lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Mukalolin da akaranta dayawa.

shin riwayoyin da suke cewa salmanu Farisi da Abu zar lokacin dawowar imam zaman (as) suna daga cikin matamaimakansa riwayoyi ne ingantattu

 

Amsa:

1-Kamar yadda ka sani ita batun raja’a yana daga akidojin shi’a imamiya, yana da ma’anar dawowa duniya bayan mutuwa gabanin tashin kiyama, sannan raja’a ba ta shafi kowa da kowa ta kebanci muminai tsantsa da mushrikai tsantsa.

Riwayoyi dangane da batun raja’a daga ingantattun masadirai aka nakalto su daga cikinsu akwai riwayar:

 

«وَ رَوَى الْمُفَضَّلُ بْنُ عُمَرَ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ (ع) قَالَ‏ يُخْرِجُ الْقَائِمُ ع مِنْ ظَهْرِ الْكُوفَةِ سَبْعَةً وَ عِشْرِينَ رَجُلًا خَمْسَةَ عَشَرَ مِنْ قَوْمِ مُوسَى (ع) الَّذِينَ كَانُوا يَهْدُونَ بِالْحَقِّ وَ بِهِ يَعْدِلُونَ‏ وَ سَبْعَةً مِنْ أَهْلِ الْكَهْفِ‏ وَ يُوشَعَ بْنَ نُونٍ وَ سَلْمَانَ‏ وَ أَبَا دُجَانَةَ الْأَنْصَارِيَّ وَ الْمِقْدَادَ وَ مَالِكاً الْأَشْتَرَ فَيَكُونُونَ بَيْنَ يَدَيْهِ أَنْصَاراً وَ حُكَّاما

2-Mufaddal bn umar ya rawaito Abu Abdullah 9as) yace: ka’im (as) zai fito da mutum27 daga garin kufa mutum 15 daga mutanen Musa 9as) wadanda suka ksance suna shiriya da gaskiya suna adalci da ita da kuma mutum bakwai daga Ashabul kahfi da Yusha’u bn nun da salmanu da Abu dujana Ansari da mikdadu da malikul Ashtar  sai su kasance alkalai a gabansa da mataimaka.[1]

3-wannan riwaya duk da cewa ta zo daga masdari ingantacce misalign littafin isrhad  da tafsirin Ayyashi,[2] sai dai cewa ka sani bai da ma’anar cewa duk kanin riwayar da aka nakalto ta daga ingantaccen littafi ba lallai ne ita riwayar ta kasance ingantacciya ba, dole a kowanne waje a lura da isnadi da matani.

4-dayawa daga riwayoyi da suka zo kan raja’a basu ambaci sunaye ba, sannan wadanda suka zo da amabton sunaye mutane misalign manzon Allah (s.a.w) A’imma (as) hazrat isa (as) da annabawa misalign zakariyya hizkilu (as) wadanda akan tafarkin Allah suka fuskanci azaba da wahalhalu, haka ma wasu riwayoyin sun ambaci imam na farko da zai fara dawowa shine imam Husaini (as).


[1] Mufid muhammad bn muhammad isrhad juz 2 sh 386

[2] Ayyashi mohd bn mas’ud juz 3 sh 33 mabugar ilimiya tehran

Tura tambaya