Aklak a luggance da isdilahi

 

Aklak a luggance jam’I ne daga kulku, an ciro shi daga kalku da wasalin fatahar lamun yana shiryar kan halitta ta zahiri da ta zama jiki da ake iya ganinta da idanu da hasken ido, sannan da wasalin rufu’a tana shiryarwa kan wata halitta ta badini da ake iya ganin ta da basira da hasken zuciya, sannan a isdilahance bayani kan wata dabi’a da ta zama jiki cikin nafsu da ayyuka suke gangarowa daga gareta daga mutum cikin sauki ba tare da kewaya tunani ba, , ko dai ta kasance daga sharri da munanan siffofi ko kuma daga alheri da halaye ababen yabawa da siffofi masu kyawu wadanda suke haddin tsakatsaki tsakanin wuje goda iri da takaitawa

(وَكَذلِکَ جَعَلْنَاكُمْ أُمَّةً وَسَطاً لِتَكُونُوا شُهَدَاءَ عَلَى آلنَّاسِ وَيَكُونَ آلرَّسُولُ عَلَيْكُمْ شَهِيداً)[1

Haka zalika muka sanya ku al’umma tsakatsaki domin ku kasance shaidu kan mutane shi kuma manzo ya zama shaida kanku.

Da Kuma zama mizani da ababen kwaikwayo da falala cikin samfuri cikin kyawawan halaye da sairi da suluki, sannan daga cikin ma’ana tsakatsaki akwai: tsanin faira daga na sama zuwa na kasa, sai ya kasance cikin kaddin amudi, kamar yanda na farko yake kan kaddin ufuki, bai buya cewa A’imma (a.s) sune matashin tsatsaki kamar yanda Imam Sadik (a.s) ya fadi

«نحن الشهداء على الناس بما عندهم من الحلال والحرام ، وبما ضيعوا منه »

Mune masu bada shaida kan mutane daga abin da ya kasance daga garesu daga halal da haramun, daga abin da suka tozartar daga gareshi.

Manzon Allah (s.a.w) sai ya kasance shi ne shaida kan su, su kuma suka kasance shaidu kan mutane, kamar yanda sarkin muminai Ali (a.s) ya fada, sannan kur’ani mai girma yana ishara zuwa ga nau’uka biyu daga Aklak: kyakkyawa da mummuna, sannan ya ambato jumla daga masadik din su.

 (وَنَفْسٍ وَمَا سَوَّاهَا * فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَاهَا)[3] .

 da nafsu da abin da ya daidaita ta* sai ya kimsa mata fajircinsa da shiriyarsa.

Ga wasu fihirisosi cikin kyawawan halaye da munanan su, idna kana bukatar kari to ka koma ga littafin (Tafsilul Ayat Kur’an Karim) Juli Labon ya sanya ta da harshen faransanci sannan Muhammad Fu’ad Abdul-Baki ya nakalto ta zuwa larabci, cikin ta akwai maudu’ai ayoyin kur’ani ta hanyar kawo lambar sura da lambar aya.

Abin ban takaici bare suna gabatar musulmai cikin neman sanin kur’ani da ilimummukan da ya kunsa?!