lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

muslunci a takaice


 

Allah madaukakin sarki cikin bayyanannen littafin sa da yankaken zancen sa yana cewa:

(إنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللهِ الإسْلامُ ) .

Hakika addinin a wurin Allah shi ne muslunci.[1]

(وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الإسْلامِ دِينآ فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ ) .

Duk wanda ya nemi wani addini koma bayan muslunci ba za a karba daga gare shi ba.[2]

(اليَوْمَ أكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإسْلامَ دِينآ).

Yau ce ranar da na kammala addininku gareku na cika ni'imata kanku na yardar muku da muslunci a matsayin addini.[3]

 

Muslunci mai girma shi ne addinin Allah madaidaici kamar yadda ayoyi masu daraja da lafiyayyen hankali suka nassanta hakan da dukkanin bayyanarwa kan haka.

Muslunci shari'a ce daga sama wacce aka aiko Muhammad annabi mafi girmama annabin rahama kuma rahama ga dukkanin talikai (s.a.w) ya aiko shi da wannan shari'a wacce gabaninsa ya aiko wasu annabawan da manzanni da ita.

Sakon muslunci sako ne karfaffa kubutacce daga dukkanin jirkita cikin ginshikan sa da asalan sa, yana tafiya kafada da kafada da dukkanin zamani da lokaci, lallai shi sako ne na dukkanin duniya da yake danganta mutum zuwa ga ubangijin sa da makomar sa, sakon muslunci na warware dukkanin matsalolin al'umma har zuwa tashin kiyama. Lallai shi sako ne madawwami, kuma haske ne mai habbaka da bazuwa cikin dukkanin loko da lungunan rayuwa. Yana kuma game baki dayan bangarorin rayuwar duniya da lahira, taken sa na tauhidi ya sauya ya koma zuwa tabbatattun abubuwan ilimi cikin bangarorin da fagen rayuwa, ya shiga cikin tarihin samuwar mutum, ya kuma taimaka cikin kera shi da halaittar jama'a sabuwa ma'abota wayewa da cigaba cikin ilimansu da fannoninsu da rayuwarsu mai habbaka, kufan sakon muslunci mai matukar tasiri bai takaitu ba cikin gina wannan al'umma abar jin kai, bari dai ya mika karkashin sa domin al'umma ta kasance mai karfi da tasiri cikin dukkanin duniya kan doran hanyar tarihi a karkashin sa.

Shi sakon muslunci shi ne samfuri na karshe daga sama, shi ne karshen tsari da hanyar ubangiji da cikamakin sa ga annabta da take karfafawa da tabbatar da cigaba da mikewar sakon muslunci tsawon zamanunnuka masu zuwa, kamar yanda sakon muslunci ke kore bayyana wata annabtar sabuwa daban a dandalin duniya.

Sakon muslunci madaidaici ne cikin dokokin sa da hukunce-hukuncen sa, yana daukaka kan dukkanin sakonnin sama da suka gabace shi, domin yana dacewa da tsarin lafiyayyar halittar dabi'ar mutum da hankalin sa madaidaici, yana bude dukkanin sasannin sa tun daga zanin shimfidar da aka haifeshi har zuwa kabari, alheri da arziki da farin ciki da ni'imtuwar rayuwa  da rayuwa mani'imciya ga dukkanin wanda ya dabbaka shari'ar muslunci a aikace cikin rayuwar sa da sulukinsa da tunaninsa, duk wanda ke san yin bincike da tabbatarwa kan addinai da mazhabobi da sanin lafiyarsu da gano gaskiya daga cikinsu to wajibi kansa da farko ya fara da bincika addinin muslunci, domin cewa da hukunci lafiyayyen hankali bincike da dandakewa da ya gabata yana wadatarwa daga wanda zai zo daga baya bawai akasi ba.

Kamar yadda ya wajaba kan dukkanin musulmi wanda yayi imani da sakon muslunci da ya san musluncin sa hakikanin sani, ya koyo hukunce-hukuncen sa da dokokin sa, ya nemi samun fahimta cikin addini hakan na daga kamalar sa bari dai kamalar dukkanin kamala kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja daga shugabanmu Abu Jafar imam Bakir amincin Allah ya kara tabbata gare shi:      

«الكمال كلّ الكمال : التفقّه في الدين ، والصبر على النائبة ، وتقدير المعيشة »  .

Kamalar dukkanin kamala su ne: neman fahimtar addini, hakuri kan musiba, yin tsakatsaki cikin al'amuran rayuwa.[4]

 

Mun yi imani hakikar imani da cewa lallai addini wurin Allah shi ne muslunci cikin kur'ani mai girma wani lokacin ana kiran muslunci sai a nufi ma'ana mafi gamewa wanda shi ne addinin dukkanin annabawa tun daga annabi Adam har zuwa cikamakin annabwa (s.a.w) wannan addini daya daga wajen wanda yake shi daya ne rak tal shi ne sallamawa Allah matsarkaki, addini wurin Allah shi ne addinin muslunci, makasudi cikin wannan aya mai daraja:

 (إنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللهِ الإسْلامُ )

Lallai addini a wurin Allah shi ne muslunci.[5]

Shi ne muslunci da ma'ana mafi gamewa, a wani karo kuma akan amfani da Kalmar islam cikin kur'ani a nufi kebantacciyar ma'ana da ita, wacce shi ne bijiro da addinai da shari'o'in sama daban kamar yahudiyya da nasraniyya, lallai Allah ya hattama annabta da manzanci annabawa da addini muslunci mai karkata ga gaskiya, hakika ya sanyawa dukkanin annabi tsari hanya da shari'a, sai dai cewa ya hattama hanyoyi da shari'o'in sama da shari'ar muslunci saukakka, bai yarda ga wani mutum wani addini daban ba bayan muslunci da kebantacciyar ma'ana, kamar yadda ya zo cikin fadin sa madaukaki:

 

(وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الإسْلامِ دِينآ فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ ) ،

Duk wanda ya nemi wani addini bayan muslunci ba za a taba karba daga gare shi ba.[6]

 (اليَوْمَ أكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإسْلامَ دِينآ)

Yau ne na kammala addini gareku na cika ni'imata kanku na yardar muku muslunci a matsayin addini.[7]

 

Sai ya zama an shafe baki dayan ragowar shari'o'i, ba kuma za a kara karbar wani addini daga wani mutum ba face addinin muslunci da kebantacciyar ma'ana wanda shugaban annabawa cikamakin manzanni Muhammad bn Abdullah (s.a.w) ya zo da shi, wanda shi ne shari'ar Allah ta gaskiya wacce ta hattama shari'o'in annabawan sama, ita ce mafi kammalar shari'o'in sama kuma mafi tsinkayar farin ciki da arzikin mutum, mafi tattaro maslahohi cikin rayuwar su da makomarsu, ita ce mafi dacewa ga wanzuwa tsawon mikewar zamanunnuka, kamar yadda ta zo don ta wanzu ba zata taba canjuwa ba ko sauyawa ba cikin gundarinta da hakikaninta, tana da ubangiji da yake kareta, kamar yadda ya fada cikin bayyanannen littafin sa mai girma:

 

(إنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا الذِّكْرَ وَإنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ ).

Lallai mu ne muka saukar da Ambato lallai kuma mu ne masu bashi kariya.[8]

Wannan aya ta game ta kuma tattaro dukkanin abin da mutum yake bukata daga tsari nasa nashi kadai da kuma tsarinsa tare da jama'a da siyasa da sakafa da makamantan su, ita shari'ar muslunci addini ce da daula, daular gaskiya wacce karkashin inuwarta farin cikin mutum yake da daddadar rayuwa gare shi.

Ya zama dole a tilasta tarihi kamar yadda ya zo cikin maganarsu-wani mutum ya zo a wannan zamani da muslunci zai bazu ya yadu ya karfafa ya daukaka, lallai shi muslunci shi ke daukaka ba wani abu da yake daukaka kansa, ya mamaye duniya da adalcinsa da tsarinsa madaukaki da dokokinsa katangaggu ta yanda Allah ya yi mana alkawarin haka, ba kuma zai taba saba alkawarin sa ba, lallai da sannu bayin Allah nagargaru za su gaji kasa, sai dai cewa dole fa da farko mu fara da sauya kawukanmu, kamar yadda Allah matsarkaki ya fadi cikin littafin sa mai daraja:     

 (ذَلِکَ بِأنَّ اللهَ لَمْ يَکُ مُغَيِّرآ نِعْمَةً أنْعَمَهَا عَلَى قَوْمٍ حَتَّى يُغَيِّرُوا مَا بِأنفُسِهِمْ ).

Wancan lallai Allah bai kasance yana canja wata ni'ima da ya ni'imta wasu mutane da ita ba har sai sun canja da kawukansu.[9]

 

Ya zama dole mu san musluncinmu kamalar sani kuma mu dabbaka shi cikin dukkanin janibobin rayuwarmu ta daidaiku da ta zamantakewa da sauran jama'a.

Sannan farkon addini shi ne sanin Allah mabuwayi matsarkaki madaukaki, hakan sakamakon abin da ya bamu daga karfin tunani ya kuma yi mana kyautar hankali da ludufin sa, ya umarce mu da muyi tunani cikin halittunsa mu lura cikin kufaifayin kagarsa da hikimarsa mu san hankali cikin ayoyin sa na sasanni da wadanda suke cikin kawukanmu har ya bayyana lallai cewa shi gaskiya ne shi kadai babu abokin tarayya gare shi

 

(سَنُرِيهِمْ آيَاتِنَا فِي الآفَاقِ وَفِي أنْفُسِهِمْ حَتَّى يَـتَـبَـيَّنَ لَهُمْ أنَّهُ الحَقُّ ).

Da sannu zamu nuna musu ayoyinmu cikin sasanni da cikin kawukan su har sai ya bayyana gare su lallai cewa shi gaskiya ne.[10]

 

Hakika Allah ya zargi masu makauniyar biyayya da masu bin zarge-zargensu cikin tauhidin sa da dayantar sa, bari tilas a samu ilimi da yakini da ijtihadi cikin sanin mafara da makoma da abin da ke tsakankaninsu daga sanin siffofin mafara da annabta da imamanci, wannan shi ne abin da lafiyayyar halittar mutum ke cewa, ba zai yiwu ga mutum mai hankali ba ya yi watsi da al'amuran sakamakon kasantuwar mutum ma'abocin sasanni guda uku:hankali,ruhi,gangar jiki, to ya zama tilas gare shi ya nemi mai kammala masa hankalin sa mai bashi tarbiyar ruhi mai ladabtar da gangar jikin sa, babu abin da ke iya kosar da kishirwar da hankali ke ciki face ingantattun akidu lafiyayyu daga dukkanin shakku da wahamai da shubuhohi da karkacewa, babu abin da ke daukar nauyin bayanin wannan ingantattun akidu sai ilimul Kalam (ilimin sanin akida) babu abin da ke tsaftace zuciya da haskakata da tsarkake ruhi da tarbiyantar da nafsu daga munanan siffofi da daga halaye marasa nagarta face ilimin Akhlak da halaye da dabi'u nagari.

mai tarbiyantar da gangar jiki kan kyawawan al'adu da ayyuka nagargaru da da'ar Allah matsarkaki daga ibadoji wadanda ke danganta mutum da ubangijin sa, haka daga mu'amaloli wadanda suke tsara rayuwar sa ta zamantakewa,to babu wanda ya dau nauyin bayanin wannan sai ilimin fikihu.

Wadannan su ne ilimai da mutum ke azurtuwa da kuma samun farin cikin duniya da lahira tare da samun tsira daga abubuwa masu halakarwa, amma ragowar to dukkanin su saura ne.

Ta yiwu daga wannan tushen ne manzon Allah (s.a.w) ya iyakance ilimi cikin abubuwa uku kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja:     

 «عن أبي الحسن مولانا موسى بن جعفر  8، قال : دخل رسول الله  9 المسجد، فإذا جماعة قد أطافوا برجلٍ ، فقال : ما هذا؟ فقيل : علّامة ، فقال  : وما العلّامة ؟ فقالوا: أعلم الناس بأنساب العرب ووقائعها وأيام الجاهلية والأشعار العربية . قال : فقال النبيّ  9: ذاک علمٌ لا يضرّ من جهله ، ولا ينفع من علمه . ثمّ قال النبيّ  9: إنّما العلم ثلاثة : آيةٌ محكمة ، أو فريضةٌ عادلة ، أو سنّةٌ قائمة ، وما خلاهنّ فهو فضل ».

Daga Abu Hassan maulana Musa bn Jafar (as) ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya shiga masallaci shigar bsa ke da wuya sai ga wasu mutane sun kewaye wani mutum, sai ya ce: me ke faruwa ne? sai aka ce masa Allama ne, sai ya ce: mene ne Allama kuma? Sai aka ce mafi sanin cikin mutane cikin ilimin nasabar larabawa da waki'o'insu da wake-wakensu, ya ce: sai annabi (s.a.w) ya ce: wancan wani ilimi ne da bai cutar da wanda ya jahilce shi bai kuma amfanar da wanda ya san shi, sannan annabi (s.a.w) ya ce: kadai dai ilimi na cikin abubuwa uku: aya bayyananniya, farilla adala, sunna tsayayya, duk wani abu koma bayansu abin da suka ci suka rage ne.   

Ilimi mai amfani wanda jahiltarsa ke cutar da mutum a ma'aunin annabi (s.a.w) kadai shi bayani ne daga jumlar abubuwa uku: aya bayyananniya wanda shi ne (ilimin sanin akidu) farilla adala wanda shi ne (ilimin fikihu) sai kuma sunnoni da ladubba tsayayyu wanda su ne (ilimin Akhlak). Dukkanin ragowar ilimai saura ne da aka ci aka rage kadai na da ma'anar ragowa ko kuma muce kari ne kan wadanacan.[11]

ya zama dole mu nemi fahimtar addinin gaskiya mu zurfafa neman fahimta cikinsa kamar yadda Allah da manzon sa da Ahlil-baiti suka umarce mu da hakan hakika an karbo hadisi daga maulana imam Sadik (as) cewa shi ya ce:

«تفقّهوا في الدين ، فإنّه مَن لم يتفقّه في الدين فهو أعرابي ، إنّ الله يقول  : (لِيَـتَفَقَّهُوا فِي الدِّينِ وَلِيُـنذِرُوا قَوْمَهُمْ إذَا رَجَعُوا إلَيْهِمْ لَعَلَّهُمْ يَحْذَرُونَ ) ».

ku nemi fahimta cikin addinin Allah duk wanda bai neman fahimta cikin addinin Allah lallai shi balaraben kauye ne.[12]lallai Allah yana cewa: (domin su nemi fahimta cikin addininin Allah su kuma gargadi mutanensu idan sun dawo zuwa gare su tsammanin su sa gargadu).[13]

A wani wajen kuma Imam (as) yana cewa

«ليت السياط على رؤوس أصحابي حتّى يتفقّهوا في الحلال والحرام ».

inama akwai mai bulala tsaye kan sahabbaina har sai sun nemi fahimta cikin halali da haramun.

 Saboda haka wajibi kanmu mu fahimci addini muslunci kamar yadda yake a hakikarsa.

Take na farko da addinin muslunci ya fara bijiro da shi shi ne taken tauhidi cikin fadin manzo mai karamci

(قولوا لا إله إلّا الله تفلحوا).

Ku ce babu abin bauta da gaskiya sai Allah zaku samu rabauta.

Sai ya sanya tsira da rabauta cikin Kalmar tauhidi, ta yanda ya gwamutsa bara'a da wilaya cikin akidu, ta yanda yayi watsi da baki dayan ubangijan boge ya kore su ya tabbatar da mahalicci makagi abin bauta abin kauna matsarakaki madaukaki, daga bayan na kuma wannan watsi da korewa da kuma tabbatarwa yana tajalli cikin fikihun muslunci, lallai shi fikihu an sanya isdilahin sa cikin wajiban sa da muharraman sa, fikihu shi ne yake tsayuwa da zurfafawa cikin ga wancan shu'uri da take na imani, lallai shi fikihu wani bayani da yake a aikace a dabbake ga garizar imani, shike misalta mana da jikkanta mana wancan take na korewa da tabbatarwa bara'a da wilaya.

Fikihu bayani a aikace ga akidar muslunci, saboda haka kyawawan halaye da dabi'un Akhlak ba wani abu bane face watsi da wofuntuwa daga dabi'u da halaye marasa nagarta kamar misalin riya da hassada da girman kai da jahilci, sannan kuma tabbatar da siffofi managarta godaddu cikin zuciya da ruhi da ado da su, kamar misalin iklasi da tawali'u da ilimi.

Hadafi daga dukkanin wadannan shi ne tarbiyantar da mutum da kammaluwar sa da azurtar sa har ya kai ga kololuwar kamala, lallai ga ubangijinka komawa take, ga Allah makura take, lallai gare shi zamu koma, gare shi al'amura za su koma.

Sai ya halicci mutum wannan dai wanda ke raya cewa shi wata `yar kankanuwar halitta ce sai dai cewa cikinsa mafi girman duniya ta dunkule, cikin duniyar mada da duniya badini ma'anawi ke tattare, duniyar dabi'a (nature) da duniyar abin da ke bayan dabi'a (methapysics) ya halicce shi daga kasa turbaya, sannan Allah matsarakaki ya ce:       

 (وَنَفَخْتُ فِيهِ مِنْ رُوحِي ) .

Nayi busa cikin sa daga ruhina.[14]

Sannan Allah ya yabi kansa da halittarsa bayan haka cikin fadinsa:

(فَـتَبَارَکَ اللهُ أحْسَنُ الخَالِقِينَ ) .

Albarku sun tabbata ga Allah mafi kyawun masu halitta.[15]

Ya halicci mutum ya hore masa dukkanin abin da yake sammai da kasa ba don komai ba sai don ya san ubangijin sa ya kuma bauta masa, mutum bai gushe ba wannan halitta jahiltatta yana bincike da neman kamala da azurtar sa tun lokacin da faratan sa suka fara tsira da bayyana, yana ta bakin kokarin sa da kaikawo don tsinkayar sirrin halitta da falsafa da hikimar rayuwa, sirrin halitta da falsafar rayuwa ba komai bane face ilimi da ibada, daga karshe manyan malamanmu Allah ya saka musu da mafi alheri sakamako sun sanyawa addini asalai da rassa.


[1] Alu Imran:19

[2] Alu Imran:85

[3] Ma'ida:3

[4] Ma'alimul dini:19

[5] Alu imrana:19

[6] Alu Imran:58

[7] Ma'ida3

[8] Hijri:9

[9] Anfal:53

[10] Fussilat:53

[11] Ma'alimud dini:21

[12] Ma'alimud dini:18

[13] Tauba:12

[14] Hijri:29

[15] Muminun:14

Tura tambaya