Jigo na farko: kyawawan dabi’u da motsin Annabawa

Cikin sharar fage da mukaddima mu na cewa: idan muna son bijiro da maudu’I ko wane mafhumi daga gamagarin mafahim kulliya, sannan mu dabbaka su a aikace da sulukance cikin jama’ar mu musulmai ko ta dukkanin mutane kan dukkanin matakai cikin kowanne fagen rayuwa da sasannin su shin cikin daidaiku ne ko jama’a, da abin da ya dace da sassabawar dabakokin mutan, hakan kan tsarin hankali da tsarin zamani, da tunkude shubuhohi da warware matsaloli dukkanin su karkashin kur’ani kia girma da tafsirin ayoyin sa kan sabuwar fahimta bisa ma’aunan addini da hukunce-hukuncen shari’a ba tare da biyewa tafsiri da fassara da ra’ayin kashin kai wand ashari’a ta yi hani kansa, sannan hakan ya kasance cikin bijiro da nukdodi masu fading aske, cikin wata da’ira da za ta tattaro dukkain iliman muslunci da sakafar sa ta asali da wayewar sa mai daraja, ta hanyar kawo akidun gaske da lafiyayyen suluki cikin mihwari na tushe wanda kur’ani da kiran ubangiji wanda cikin sa rayuwar mai kyawu take yake gudana kansa, hakika kur’ani kamar yanda yayi bayanin kansa da kansa, cikin akwai bayani komai, lallai shi bayani ne da isarwa ga baki dayan mutane, ya zama wajibi garemu da farko mu tsaya kan muhimmman haduffan kur’ani mai girma ko da cikin sauri ne, da kuma abin da yake kira zuwa gareshi daga sanin gaskiya da ahlinta, sannan mu cigaba mu tsunduma cikin maudu’in mu cikin wannan dan karamin littafi da takaitaccen sako wato kyawawan dabi’un Annabawa cikin kur’ani mai girma, daga muhimman haduffa da abubuwan da kur’ani ya tattaru kansa sune abubuwan da zasu nan gaba kamar haka:   


1-shiriya ta shari’a:

Da farko ga dukkanin mutane baki daya cikin gamarin shiriya, na biyu ga masu takawa cikin zuciya da kebantacciyar shiriya daga rahama da jin ka, hakan na kasancewa bayan sun karbi gamagarin shiriya da abin da take lazimtawa da hukunce-hukuncenta da natijojin ta da abin da take jawowa.

 (شَهْرُ رَمَضَانَ آلَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ آلْقُرْآنُ هُدىً لِلنَّاسِ وَبَيِّنَاتٍ مِنَ آلْهُدى وَآلْفُرْقَانِ )[1] .

 Watan Ramadan wanda a cikin sa aka saukar da kur’ani shiriya ga mutane da hujjoji daga shiriya da rarrabewa.[1]

(ذَلِکَ آلْكِتَابُ لاَ رَيْبَ فِيهِ هُدىً لِلْمُتَّقِينَ * آلَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ وَيُقِيمُونَ آلصَّلَوةَ وَمِمَّا رَزَقْنَهُمْ يُنْفِقُونَ *وَآلَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْکَ وَمَا أُنْزِلَ مِن قَبْلِکَ وَبِالاخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ * أُوْلَئِکَ عَلَى هُدىً مِنْ رَبِّهِمْ وَأُولَئِکَ هُمُ آلْمُفْلِحُونَ )[2] .

Wancan littafin babu kokwanto cikin sa shiriya ne ga masu takawa* sune wadanda suke Imani da gaibu suke tsayar da sallah daga abin da muka azurta su suna ciyarwa* da kuma wadanda suke Imani da abin da muka saukar gareka da abin da muka saukar gabanin ka dangane da lahira suna masu yakini* wadancananka suna kan shiriya daga ubangijin su kuma wandacananka sune rabautattu.[2]

2-Bayani da wa’azi:  

 (هذَا بَيَانٌ لِلنَّاسِ وَهُدىً وَمَوْعِظَةٌ لِلْمُتَّقِينَ )[3] .

Wannan bayani ne da kuma shiriya da wa’azi ga masu takawa.[3] 

(وَآذْكُرُوا نِعْمَةَ آللهِ عَلَيْكُمْ وَمَا أَنْزَلَ عَلَيْكُم مِنَ آلْكِتَابِ وَآلْحِكْمَةِ يَعِظُكُم بِهِ )[4] .

Ka tuna da ni’imar Allah kanku da abin da ya saukar kanku daga littafi da hikima yana yi muku wa’azi da shi 

(وَلَقَدَ أَنزَلْنَا إِلَيْكُمْ آيَاتٍ مُّبَيِّنَاتٍ وَمَثَلاً مِنَ آلَّذِينَ خَلَوْا مِن قَبْلِكُمْ وَمَوْعِظَةً لِّلْمُتَّقِينَ )[5] .

Hakika mun saukar muku da ayoyi da misali daga wadanda suka gabata gabaninku da wa’azi ga masu takawa.[4]

3-fitar da mutane da duhun bata zuwa hasken shiriya: 

 (كِتَابٌ أَنزَلْنَاهُ إِلَيْکَ لِتُخْرِجَ آلنَّاسَ مِنَ آلظُّلُمَاتِ إِلَى آلنُّورِ بِإِذْنِ رَبِّهِمْ إِلَى صِرَاطِ آلْعَزِيزِ آلْحَمِيدِ)[6] .

 Littafi da muka saukar da shi domin ka fitar da mutane daga duhhai zuwa haske da izinin ubangijin su ya zuwa tafarkin mabuwayi godadde.

4- sabati da bushara:

 (قُلْ نَزَّلَهُ رُوحُ آلْقُدُسِ مِن رَّبِّکَ بِالْحَقِّ لِيُثَبِّتَ آلَّذِينَ آمَنُوا وَهُدىً وَبُشْرَى لِلْمُسْلِمِينَ )

Kace Ruhu tsarkakke ya saukar d ashi daga ubangijinka da gaskiya domin ya tabbatar wadanda sukai Imani da shiriya da bushara ga musulmai.

(تِلْکَ آيَاتُ آلْقُرْآنِ وَكِتَابٍ مُبِينٍ * هُدىً وَبُشْرَى لِلْمُؤْمِنِينَ * آلَّذِينَ يُقِيمُونَ آلصَّلوةَ وَيُؤْتُونَ آلزَّكوةَ وَهُم بِالاْخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ )[7] .

 Wancan ayoyi ne na kur’ani da littaf mabayyani* shiriya da bushara ga muminai* wadanda suke tsayar da sallah suke bada zakka suna masu yakini da lahira.

5-tunatarwa:

 (طه * مَا أَنزَلْنَا عَلَيْکَ آلْقُرْآنَ لِتَشْقَى * إِلاَّ تَذْكِرَةً لِمَن يَخْشَى )[8] .

Taha* bamu saukar da kur’ani kanka domin ka sha wahala ba* face tunatarwa ga wanda yake tsoro. 

(كَلاَّ إِنَّهُ تَذْكِرَةٌ * فَمَن شَاءَ ذَكَرَهُ *  وَمَا يَذْكُرُونَ إِلاَّ أَن يَشَاءَ آللهُ هُوَ أَهْلُ آلتَّقْوَى وَأَهْلُ آلْمَغْفِرَةِ )[9] .

A’ a lallai shi tunatarwa ne* duk wanda ya so zai ambace shi* basa ambata face Allah ya so shi ne Ahalin takawa da gafara.

 

(فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاهُ بِلِسَانِکَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ )[10] .

Kadai dai mun saukake shi a harshenka saran su sa tunatu. 

(كِتَابٌ أُنْزِلَ إِلَيْکَ فَلاَ يَكُن فِي صَدْرِکَ حَرَجٌ مِنْهُ لِتُنذِرَ بِهِ وَذِكْرَى لِلْمُؤْمِنِينَ )[11] .

Littafi ne da aka saukar da shi gareka kada wata takura ta kasance cikin kirjinka daga gareshi domin kayi gargadi da shi da kuma tunatarwa ga muminai.

Shi kur’ani littafi ne na Allah da ya saukar da shi ga Muhammad (s.a.w) wanda ake bautawa ubangiji da yin tilawar sa shi ne wannan da yake tsakanin bangwaye biyu, daga fadin sa madaukaki cikin suratu Hamdu:  

بِسْمِ اللهِ آلرَّحْمنِ آلرَّحِيمِ آلْحَمْدُ للهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya zuwa fadinsa (daga aljanu da mutane) farkon kur’ani ya fara da harafin ba’un ya kuma karkare da harafin sinun ma’ana wannan kadai kamar yanda fadin larabawa (haza wa bas).

Kur’ani a luggance: masdari ne na biyu da kara’a yakara’u kur’anan kan wazanin (fulanu) da wasalin damma kamar misalin gufranu, yana da ma’anar tattarowa da rungumowa an kirashi da makaru’i bisa sunan san a maf’uli a masdari, shi kur’ani masdari da aka nufi sunan maf’ulin sa daga gareshi ma’ana mak’ru’u tattare rungumamme ba’arin sag a ba’ari.

Sannan a isdilahance: shi littafi ne da aka saukarwa Annabin muslunci Muhammad (s.a.w) sai ya zamanto kamar misalin ilmul shaksi, sa’ilin da aka ambace ana fahimtar saukakken littafi daga gareshi, sannan ana kiransa da hakan ta hanyar tarayya lafazi kan majmu’u din kur’ani baki dayan sa, haka ma kan kowacce aya daga ayoyin sa, abin da yake gasgata hakan shi ne duk sanda kaji wani yana karanta wata aya sai kace yana karanta kur’ani mai girma. 

 (وَإِذَا قُرِئَ آلْقُرْآنُ فَاسْتَمِعُوا لَهُ وَأَنْصِتُوا لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ )[12] 

Idan aka karanta kur’ani ku gaza kunnuwanku ku saurare shi ku yi shiru saranku ku samu rahama.

Wasu sun ce ana kiransa da kur’ani sakamakon ya tattaro na farko dana karshe da kuma abin da yake cikin litattafan sama.

 (وَنَزَّلْنَا عَلَيْکَ آلْكِتَابَ تِبْيَاناً لِكُلِّ شَيْء)[13]  (مَا فَرَّطْنَا فِي آلْكِتَابِ مِن شَيْءٍ)[14] .

Kuma mu saukar da maka da wannan littafi faiface bayani ga komai.

Bamu yi gangancin barin wani abu cikin littafi.

6- ibada da iklasi:

 

 (تَنزِيلُ آلْكِتَابِ مِنَ آللهَ آلْعَزِيزِ آلْحَكِيمِ * إِنَّا أَنزَلْنَا إِلَيْکَ آلْكِتَابَ بِالْحَقِّ فَاعْبُدِ آللهَ مُخْلِصاً لَهُ آلدِّينَ )[15] .

Saukar da littafi daga Allah mabuwayi mai hikima* mun saukar maka da littafi da gaskiya ka bautawa Allah kana mai tsarkake addini gareshi.

7- yana tausasa zuciya: 

 (آللهُ نَزَّلَ أَحْسَنَ آلْحَدِيثِ كِتَاباً مُتَشَابِهاً مَثَانِيَ تَقْشَعِرُّ مِنْهُ جُلُودُ آلَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُمْ ثُمَّ تَلِينُ جُلُودُهُمْ وَقُلُوبُهُمْ إِلَى ذِكْرِ آللهَ ذلِکَ هُدَى اللهَ يَهْدِي بِهِ مَنْ يَشاءُ وَمَنْ يُضْلِلِ اللهُ فَما لَهُ مِنْ هادٍ)[16] .

Allah ya saukar mafi kyawun zance littafi mai kamanceceniya da juna wanda ake maimaita karatun sa fatocin wadanda suke tsoran ubangijin su tana kwansarewa daga gareshi sannan fatocin su suyi taushi da zukatun su zuwa ga ambaton Allah wadancananka shiriya Allah yana shiryar da wanda ya so duk wanda Allah ya batar bai da mai shiryar da shi.

8- mai bushara da gargadi: 

 (كِتَابٌ فُصِّلَتْ آيَاتُهُ قُرْآناً عَرَبِيّاً لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ * بَشِيراً وَنَذِيراً فَأَعْرَضَ أَكْثَرُهُمْ فَهُمْ لاَ يَسْمَعُونَ )[17]

Littafi ne da aka faiface ayoyin sa abin karantawa na larabci ga mutanen da suke sani* mai bushara da gargadi sai akasarin su ka juya ba alhalin su basa ji.

  (آلْحَمْدُ للهِ آلَّذِي أَنزَلَ عَلَى عَبْدِهِ آلْكِتَابَ وَلَمْ يَجْعَل لَّهُ عِوَجا * قَيِّماً لِّيُنذِرَ بَأْساً شَدِيداً مِن لَّدُنْهُ وَيُبَشِّرَ آلْمُؤْمِنِينَ آلَّذِينَ يَعْمَلُونَ آلصَّالِحَاتِ أَنَّ لَهُمْ أَجْراً حَسَناً * مَاكِثِينَ فِيهِ أَبَداً)[18] .

 godiya ta tabbata ga Allah wand aya saukar wa da bawan sa littafi bai sanya karkatacce ba* madaidaici domin ya yi gargadi da azaba mai tsanani daga gareshi ya kuma yi bushara ga muminai wanda suke aikata ayyuka nagari da cewa lallai suna da lada mai kyawu* suna masu zama cikin sa har abada.

9- shi waraka ne ga muminai:

 (قُلْ هُوَ لِلَّذِينَ آمَنُوا هُدىً وَشِفَاءٌ)[19] .

 Kace shi ga wadanda suka yi Imani shiriya ne da waraka.

(وَنُنَزِّلُ مِنَ آلْقُرْآنِ مَا هُوَ شِفَاءٌ وَرَحْمَةٌ لِلْمُؤْمِنِينَ وَلاَ يَزِيدُ آلظَّالِمِينَ إِلاَّ خَسَاراً)[20] .

Muna saukar wa daga kur’ani abin da yake waraka da rahama ga muminai babu abin da yake karawa azzalumai face hasara.

10- shi gaskiya da mizani: 

آللهُ آلَّذِي أَنزَلَ آلْكِتَابَ بِالْحَقِّ وَآلْمِيزَانَ )[21] .

Allah shi ne wanda ya saukar da littafi da gaskiya da kuma mizani.

11- yana shirywarwa zuwa gaskiya da tafarki madaidaici: 

 (كِتَاباً أُنزِلَ مِن بَعْدِ مُوسَى مُصَدِّقاً لِمَا بَيْنَ يَدَيْهِ يَهْدِي إِلَى آلْحَقِّ وَإِلَى طَرِيقٍ مُسْتَقِيمٍ )[22] .

Littafi ne da aka saukar bayan Musa mai gasgata abin da yake gabansa yana kuma shiryarwa zuwa gaskiya da hanyar madaidaiciya.

12- a cikin sa akwai ilimin da ba a sani ba: 

 (كَمَا أَرْسَلْنَا فِيكُمْ رَسُولاً مِنْكُمْ يَتْلُوا عَلَيْكُمْ آيَاتِنَا وَيُزَكِّيكُمْ وَيُعَلِّمُكُمُ آلْكِتَابَ وَآلْحِكْمَةَ وَيُعَلِّمُكُمْ مَا لَمْ تَكُونُوا تَعْلَمُونَ )[23] .

Kamar yanda muka aiko da manzo cikin ku daga gareku yana karanta muku littafi yana tsarkakeku yana sanar da ku littafi da hikima yana sanar da ku abin da baku kasance kuna sani ba.

13- Albarka da rahama: 

 (وَهذَا كِتَابٌ أَنْزَلْنَاهُ مُبَارَکٌ فَاتَّبِعُوهُ وَآتَّقُوا لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ )

Wannan littafi ne da muka saukar da shi mai albarka ku bi shi ku yi takawa saran ku kwa samu rahama.

  (وَإِذَا قُرِئَ آلْقُرْآنُ فَاسْتَمِعُوا لَهُ وَأَنْصِتُوا لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ )[25] .

Idan an karanta kur’ani ku saurare shi kuyi shiru saranku kwa samu rahama.

14- Ambato da kuma alkawarin azaba: 

 

وَكَذلِکَ أَنزَلْنَاهُ قُرْآناً عَرَبِيّاً وَصَرَّفْنَا فُيهِ مِنَ آلْوَعِيدِ لَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ أَوْ يُحْدِثُ لَهُمْ ذِكْراً)[26] .

Haka zalika muka saukar da shi abin karantawa balarabe muka karkatar cikin sa daga tsoratarwa saran su sa yi takawa ko ya haifar musu da wani wa’aztuwa

15- misalsalai don fadakuwa da daukar darasi: 

15 ـ وأمثال للعبر والدروس : (وَلَقَدْ صَرَّفْنَا فِي هذَا آلْقُرْآنِ لِلنَّاسِ مِن كُلِّ مَثَلٍ وَكَانَ آلاْنسَانُ أَكْثَرَ شَيْءٍ جَدَلاً)[27]

Hakika mun jujjuya cikin wannan kur’ani ga mutane aga dukkanin misali mutum ya kasance mafi jidali abu.

  (وَلَقَدْ صَرَّفْنَا لِلنَّاسِ فِي هذَا آلْقُرْآنِ مِن كُلِّ مَثَلٍ فَأَبَى أَكْثَرُ آلنَّاسِ إِلاَّ كُفُوراً)[28]

 Hakika mun jujjuya ga mutane cikin kur’ani daga dukkanin misali sai galibin mutane suka ki sai dai kafircewa.

16- gasgata Annabtar cikamakin annabawa da manzancin da suka gabata:

 (وَمَا كَانَ هذَا آلْقُرْآنُ أَن يُفْتَرَى مِن دُونِ آللهَ وَلكِن تَصْدِيقَ آلَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ وَتَفْصِيلَ آلْكِتَابِ لاَ رَيْبَ فِيهِ مِن رَبِّ آلْعَالَمِينَ )[29]

Wannan kur’ani bai kasance ba a kage shi daga koma bayan Allah sai dia cewa shi gasgatawa gabansa da faifaicewa littafi babu kokwanto cikinsa daga mai rainon talikai. 

(وَهذَا كِتَابٌ أَنْزَلْنَاهُ مُبَارَکٌ مُصَدِّقُ آلَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ وَلِتُنذِرَ أُمَّ آلْقُرَى وَمَنْ حَوْلَهَا)[30] .

Wannan littafi ne da muka saukar da shi mai gasgatawa wanda yake gaban sa domin ka gargadi uwar alkaryu da wadanda suke kewaye da ita.

17- yana shiryawa zywa shiriya yana umarni da kyakkyawa da adalci:

 (قُلْ أُوحِيَ إِلَيَّ أَنَّهُ آسْتَمَعَ نَفَرٌ مِنَ آلْجِنِّ فَقَالُوا إِنَّا سَمِعْنَا قُرْآناً عَجباً * يَهْدِي إِلَى آلرُّشْدِ فَآمَنَّا بِهِ وَلَن نُشْرِکَ بِرَبِّنَا أَحَداً)[31] .

 Kace an mini wahayi lallai wasu daga aljannu sun ji sai suka ce lallai mu mun ji abin karantawa mai ban mamaki* yana shiryarwa zuwa ga shiriya sai muka yi imani da shi bau tarayya da ubangijin mu da wani abu ba.

(إِنَّ آللهَ يَأْمُرُ بِالْعَدْلِ وَآلاْحْسَانِ وَإِيتَاءِ ذِي آلْقُرْبَى وَيَنْهَى عَنِ آلْفَحْشَاءِ وَآلْمُنكَرِ وَآلْبَغْيِ يَعِظُكُمْ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ )[32] .

Allah ya umarni da adalci da ihsani da baiwa ma’abocin zumunci yana kuma hani da alfasha da munkari da zalunci yana muku wa’azi saran ku kwa tuna.

18- yana shiryarwa zuwa ga wacce da tafi daidaito: 

 (إِنَّ هذَا آلْقُرْآنَ يَهْدِي لِلَّتي هِيَ أَقْوَمُ وَيُبَشِّرُ آلْمُؤْمِنِينَ آلَّذِينَ يَعْمَلُونَ آلصَّالِحَاتِ أَنَّ لَهُمْ أَجْراً كَبِيراً)[33] .

Lallai wannan kurani yana shiryarwa zuwa zywa ga wacce tafi daidaito yana kuma bushara ga muminai wadanda suka aikata ayyuka nagari lallai suna da lada babba.

19- bayyannun ayoyi: 

 (وَمَا كُنتَ تَتْلُوا مِن قَبْلِهِ مِن كِتَابٍ وَلاَ تَخُطَّهُ بِيَمِينِکَ إِذا لاَرْتَابَ آلْمُبْطِلُونَ * بَلْ هُوَ آيَاتٌ بَيِّنَاتٌ فِي صُدُورِ آلَّذِينَ أُوتُوا آلْعِلْمَ وَمَا يَجْحَدُ بِآيَاتِنَا إِلاَّ آلظَّالِمُونَ )[34] .

Baka kasance kana karantawa gabanin sa daga littafi baka zana shi da hannun ka da hakan ta kasance da batattu sun kawo kokwanto* bari da shi ayoyi ne bayyanannu cikin kirazan wadanda aka baiwa ilimi babu mai musu da ayoyin mu face azzalumai.

20- hujjoji ga mutane:

 (هذَا بَصَائِرُ لِلنَّاسِ وَهُدىً وَرَحْمَةٌ لِقَوْمٍ يُوقِنُونَ )[35] .

Wannan kur’ani hukunce-hukuncen nutsuwa ga mutane kuma shiriya da rahama ga masu yakini.

21-faifaice Magana: 

 (إِنَّهُ لَقَوْلٌ فَصْلٌ * وَمَا هُوَ بِالْهَزْلِ )[36] .

Lallai shi faifaice Magana* shi ba maganar wargi bane.

22- karya bata zuwar masa: 

 (إِنَّ آلَّذِينَ كَفَرُوا بِالذِّكْرِ لَمَّا جَاءَهُمْ وَإِنَّهُ لَكِتَابٌ عَزِيزٌ * لاَ يَأْتِيهِ آلْبَاطِلُ مِن بَيْنِ يَدَيْهِ وَلاَ مِنْ خَلْفِهِ تَنزِيلٌ مِنْ حَكِيمٍ حَمِيدٍ * مَا يُقَالُ لَکَ إِلاَّ مَا قَدْ قِيلَ لِلرُّسُلِ مِن قَبْلِکَ إِنَّ رَبَّکَ لَذُو مَغْفِرَةٍ وَذُو عِقَابٍ أَلِيمٍ )[37] .

Wadanda suka kafirce da Ambato sa’ailin da ya zo musu lallai shi littafi ne mabuwayi* wargi bai zuwar masa daga tsakanin gaban sa da bayan sa saukarwa ne daga mai hikima godadde* babu abin da ake gaya maka face abin da aka gayawa manzanni gabaninka lallai ubangijinka tabbas ma’abocin gafara ne kuma ma’abocin ukuba mai radadi.

23- kira zuwa ga aikin da hankali da sanya hankali: 

 (لَقَدْ أَنزَلْنَا إِلَيْكُمْ كِتَاباً فِيهِ ذِكْرُكُمْ أَفَلاَ تَعْقِلُونَ )[38] .

 Hakika mun saukar muku da littafi cikin sa akwai ambatonku yanzu ba zaku hankaltu ba.

Hakan ya kasance haduffa 23 tsarkaka gwargwadon adadin shekarun aiko annabi da cika annabta da manzanci.

Wannan ishara ce ta gaggawa da kuma fihirisa takaitacciya ga mafi muhimmancin mihwarori da haduffa tsarkaka wadanda mai girma kur’ani yake neman su, sai dai cewa hadafi na farko da yake tattarowa shi ne canja daidaiku da jama’a da cirato mutum daga kogon jahicli zuwa kololuwar kamala da farin ciki a duniya da lahira, da kira zuwa rayuwa madaukakiya tsarkakka wacce zurfaffenImani da ayyuka nagari ke jagorantar ta, koma bayan wannan lallai mutum yana cikin hasara dabata, lallai shi yana son yi fajirci a gaban sa, shi ya kasance mai zaluntar kansa mai yawan jahilci da butulci, me yafi shi kafircewa?!

Na’am dole ne a koma ga kur’ani mai girma a karanta shi da sabon karatu ingantacce da ya ginu kan ma’aunan shari’a da asalan tafsiri, ta hanyar komar da tawili zuwa ga zahiri, domin mu fahimci asalan rayuwa mai cike da farin ciki da ni’ima daga gareshi, lallai shi kur’ani: (yana shiryarwa ga wacce daidaito yana kuma bushara ga muminai) shi dausayin zukata ne kuma warakar cututtuka, mabubbuga ilimummuka da ma’adanar su, fannoni, kuma shi ne mai halakar da dukkanin duhu, shi ne mafi karfafar majingina ga sani, mafi cikar ta da tabbatuwa, shi sakon Allah wanzazze, shi kira ne mai wanzuwa a tsahon zamanunnuka, shi mahaskakar ne ga wanda yake bukatar haske, yana daukakar mutun cikin matattakalolin kamala, yana kuma kaishi ga burin sa madaukaki da haduffan sa masu daukaka.

Hakika wnanan kur’ani da jazibiyar sa da fadadar sa da tattariwar say a fitar da mutane daga duhun jahiliya ya zuwa shugabancin duniya yayin hudar ranar sa amu huda, mutane sun kasance cikin wani lokaci mai tsananin duhu da zamani jahiliya

«في فتن انجذم فيها حبل الدين وتزعزعت شوارى اليقين »[40] .

 Cikin fitintinu wanda cikin su igiyar addini ta yanke rukunan yakini suka girgiza.

Mutane sun kasance mazhabobi masu rarraba, da karkace-karkace mai yawan gaske da kungiyoyi daban-daban, daga mai suranta Allah da halittun sa ko kuma mai karkacewa cikin sunan sa, ko kuma mai ishara zuwa ga wanin sa. Nahjul balaga.

Cikin wannan yanayi da yake cike da duhu sautin kur’ani ya tashi ya daga domin yantar da mutum da kwance masa dabaibayi da sasari, domin fitar da shi daga duhu zuwa haske, da tseratar da shi daga mahalakar kafirci da tarkon shirka ya zuwa kololuuwar tauhidi da fadar Imani ta hanyar koyarwar ginanna da hukunce-hukunce yardaddu karfafa, domin Kalmar tauhdi ta yadu cikin zuciyar say a koma zuwa ga ubangijin sada yardajjen rai mai yarda.

Kur’ani mai girma ya zo ne domin `yantar da mutum da kwance masa sasari da dabaibayi, da kuma ceton jama’a daga faratan jahilci da zalunci da ta’addanci kan wasu, al’ummar jahiliya sun kasance a wancan lokaci baki dayan sa yana mai cike da rayuwar dabbanci da tsoro da razani da kashe binne `ya’ya mata da ransu da zubar da jini da jahilci da rashin aminci da tabbaci, kamar yanda sarkin muminai Ali (a.s) yake siffanta mana haka cikin Nahjul balaga: (cikin fitintinu da suka tattake su da kofutan su suka take su da duhun su, suka tsayu kan kafadun su, su cikin wadannan fitintinu suna firgice sun gigice suna cikin jahilci sun fitinu cikin mafi alherin gida Makka da mafi sharrin makotam barcinta ido bude, kwallin ta hawaye, a cikin kasar da malamin ta yana cikin takunkumi, amma kuma jahilin ta shi ne abin girmamawa.

Cikin misalin wannan al’umma da take ciki da bakin duhu kura’ni mai girma ya sauka, da karamcin sa da karamar sa ya fitar da mutane ya kama hannun su ya kai su ga kololuwar kamala da farin ciki, har ta kai ga suna tserereniya ya zuwa ayyukan alheri, suna neman shahada cikin tafarkin Allah da dukkani fadadar kirji, akai watsi da banbance matsayi na  zamantakewa, da hukumar danniya da jari hujja da gurguzu-kamar yanda ake fadi a wannan zamani, kur’ani ya kawo wani tsari da yak dacewa da tsarin halittar mutumtaka da yake jagoranci da adalci da ihsani da rahama da aminci    

 (وَإِذَا جَاءَکَ آلَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِآيَاتِنَا فَقُلْ سَلاَمٌ عَلَيْكُمْ كَتَبَ رَبُّكُمْ عَلَى نَفْسِهِ آلرَّحْمَةَ )[43] .

Idan wadanda sukai Imani suka zo wajen ka to kace aminci ya tabbata a gareku ubangiji ya wajabta rahama a kansa. 

(يَا أيُّهَا آلَّذِينَ آمَنُوا آدْخُلُوا فِي آلسِّلْمِ كَافَّةً وَلاَ تَتَّبِعُوا خُطُوَاتِ آلشَّيَطانِ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُبِينٌ )[44] .

Yaku wadanda kukai Imani ku shiga cikin muslunci baki daya kada ku bi tattakin shaidan lallai shi gareku makiyi ne mabayyani.

matukar mutane sukai riko da kur’ani za su azurtu, idna ka ga musulmai sun fada cikin tabarbarewa da ci baya, to lallai sun kauracewa kur’ani cikin matakin aiki da shi sun wadatu da iya zahirin sa da sunan sa, babu abin da ya rage daga muslunci face suna babu abin da ya rage daga kur’ani sai zanen sa. Lallai kur’ani mai girma bai gushe ba har abada ba zai taba gushewa ba yana shiryarwa ya zuwa wacce take mafi daidaito  

 (وَيَضَعُ عَنْهُمْ إِصْرَهُمْ وَآلاْغْلاَلَ آلَّتِي كَانَتْ عَلَيْهِمْ )[45] .

Yana dauke musu nauyin su daga barin su da sasarin da ya kasance kansu.

Shi ne tafarki zuwa ga yanci da karama da mutumtaka da yantuwa daga bautar wanin Allah matsarkaki.

Ina hada ku da Allah ina hadaku da Allah kan wannan kur'ani kada ku sake wanin ku ya gabace ku da yin aiki da shi, me yafi kayatarwa daga abin da sarkin muminai Ali (a.s) yake fadi cikin girmamar kur'ani mai girma:

واعلموا انّ هذا القرآن هو الناصح الذي لا يغش ، والهادي الذي لا يضلّ ، والمحدث الذي لا يكذب ، وما جالس هذا القرآن أحد إلّا قام عنه بزيادة أو نقصان : زيادة في هدى أو نقصان من عمى .

Ku sani lallai wannan kur'ani shi mai nasiha ne wanda baya yin algus, mai shiryarwar da baya batarwa, mai zantarwar da baya yin karya, babu wani mutum da ya zauna tare da wannan kur'ani face ya tashi da Karuwa ko tauyuwa: karuwa cikin shiriya da tauyuwa daga makanta.

واعلموا انّه ليس على أحد بعد القرآن من فاقةٍ ، ولا لأحد قبل القرآن من غنى ، فاستشفوه من أدوائكم ، واستعينوا به على لأوائكم ، فانّ فيه شفاء من أكبر الداء وهو الكفر والنفاق والغيّ والضلال ، فاسألوا الله به وتوجّهوا إليه بحبّه ، ولا تسألوا به خلقه . إنّه ما توجّه العباد إلى الله تعالى بمثله ، واعلموا انّه شافع مشفّع وقائل مصدّق ، وأنّه من شفع له القرآن يوم القيامة شُفع فيه ، ومن محل به القرآن يوم القيامة صُدِّق عليه ، فانه ينادي منادٍ يوم القيامة : ألا إنّ كلّ حارث مبتلىً في حرثه وعاقبة عمله غير حرَثة القرآن ، فكونوا من حرثته وأتباعه ، واستدلوه على ربّكم ، واستنصحوه على أنفسكم ، وأيهموا عليه آراءكم ، واستغشّوا فيه أهواءكم »[46] .

Ku sani lallai babu wani talauci ga wani mutum bayan kur'ani, hakama babu wata wadatuwa ga wani mutum gabanin kur'ani, saboda haka ku nemi warakar cututtukan ku daga gareshi, ku nemi taimakon sa kan wahalhalun ku, lallai cikin sa akwai waraka daga babbar cuta wand ashi ne kafirci da munafunci da zalunci da bata, ku roko Allah da shi ku neufe shi da soyayyar sa, kda ku roki halittun sa da shi, lallai bayi bas u fuskanci Allah da wani abu misalin sa ba, ku sani lallai shi mai ceto ne mai cetacce mai magana gasgatacce, lallai yanda al'amarin yake duk wanda kur'ani ya cece ranar kiyama za  ai ceto cikin sa, lallai ranar kiyama mai shela zai yi shela, lallai duk wani mai shuka an jarrabce shi cikin shukar sa da karshen lamarin sa face masu riko da kur'ani , ku kasance daga masu riko da shi mabiyan sa, kafa kafa hujja da shi kan ubangijin k, kuyi kanku nasiha da shi, ku tuhumi ra'ayoyin ku kansa, ku nemi lullube son zuciyar ku cikinsa.

Ba buya cewa hakika mutane sun fuskanto zuwa ga kurani mai girma, sai dai cewa kadai cikin lafuzzan sa da karanta shi da sautin sa, malamai sun fuskanto zuwa gareshi sai dai cewa cikin tafsirin sa da kira'ar s, amma aiki wanda shi ne ake bukata daga gareshi, kamar yanda kake gani a zahiri galibin musulmai da al'ummmin sun kauracewa wannan kur'ani ciikin aiki da shi, babu abin da suka rika daga kur'ani face ado a kan ma'ajiya, ko kuma daya daga cikin kayayyakin adon biki ko kuma tilawar sa a majalisosi zaman makoki da buda kanun labarai gidajen rediyo, ko kuma amfani da shi wajen danne mutane da hana musu yanci kamar yanda masu mulki suke yi domin hana mutane tofa albarkacin bakin su da kife tunanin su sakamakon tsoran kada suyi musu tawaye da kifar da hukumar su, ko kuma dai amfani da shi kan wasu bukatu na kankin kai.

Malam Rafi'I yana cewa: ( a tarihin ba san wani littafi da akai sharhin sa da tafsirai kan sa ba da wallafe-wallafe misalin kur'ani ba)

Hakika cikin babin mun kawo wata riwaya daga tarihi da cewa Abu Aliyu Aswari Alkali masanin balaga ya fassara kur'ani da sirori da tarihi da fuskokin tawili, sai ya fara daga tafsirin Bakara sannan ya kawo kissa talatin da shida sai ya zamanto ya mutu gabani hattamawa, ta yiwu yana fassara aya guda daya cikin satuttuka baa iya kammalawa, cikin wannan labari babu zuzutawa.

Hakika cikin ba'arin litattafan Tarjama mun samu Abubakar Al'adwafi wanda yayi wafati a 399 hijri ya wallafa littafi mai suna Al'istigna'u fi Tafsirul kur'an cikin mujalladi 120, hakika ya kasance dayantacce a zamanin sa cikin nau'o'i daban-daban na Kiraa da ilimin arabiyya da fannoni masu yawa daga ilimummuka.

Masanin falsafa malam Arastaranan ya kawo cewa ya tsinkati wani rubutu wanda yaku shiryarwa kan cewa ya samo asali ne daga daya daga cikin dakunan nazari Andulus wadanda suka kona kur'ani wannan tafsiri da yake cikin mujalladi 300.

Sha'arani cikin littafin sa Almatanu ya ce akwai wani tafsiri da yakai mujalladi 1000.

Wannan dukkanin sa fa cikin tafsiri kenan banda wallafe-wallafe da risaloli kan mas'alolion kur'ani daga nasiku da mansuk da asbabu nuzul da girubul kur'ani da dai sauransu, wadanda ba za a iya kidaice su.

Bama inkarin falalar hakan bari dai ma dole ne a himmatu da wannan bangare a kara zage dantse cikin sa fiye da na baya, sai dia cewa kamar yanda kur'ani mai girma ya kiraye zuwa ga aiki   

 (وَقُلِ اعْمَلُواْ فَسَيَرَى اللّهُ عَمَلَكُمْ وَرَسُولُهُ وَالْمُؤْمِنُونَ)[48] .

Kace kuyi aiki da sannu Allah da manzonsa da muminai za su ga ayyukan ku.

Ya zuwa daddadar rayuwa da ta ginu kan ingantaccen imani da aiki nagari 

 (مَنْ عَمِلَ صَالِحاً مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَى وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَنُحْيِيَنَّهُ حَيَاةً طَيِّبَةً)[49] .

Duk wanda yayi aiki nagari daga mazaje da mata alhalin yana mumini tabbas zamu raya shi daddadar rayuwa. 

Kan hasken abin da muka ambata muna son mu san mas'uliya da nauyyin da yake kan Annabawa da manzanni fuskanin al'ummomin su da mutanen su, sannan kiransu ya zuwa kyawawan halaye wadanda lafiyayyen tsarin halitta da mutumtaka da wahayi gasgatacce ya kasance tushen su, wadannan abubuwa uku suna daga hujjojin Allah ma'asumai da basu karbar kuskure kuma suna daga tabbatattun abubuwa da addinin Allah ya doru kansu.[5]

Kadai dai muna iya sanin haka daga littafin Allah gasgatacce wanda yake magana da gaskiya bayan mun nemi fahimta mun tambaye shi kyawawan halaye da munanan su, lallai kur'ani yana da luggar sa da sakafar sa ta kansa kebantacciya da ya ciro ta daga sama da tsarkakan hannaye[1] Bakara:187

[2] Bakara:1-2-3-4-5.

[3] Alu Imran:138

[4] Nuru: 34

[5] Abin da nay i imani da shi lallai cikin dukkanin ilimi da fanni akwai tabbatattu da kuma masu canjawa, na farko bayani ne kan mafahim na nazari kulliya mudlaka wadanda basa karbar takassusi kuma kuskure bai afkuwa cikin su, kamar misalin hukunce-hukuncen hankali kamar ijtima'ul nakidaini wanda yake korarre, lallai su ma'asumai ne a zatin su.