lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Mukalolin da akaranta dayawa.

Amsar SAYYID Adil ga D.R Kubaisi


 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

dana na kaina mai neman sanin gaskiya da hakikanin al’amari hakika abin da mai ambaton tarihi ya Ambata kadai ba wani abu bane face jinkirtaccen al’amari daga tarihi wanda malaman tarihi yaran sarakuna da yan kanzagin halifofi da sarakuna daga Umayyawa da Abbasiyawa kamar yadda dama a dabi’ance yake cewa za su rubuta abubuwan da sarakuna da halifofin zalunci da danniya suke so, musammam ma da yake ma akwai yunkurinsu na wanke zalincin da sukai  da barnarsu da danniya kan al’ummu da imani da muslunci, saboda haka ba zai yiwu a iya dogaro da tarihin da alkalaman da aka dauke haya aka biya su kudi suka rubuta ba da ya kasance jirkitacce na jabu.

Ya isar maka zama shaida cikin fadin mai fadi  (da kashe mutane biyu da akaiwa bushara da aljanna) cikin abin da ke wajen mutane na cewa anyiwa mutane goma bushara da aljanna sai dai cewa daga cikin abin da ke nuni kan karyata wannan hadisi shi ne abin da ya afku daga kisan wadanda suka warware alkawali lalle manzon Allah(s.a.w) ya baiwa sarkin muminai Ali (a.s) labari cewa da sannu zai yaki  masu warware alkawali ma’ana masu warware alkawalin mubaya’a wanda hakan karara na nuni da ishara kan zarginsu domin shi Ali ya na tare da gaskiya, kuma gaskiya na tare da shi  duk inda ya juya gaskiya nan take juyawa, duk wanda suka yaki Ali lalle sun kasance munafukai lalle sun kasance Azzalumai, sannan babu shakka cikin kasancewa azzzalumai da munafukai cikin wuta kamar yadda nassi mabayyani ya tabbatar da hakan da kuma nassin kur’ani cikin ayoyi masu tarin yawa, bayan haka ta yaya Dalha da Zubair wadanda an kashe su suna masu yakar Ali (as) za su kasance daga cikin wadanda akaiwa bushara da aljanna?  sannan shima Ali (as) ace yana daga cikin wadanda akaiwa bushara da aljanna wannan na daga tufka da warwara ace azzalumi da wanda aka zalunta da wanda ya yi kisa da wanda ya kashe ace dukkaninsu suna aljanna kuma dukkaninsu suna kan gaskiya da Imani?

Bari dai dole daya daga cikinsu ya kasance mumini dayan kuma ya kasance munafuki hakan idan sun kasance daga musulmai, sannan su munafukai yan wuta ne bawai ai musu bushara da aljanna ba wanda hakam na nuni da cewa sun aminta daga aikata sabo sun zama ma’asumai

Tura tambaya