lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Mukalolin da akaranta dayawa.

Tambaya a takaice:wannan tuhumar da akewa annabi cewa ya koyo kur’ani daga wani mutum ba’ajame,

 

Amsa:

Kur’ani littafi ne da yake matsayin littafin cikamakin annabawa (s.a.w) wanda yake kumshe da mu’ujizozi masu tarin yawa, abinda ya fara sauka cikin kur’ani yawancinsa yah ore idanu da zukatan mutane, daga fasaha da balaga  wanda ya kasance tareda ma’anoni  cikin zirin lafuzza kyawawa takaitattu shima kur’ani ya bayyanarsu da su.[1] Mushrikai saboda hana tasirin wannan kira na Allah cikin zukatan al’umma sunyi bakin kokarinsu cikin katange mutane daga jin wannan kira, cikin tsammanisu zasu iya hana yaxuwar wannan haske na kur’ani cikin zukatan al’umma.

Wasu lokutan sukan cewa, me yasa Allah bai turo mala’ika da wannan kur’ani wanda Allah ya basu amasa da da cewa{idan ma mun aiko mi shi mala’ika tabbas zamu sanya shi da surar mutum za kuma m tufatar da shi da abinda suke sanyawa}[2]

Wani lokacin kuma zasu ta kawo uzururruka ta yadda ta kai ga suna neman cewa a saukar musu da takardun kur’ani daga sama su taba su da hannunsu, sai dai cewa wannan ba bakon abu bane, sabaoda haka ma Allah cikin kur’ani  yake ce musu koda ma mun saukar ta takardun kun gansu kun karanta su  duk da haka kafirai zasu ce wannan ba wani abu bane face tsafi da sihiri.

Wani karon domin ragewa kur’ani daraja, sai suce kawai shi tatsuniyoyin tarihi ne, suka ce kur’ani littafin tatsuniya ne kawai wanda da yake nakalto kissoshin mutanen da suka gabata saboda haka nema suke cewa: {lokacin da wadanda suka kafirce  suke shirya maka makirci domin su tabbatar da kai ko su kashe ka ko kuma su koreka suna shirya makirci Allah yana warware makircinsu Allah shine mafificin masu makirci}[3]

Acikin wannan lokaci dukkanin shubuohinsu suka rushe basu kai ga cimma wata natija ba, a lokacin da suka tsinkayi mutane sun ga balaga da fasahar kur’ani, sai suka kirkiro wani sharrin suka ce wannan kur’ani ba littafin Allah bane kadai kirkirar malaman muhammadu (s.a.w) ne. sai kur’ani yayi musu martani da: {mu mun san cewa lallai su suna cewa kadai dai wani mutum ke koyar da shi harshen wanda suke karkata zuwa gareshi ba’ajame ne  wannan kuma wannan kur’ani harshe ne balarabe}[4]

Gaskiyar magana shine cewa mushrikan larabawa da suka cewa ba zasu iya samun wanda zasu danganta kur’ani gareshi daga cikinsu su larabawa sai suka fake da shirya makida suka tashi suka yunkura bincikowani mutum wanda yake ba a sanshi ba sais u danganta kur’ani gareshi ta yadda bayan wasu yan kwanaki cikin sauki su gafalar da mutane daga kur’ani.

Tambaya kan cewa mene ne hadafin wannan shubuhar? Cikin tsammani zami iya amfanuwa da wannan aya.

1-mene ne manufarsu cikin wannan tuhuma da kage na cewa mai karantar da annabi (s.a.w) lafuzzan kur’ani wani mutum wanda ma kwata-kwata bai san harshen larabaci ba! Wannan karshen tanuwa asirinsu ce, sannan wannan ba wata karfaffiyar shubuha bace, sannan a gefe guda ta kaka wannan ba’ajame d aya jahilci yaren larabci za a ce ya kawo wannan jumloli masu cike da balaga da fasaha wanda ma’abota salin yaran baki dayansu sun gaza gabansu kai hatta ta kai ga basu da karfin gwiwa da ikon iya kalubalantar sura daya daga kur’ani?

2-manufarsu shine cewa annabi (s.a.w) ya karbo abinda ke kumshe cikin kur’ani daga wani ba’ajame , wannan ma zamu ce zuba abinda kur’ani ya kumsa cikin zirin wadannan lafuzza da jumloli masu gajiyarwa wadanda dukkanin masu fasahar larabawa na baki dayan duniya suka durkusa masa suka gaza gabansa, ta hanyar wanne mutum ya faru? Shin hankali zai yadda cewa wani mutum ne ba’ajame da ya jahilci larabci ko kuma ta hannun wani mutum da ikonsa ya shallake ikon dukkanin mutane ya faru?

Cikin kowanne hali wannan shubuha, wani batu ne sabo da ya kasance domin nesanta mutane daga kur’ani; Allah ta hanyar amfani da harshen larabci da bayyanarwa kur’ani sai ya basu: malaman da kuke danganta kirkirar kur’anu zuwa garesu mutane ne wanda bama larabawa bane, duk da cewa zasu iya cimma kololuwar adabin larabci sai dai cewa a wannan zamani  ma’abota fasahar larabawa da balagar harshen sun kasance masu tarin yawa amma duk da haka sun gaza iya saka aya guda da ya rak misalign ayar kur’ani, ta kaka kuma wanda bama balarabe ace zai iya zuwa wanda wannan kalami?!

Wanne mutum ne suke nufi da malamin annabi (s.a.w)?

Kamar yadda aka ce : wanda kafirai suke nufi da malamin annabi (s.a.w) wani bawan ibn hadarami ne da ake kiransa da sunan makisu,  a wata magana ance  akwai bayi biyu na ibn hadarami wadanda suke d sunayenb yasar da jabar, ko kuma abinda suke nufi da shi shine wani bawa da ake kira da sunan bal’am da ya kasance a makka, daga karshe dai wasu sunce : salmanul farisi[5] ne cikin wadanda ake tsammani akwai wani mutum da ake kira ruze wanda ba ambaci ianahin sunansa ba in banda cikin ba’arin rubuce-rubucen suyudi[6] da a cikinsu ya bayyana cewa wanda ake nufi da ruzu shine salmanul farisi, wanda ake nufi da ruze shine dai salmanul farisi

   

 [1] Wujuhul I’ijazul kur’ani

[2] An’am:9

[3] Anfal:31

[4] Nahlu:103

[5] Suyudi jalal dini cikin littafin itkanul ulumul kur’ani juz 2 sh 322 bugun bairut darul kutubul arabi, shekara 1421

[6] Duraihi fakrud dini, majma’ul baharaini ju z 2 sh 70 bugun Tehran shekara ta 1375 kamari

Tura tambaya