lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KAN HANYAR SHUGABAN SHAHIDAI IMAM HUSAINI a.s


Da sunan Allah mai rahama nmai jin kai

Ubangiji madaukakin sarki cikin littafinsa mai girma da hikima mai zartarwa da tabbatar da maganarsa yana cewa:

﴿ اللَّهُ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ مَثَلُ نُورِهِ كَمِشْكَاةٍ فِيهَا مِصْبَاحٌ الْمِصْبَاحُ ﴾.

{Allah shi ne hasken sammai da kasa misalin haskensa kamar misalin taga ce da aka ajiye fitila a cikinta}

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: cikin daman Al'arshi anyi rubutu da koren launi cewa Husaini ne fitila shiriyakuma shi ne jirgin tsira..

Bayan haka: daga cikin muhimmman ayyuka nagari mafi falalar ibada tsarkakakku ma’abota mukami mai girma da gwaggwaban lada da samun aljanna Firdausi mani’imciya da tsira daga azabar jahannama shi ne yin kuka kan musibar da bala’in da ya samu shugaban shahidai Imam Abu Abdallah jikan manzon Allah Ta'ala (s.a.w) furen Fatima batula (a.s) `dan karamin zakin Aliyu Almurtada `dan'uwan Hassan almujtaba mutum na biyu cikin mutanen cikin bargo dubun dubatar gaisuwa  da yabo da aminci su kara tabbata gare su, lallai cikin haka masu rigengeniya su yi rigengeniya, masu aiki su yi aiki tukuru, lallai babu mai samun wannan sai mai babban rabo

Lallai Allah matsarkaki madaukakin sarki hakika ya kebanci Husaini (a.s) zinariya kasantattu dayantacciya, babbar ayar Allah, mafi girman sirrin samuwa da wasu falalloli kususiya da wasu Abubuwa da fifita da su koma bayan dukkanin halittu, babu banbanci cikin tsarin halitta ko na shar’antawa.

Daga farko: hakika Allah ya sanya waraka cikin kasa mai albarka wadda cikinta aka kashe Husaini (a.s) kamar yadda ya sanya waraka cikin ruwan zamzam.

Na biyu: haramun cin dukkanin kasa face kasar Imam Husaini(a.s) domin neman waraka, sannan makaruhi ne sanya bakin tufafi da yin raki face kan musibar da ta samu shugaban shahidai cikin watannin safar da Muharram da Safar, kan wadannan matakai biyu daga shaidu da misalai masu tarin yawa

Shin ma kasan cewa kacokafAllah ya halicci aljanna daga hasken Imam Husaini (a.s) shi ya kasance sababin samuwarta cikin duniyar yiwuwa ya yinda cikin aljanna akwai abin da wani ido  bai taba gani ba wani kunne ba ta ba ji ba. bai kuma taba darsuwa cikin zuciyar wani dan Adam ba

ya kake tsammanin sababin samuwar aljanna shi kuma zai kasance tunda dai ka ji kadan daga labarin aljanna, shi kana tunanin akwai wani mutum da zai iya tsinkayar hakikanin yadda Imam Husaini (a.s) yake, lallai dukkanin abin da muka sani dangane da shi tun zamanin farko zuwa wannan zamani da muke ciki kai har zuwa tashin kiyama kaso daya ne daga cikin `dari ne wanda ragowar kaso casa’in da tara na wajen Imamul Hujja ma’abocin zamani (a.f) abin da ke gare mu kamar misalin cikin tafin hannu ne da muka kwarfa daga tafkunan falalolinsa da darajoji kai a hakika ma dai abin da ke gare mu wani Abu ne da yake daga gere su zuwa gare su yake komawa kai da ba don su ba da har abada ba za mu taba iya saninsu ba

da za mu karanta tarjamomin malamanmu kan manya-manyan masana ilimin fikihun mu ma’abota girma daga magabata da wadanda suka biyo bayansu har zuwan wannan zamani da muke ciki muka bincika halayyarsu lallai babu makawa za mu gano sabubban samun dacewarsu da tsinkayarsu da shahararsu kamar misalin shaik `Dusi da Shaik Mufid da Sharifai biyu Sayyid Murtada Alamul huda da Sayyid Sharif Radi, da kuma irin su Sayyid Mahadi Bahrul ulum da shaik Abdul karim Ha’iri da Allama majalisi da Sayyid malaminmu Najafi Nar’ashi (ks) da ire-irensu daga manya-manyan malamai lallai mafi bayyanar sababin samun dacewarsu shi ne dangantakarsu tsarkakakka tsaftatta da lamarin shugaban shahidai Imam Husaini (a.s) da kuma rige-rigensu cikin raya bukukuwan ta’aziyyarsa da dukkanin yanayinsu  da launukansu saboda girmamawa da raya ibadun Allah matsarkaki

An karbo daga Imam Rida (a.s) cikin wani hadisi da ya yi bayani dalla-dalla: (lallai tunawa da ranar da aka kashe Husaini ya na sanya idaniyarmu tayi radadi yana sanya mu zubda hawaye yana kaskantar da madaukakinmu)

an karbo daga majibancin lamarinmu Imamul Hujja da zamani Hujja ibn Hassan Al’askari Allah ya gaggauta bayyanarsa mai daraja yana cewa: ya kakana zan kiraye ka safe da yamma zanyi maka kukan jini mayin kukan hawaye.

Lallai Imam Husaini (a.s) hasken Allah ne kuma fitilarsa cikin duniyar samuwa, lallai shi cikakken mutum ne kammalalle wanda sunan ubangijinsa mi girma ya yi tajalli cikinsa, da kuma hakikar kansa mai mafi girma, hakika ya bayyana cikin dabi’unsa na zati da juyin juya halinsa na kawo gyara madawwami matukar dawwamar zamani.

Lallai jahilai sun nuna masa kiyayya da dukkanin siffofinta, gafalallu da makiya sun tadar da fitina da shubuhohi kan rayar da tunawa da kisansa da yunkurinsa daga wannan lokaci zuwa wancan lokaci suna son dusashe hasken Allah da bakunansu da shubuhohinsu da kafofin sadarwarsu sai dai cewa kuma shi Allah zai cika haskensa cikin Imam Husaini (a.s) har zuwa bayyanar Imam Hujja (af) Almahadi wanda zai cika kasa da adalci bayan ta cika da zalunci da danniya.

Imam Husaini (a.s) zai dawo karo na biyu tare da sahabbansa masu daraja dawowa tabbatatta da Hujja da hankali da nassi wanda hakan ya kasance daga Abubuwa da aka sallamawa cikin mazhabar Ahlul baiti (a.s) 

        Sannan yin shakka da mukamomin Ahlul baiti (a.s) da zantukansu bawai bakon Abu ba ne wanda zamani da muke ciki ya kagar ya farar, bari dai ya kasance hatta a zamanin Imamai (a.s) kai har lokacin Annabin rahama akwai cikin mutane mutumin da yake nuna wani nau’in daga jayayya da kin yarda da zantukan Annabi (s.a.w)

An rawaito daga Imam Sadik (a.s) da ingantaccen isnadi cikin littafin Alkamilul Ziyarat ya ce: Imam Husaini ibn Ali (a.s) wata rana ya kasance cikin dakin annabi (s.a.w) suna wasa tare yana sanya shi dariya, sai A’isha ta ce: ya manzon Allah menene ya fi tsanani daga yadda wannan yaro karami ke burgeka? Sai ya ce: mata: kaiconki ta kaka ba zon shi ba ta kaka ba zai burgeni ba bayan shi ne kayan marmarin zuciyata sanyin idona? Amma da sannu al’ummata zata kashe shi duk wanda ya ziyarce shi bayan wafatinsa Allah zai rubuta masa ladan hajji daga hajjin dana halarta

sai ta ce: ya manzon Allah(s.a.w) hajji fa daga hajjin da aka halarta?

Sai ya ce: eh ladan hajji guda biyu daga hajjin dana halarta

Sai ta kara cewa: ya manzon Allah (s.a.w) hajji biyu fa daga hajjinka?

Sai ya ce: na’am hajji guda hudu.

Ba ta gushe ba tana kokawa da mamaki shi kuma yana karawa kan kokawarta ya ninninkawa har sai da yakai ga adadin hajji ya kai 90 daga hajjin manzon Allah (a.s), tare da Umararsa

Daga cikin mafifitan kwanakin ziyararsa mai albarka cikin ranar Ashura daga mafi falala ziyara da hadisi ya zo kanta ita ce ziyarar Ashura. Hakika cikin shekaru biyu da suka gabata cikin watan Muharram mai alfarma mun yi muhadara kan tafsiri da sharhin ziyarar Ashura da bayani wasu nukdodi cikinta, domin ta kasance karin haske mai haskaka cikin rayuwar mu ta ilimi da aiki da zamantakewa da daidaito

bai buya ba cewa ishkaloli da shubuhohi wanda ake tayarwa game da ziyarori da bakukuwan ta’aziyya wanda a zahirinsu ba baki bane, bai gushe ba akwai wadanda suke ta ruruta wuta da yin huri cikin kura, sai dai cewa ya tabbata a bayyane a gaban idanu yin hakan babu abinda yake janyowa masu yi face kunyata da tozarta da haramtuwa, domin shi Allah madaukaki  hakika ya yi alkawalin azaba da cewa babu  makiya lamarin Husaini (a.s) za su karu da shi face faduwa da tozartuwa da rashin nasara da kaskanta, shi kuma raya lamarinsa zai ta bayyana da kuma samun daukaka.

Mene ne ya fi kyawu da kayartawa daga abin da gwagganmu Hurriya Zainabul Kubura (a.s) ta bada labari da goben `dan’uwanta Husaini (a.s) kamar yadda ya zo cikin littafin Alkamilul ziyarat da isnadinsa daga majibancinmu kakanmu Imam Zainul Abidin shugaban masu sujjada Ali ibn Husaini (a.s) ya ce: lokacin da abin da ya faru ya faru damu a garin daffi da kashe babana (a.s) aka kuma kashe wadanda suka kasance tare da shi daga `ya`yansa da `ya’uwansa da sauran iyalansa aka dora matayensa masu alfarmarsa  kan dokkai ba tare da siddi ba aka nufi kufa damu sai na dinga kallon gawarwakinsu kwance kan kasa ba tare da an binne su ba  kai hakan ya girmama cikin kirjina ya tsananta damuwata, raina ya kusa fita sai gwaggona Zainabul Kubra diyar Ali (a.s) ta fuskanci halin da nake ciki sai tace: yaya nake ganinka kana kyauta da ranka ya kai wanda kai ragowa daga zuriyar kakana da babana da `yan’uwana?

Sai na ce: yaya bazan yi raki da gigita bacin ina kallon shugabana da `yan’uwana da baffanena da iyalina suna jike cikin jinanensu  an barsu kwance kan tsaurin kasa an yi musu kwacen hakki an bar su ba tare da likkafani ba a binne gawarwakinsu ba babu wanda ya zo wajensu ko kusanto su, kai kace su wani gida ne daga Dailama ko Kazar.

Sai sayyada Zainab ta ce: kada abin da kake gani ya gigita ka ya saka raki wallahi wannan alkawali ne daga Allah da manzon Allah (s.a.w) zuwa ga kakanka da baffanka hakika Allah ya riki alkawalin wasu mutane daga wannan al’umma wadanda fir’aunoni  kan kasar wannan zamani  basu sansu ba, sannan su sanananu ne a wajen mutanen sammai lallai su ne zasu tattaro gabban wadannan jikkuna da gangunan jiki da suke jike cikin jini suke a warwatse su binne su sanya wata alama a kabarin babanka shugaban shahidai a wannan gari na daffi  da kabarinsa bi dusashe ba ya zama ba wata alama da za tai nuni zuwa gare shi tsawon darare da kwanaki lallai jagororin kafirci da mabiya bata suna bakin iyawarsu da kokarinsu wajen  busashe kabarinsa da shafe shi amma babu  abin da hakan ke kara masa face kara bayyana da kara daukakar lamarinsa

Ka sani cewa lallai zurfafar musibar karbala da kuma zurfafar sirrikanta  da  ke bayan hakan daga ilimummuka  na sanain Allah wanda babu mai iya riskarsu hakikanin riska face Ahlul-baiti (a.s) misalinsu ke cewa: (babu wata rana misali ranarka ya baban Abdullah)  amma  muka fuskanta daga wannan waki’a mai girma  da musiba mafi girma to bai wuce gwargwadon kwarfar tafin hannu ba daga tafkunan Husainiyya  dake cike da kumfa mai karo da juna mai zurfin da nisan geffa mai nitsa matuka da aka gaza riskar zurfinta

Kamar yadda ya gabata lallai Imam Rida (a.s) Imami na takwas daga hujjojin Allah yana cewa: (lallai tunawa da ranar Husaini na sanyawa idaniyarmu ciwo).

 misalin mafi girman waliyyin Allah ma’abocin zamani (af) yana cewa: (zan yi maka kukan jini mayin hawaye).

  menene ya farune ranar Ashura cikin kasar karbala da har ya kawo misalin irin wannan radadi da gigita da shiga musiba daga Imamanmu(a.s) tsarkaka?!

    Za mu iya fuskanta daga wadannan hadisai guda biyu masu daraja ma’ana hadisin Imam Rida da na Imam Hujja (a.s) cewa kwarmin idaniyarsu ta zubar da hawayen jini sakamakon musibar da ta sami baban Abdullah (a.s) da kakansu shugaban shahidai bawai kadai cikin kwanakin watannin Muharram da Safar ba kadai bari dai tsawon kwanakin cikar shekara baki daya ba tare da kayyadewa ba ko kebantarwa, ba komai ya sanya hakan ba face bakin ciki mai girma kan waki’ar Karbala

 Da  ya afku ranar Ashura sai idaniyar ta bushe sakamakon yawan kuka da dawwamarsa safe da yamma kan musibar da ta sami kakansu baban Abdullah Husaini (a.s)

Lallai muna da abin kwaikwayo nagari kakkyawa daga garesu, ya zama wajibi kan mu cikin kowanne zamani da lokaci mu halarto da musibar da ta afku a karbala da tunawa da ita, kai hatta idan mun samu damar iya tsayar da bukukuwan jaje da ta’aziyya ko da kuwa da mustawar iya tara makota da abokaine  da mutanen unguwa daga kowanne gida guda daga gidajen muminai tsawon shekara cikin kowacce rana daya bayan dayansu safe da yamma, lallai shi tunawa da Ahlul baiti (a.s) na da lada mai girman gaske da albarka ga dangi da mutanen gida da dukkanin wanda ya halarci ta’aziyya, cikin hakan akwai tarbiyantar da yara  kan soyayyar Husaini (a.s) da kaunarsa da narkewa cikin tushensa da misalsalansa madaukaka wadda ya sadaukar da ransa dominsu domin ya zamanto abin koyi da misali da fitila shiriya ga wanda yake son bin hanyarsa  hanyar `yanci da aikata muslunci na Asali da dabbaka shi, kamar yadda shi dama ya kasance jirgin tsira  ga wanda ya haushi  don ya kai ga bakin gabarsa (a.s) da bakin tafkin nutsuwa da zikirin Allah matsarkaki.

 ya dace ga dukkanin masoyi shi ne ya zama wajibi ya karu cikin sanin wannan tafarki mai yalwa da fadada ya kuma tsinkayi sasanni sabbi ya jibanci sabuntawa da cigabantarwa tare da kiyaye Asali da ilimummuka masu kima, lamarin Ashura  da musibar Husaini shugaban shahidai (a.s) itace mafi girman musiba da tarihin dan adam ya shaida, saboda wannan nema magabata nagargaru  daga malamanmu masu girma da maraji’ai masu girma  suke tanadi domin raya da girmama alamun Husainiyyya bayan bikini din Gadir mafi haske, shi’a sun kasance cikin zaman makoki da bakin ciki sukan rataye bakin kyalle jikin bangunan Husainiyya da maukibobi da tarukan majalisai, ana kafa minbarori  a raya zaman makoki da ta’aziyya cikin sasannin duniya, Allah ya so tutocin daffin Husaini su wanzu suna madaukaka a dage suna filfilawa a sama, lallai amabaton Husaini(a.s) madawwami ne mai dawwama tare da dukkanin kokari da yunkurin makiya cikin busasheshi da gogeshi da shafin samuwa, lallai Allah matsarkaki yana sakayya da kuma azaba cikin gidan duniya da lahira  ga dukkanin wanda ya yi gaba da kiyayya da shi yayi kiyayya da gaba da ibadunsa da bukukuwansa, shaida nawa muke da su cikin tarihi kan haka, musammam ma cikin wannan zamanin da muke ciki, lallai Allah yana gaggauta azabtar da makiyan Imam Husaini(a.s) kai hatta hakan ya kusa ya zama ana kidaya shi daga Abubuwan da Imam Husaini ya kebanta da su ya dayantu da su.

Haka iradar Allah da mashi’arsa ta so ta kuma hukunta ya yi mu’amala da lamarin Husaini (a.s) a haka yana mai banbantawa daga waninsa, ya kasance al’umma bayan al’umma suna tunawa da shi fiye da yadda ake tunawa da waninsa, tare da cewa makiya da munafukai sunyi bakin  kokarinsu cikin dusashe ambatonsa da goge shi da bushe haskensa. Sai dai cewa Allah yaki yarda face sai ya cika haskensa, lallai an rubuta a daman Al'arshi cewa Husaini shi ne fitilar shiriya jirgin tsira, lallai babu shakka ko kokwanto kan cewa lamarin Al'arshi da sammai na sama da lamarin kasa da  cikinta da wanda ke cikinta. Idan ya zamanto Imam Husaini (as) da dukkanin zahirinsa hakika Allah ya togaceshi  to babu abinda yake kan mu face muyi ta’ammuli da lamarinsa ta yadda aka bukace mu da muyi da kuma fifitawa kamar yadda halin hakan yake wurin `yan shi’a da masoya masu daraja, lallai ana sanin `dan shi’a Imamiyya da imaninsa da Gadir da Ashura, lallai tsawon zamani da cikin dukkanin kasashe da garuruwa an san shi’anci da raya ranar wilaya(ranar Gadir) da kuma ranar bara’a daga makiya ranar Ashura.

Lallai hukumar Banu Umayya ta yi ganganci tun ranar farko cikin boye hasken Imam Husaini(a.s) idan muka duba ingantattun littafan sunna za su shaida ma wannan lamari a bayyane saboda karancin hadisai kan Imam Husaini (a.s) da falalolinsa, misali cikin sahihul buhari bai nakalci riwaya ba kan Imam Husaini (a.s) face riwaya guda daya rak tare da  ke cikinta daga matsaloli kamar yadda ma’aboda ilimi da sani suka fadaka da hakan, sai dai cewa tare da hakan akwai hadisai cikin littafan jamhur dake bayyana girman shugaban shahidai (a.s) da shahadarsa da lamarinsa.


cikin musnad Ahmad juz 1 sh 85, musnad Abu ya’ala juz 1 sh 298 h 33. Mu’ujamu Kabeer na dabarani juz 3 sh 105 h 2811 da isnadinsa daga Najani Hadarami cewa ya yi tafiya tare da Imam Husaini (a.s) ya kasance shi ke rike da butar alwalarsa yayin da ya taka sawun garin Nainawa (karbala) hanya zuwa Siffaini sai ya daga murya ya ce: hakuri ya baban Abdullah

Sai na ce: me ya faru ya baban Abdullah?

Sai ya ce: wata rana na shiga wajen annabi (s.a.w) idanunsa suna kwarar da hawaye sai na ce ya Annabin Allah menene ya samu idanunka take kwararar da hawaye? shin wani mutum ya bakanta maka? Sai ya ce: Jibrilu ne ya tashi daga wajena da zu ya kuma bani labari cewa za a kashe Husaini a gefen koramar Furatu, sai ya ce mini shin kana so in kamsar da kai kamshim kasar da za a kashe Husaini cikinta?

Sai nace : na’am

Sai ya mika hannunsa ya damko wata kasa ya bani sai na kasa mallakar idaniyata har sai da ya kai ta zubar da hawaye

Irin wannan ta faru da Sarkin muminai Ali (a.s) a kan hanyarsa zuwa garin Siffaini gabanin mai afkuwar  ta afku a karbala da shekaru ashirin sai baban Husaini ya yi zaman makoki kansa tun gabanin shahadarsa kamar yadda Annabawa sukai tun daga Adamu har zuwa cika makin Annnabwa (s.a.w)

Tura tambaya