gabatarwa

 Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Kyawawan dabi’un Annabawa a cikin kur’ani mai girma

Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya sanar da mutum abin da bai sani ba, ya turo da Annabawa da littafi da ilimi da mizani da fasahar Magana, tsira da aminci su kara tabbata ga mafi daukakar halittu shugaban larabawa da Ajamawa Muhammad da iyalan sa jagororin dukkanin al’ummu.

Bayan haka: atakaicen takaitawa zamu yi bayani da Karin haske kan kyawawan dabi’un Annabawa da manzanni kan hasken kur’ani mai girma, wannan littafi da babu kokwanto cikin sa shiriya ga masu takawa, yana shirywarwa zuwa ga abin da ya fi kasantuwa mafi daidaito cikin rayuwar mutum, domin mutum ya rayu kyakkyawar rayuwa cikin izza da karamci yana kuma bushara ga muminai, hakan yana kasancewa ne cikin jigo biyu: