lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

siffofin jagoraHar yanzu muna kan bahasin siffofin jagora, daga cikin abind ayake siffar jagora shine ya zama yanada kaifin hankali ya zamanto hakim kamar yadda aflaton yake cewa : jagoranci dole ne ya kasance ga ma’abota falsafa suke sama wannan ra’ayi ne na aflaton yayinda yake bayanin yadda ya kamata ta kasance amintacciya wacce take tafiya kan tsarin hankali, sannan falsafa din nan ba dole bane ya zama mutum sai ya karanta muhimmi shine ya zama a aikace yana yinta ko,ai ya zama akwai hikima ya zama an duba shi an yi hangen nesa kansa an ajiye komai a mahallinsa ya ishi mutum  ya zama (philosophy) da wannan ma’ana. Ala ayyi halin dole ya kasance ga shugaba.

Imam Ali (as) yana cewa: (daga cikin abubuwa da suke sanya daula cigaba fadakar daula.

Idan hankali ya zamnto yana da haske yana kallon ko ina daula zata cigaba da samun tabbata da dawwama. Wata sifa ta gaba shine ilimi dole ne shugaba ya zama yana ilimi da abinda yake gudana a kasa da ilimin yanda za a tafiyar da kasa wannan dole idan bai da ilimin yanda zai tafiyarsa da abu zai rushe, idan kuma bai da ilimi dole ya samu masu nuna masa hanya wadanda suke da ilimi, Allah yana cewa:

إن الله اصطفاه عليكم وازده بسطة في العلم والجسم.

Allah ya zabe shi a kanku ya kara masa cikin ilimi da jiki.

Da wanne matsayi Allah ya zabe shi, Allah ya zabe shi don ilimi da jismi, wasu sun dauka jismi shine girman jiki suna ganin kato ne, wannan sam babu ma’ana idan haka ne sai mu samu wanda ya fi zama lukuti a najeriya ya zama shugaba,  sai kowacce kasa ta zabi wanda yafi kowa zama kato sai ta sa shi shugaba, jisim anan yana nufin kudura iko wato yanada tasiri, shi jagora wanda idan an bashi jagoranci zai yi amfani da wannan ikon da wannan kudura din ya tafiyar da komai saboda haka kenan akwai ilimi akwai kuma karfin tafiyar da wannan ilimin shine abidan Allah ya baiwa dalut, saboda haka dole ne shugaba ya san ilimin abinda yake tafiyarwa, sannan har ila yau ya zamanto yanada ibtikar wato haifar da wasu sababbin abubuwa ya zama kullum cikin shugabancinsa anan ganin sababbin abubuwa idan ba haka zai gundiri mutane kasa ta daskare.

Sanann ya bada lokacinsa wajen himma kada ya zama mai nauyin jiki da kasala

من اعمل اجتهاده بلغ مراده

Imam Ali (as) yana cewa duk wanda yayi amfani da kokarinsa himmarsa yayi sa’ayi sosai zai samu abinda yake son cimma.

Tura tambaya