da wahalarwa babu mai daukarsa sai mala’ika  makusanci ko annabi aikakke ko bawa da Allah ya jarrabi zuciyarsa da Imani.

Haka ma ya zo:

«لو علم أبو ذرّ ما في قلب سلمان لقتله »

Da abu Zar ya san abinda ke kunshe cikin zuciyar Ammar da tabbas sai ya kashe shi.

Da makamancion haka daga abinda ya gabata da wanda zai zo nan gaba.

Tura tambaya