Halifan Allah a doran kasa

Bai buya cewa kasa Allah ya fifita tsakanin sauran duniyoyin taurari ya sanya masaukar waliyin sa halifar sa, hikimar sa da mashi'ar sa sun hukunta cewa ya cudanyu da adawar Iblis la'ananne wanda yayi girman kai yaki mika wuya da yin sujjada ga Adam wanda ubangijin sa ya sanar da shi ilimin komai, kamar yanda sauran Mala'iku suka yi sai ya kasance daga kafirai.

Sai mutane suka kasu cikin zabin su tun zamanin farko ya zuwa sinfi biyu: mumini kasashshe da yake tare da siffofin alheri da falaloli da kyawawan dabi'u, da kafiri mai kisa wand ayake tare da siffofin sharri da kaskanci da munanan dabi'u, abin da ya kasance ya kasance cikin kissar Habila da Kabila, al'umma suka kasu a wancan zamani zuwa rundunoni biyu: bayin Allah muminai da kuma dawagitai mabiyan Iblis, daga cikin mutane akwai wanda yayi imani da Allah ya kafircewa dagutu, sai Allah ya kasance majibancin lamarin sa, domin ya fitar da shi daga duhu zuwa haske, daga duhun jahilci zuwa hasken ilimi da hankali, hakama daga cikin su akwai wanda yake imani da dagutu ya kafircewa Allah ya riki shaidan waliyin sa, domin ya fitar da shi daga haske zuwa duhu, sannan duk abin da yake daga Allah shi ne wanzazze, kamar misalin Annabawa  da duk wanda ya bi sawun su, ya shiriya da shiriyar su, Kalmar su ta kasance wanzazziya kamar misalin Ibrahim Kalil

7 (وَجَعَلَهَا كَلِمَةً بَاقِيَةً فِي عَقِبِهِ )

Ya sanya ta kalma wanzazziya cikin zuriyar sa.

Amma dawagitai da wanda suka bi sawun su wadanda suka zalunci kawukan su, hakika Allah ya karar da su.

(فَجَعَلْنَاهُمْ أَحَادِيثَ وَمَزَّقْنَاهُمْ كُلَّ مُمَزَّقٍ )[2]

Sai muka sanya su labarai muka kekketa dukkkanin kekketawa.

Shi alheri da kyawawan dabi'u wanzazzu ne, shi ko sharri da kaskantattun halaye suna karewa ne, shi abin da yake wurin Allah shi ne mai wanzuwa da wanzuwar sa abadiya sarmadiya, ba komai ne kyawawan halaye ba face dai dabi'un Allah da madaukakan siffofin sa da kyawawan sunayen sa da girmamar su da kyawuntar su da kamalar s, tsarki ya tabbatar maka ya ma'abocin girmama da karamci, masu tajalli cikin kammalallen mutum, wanda Allah ya halifantar da shi a doran kasa, sai ya kasance hujjar sa kan halittun s, abin koyi da kwaikwayo ga wanin sa, hujja ba ta iyakantu ba cikin Annabawa da wasiyyai, bari dai ta hado da waliyai daga maza da mata, Maryan shugabar matan zamanin ta da Fatima shugabar matayen matan farko da na karshe duniya da lahira basu kasance wani abu ba face samfuri da misali nagari abin koyi da kwaikwayo ga dukkanin halittu, har ta kai ga Zahara ta kasance hujja daga hujjojin Allah kan halittun su, ababen masu jikkuna da marasa jikkuna sun cuka da hasken ta, sama da ksa ma sun cika da hasken ubangijinta wanda yayi tajalli cikin Zahara (a.s) tsarki ya tabbata a gareshi hasken sammai da kasa misalin haskenta kamar misalin tagar bango, ita Zahara tagar hasken Allah duniya da lahira.

Sannan su Annabwa da manzanni sun daidaita cikin asalin mukamin manzanci da falalar annabta, sai dai cewa Allah matsarkaki ya fifita sashin su kan sashe cikin ilimi da siffoi da sauke sako daurar sa iyakantacce ne ko kuma gamamme, kamar yanda Allah Azza wa Jalla ya fada: 

 (تِلْکَ آلرُّسُلُ فَضَّلْنَابَعْضَهُمْ عَلَى بَعْضٍ )[5]

Wadancan manzanni mun fifita ba'arin su kan ba'ari.

Sai Allah ya danganta fifitarwa zuwa kansa, haka zalika fadinsa madaukaki:

 (وَرَبُّکَ أَعْلَمُ بِمَن فِي آلسَّمواتِ وَآلاَْرْضِ وَلَقَدْ فَضَّلْنَا بَعْضَ آلنَّبِيِّينَ عَلَى بَعْضٍ )[6]

Kuma ubangijinka shi ne mafi sanin wadanda suke sammai da kasa hakika mun fifita ba'arin Annabawa kan ba'ari.

Kuma cikamakin Annabawa da manzanni masoyin Allah manzonsa Muhammad bn Abdullah shi ne mafi falalar su saki babu kaidi kamar yanda yake fadi:

«فضّلني على جميع النبيّين والمرسلين »

Allah ya fifita ni kan baki dayan Annabawa da manzanni.

Ya samu fifiko kan su da kasa'si masu tarin yawa, kamar misalin dawwamammiyar mu'ujizar sa wato kur'ani mai girma da gamammen sakon sag a dukkanin al'ummomi har zuwa tashin kiyama, da kasantuwar sa mai bada shaida kan al'umma (kuma manzo ya kasance shaida kanku) da kuma kammala addini da ika ni'ima, da kasantuwar sa farkon halittar Allah da ya tsago shi daga hasken sa Azza wa Jalla, Allah ya kasance haske da yayi tajalli cikin cikamakin Annabawa manzanni Muhammad sai ya kasance fitila mai haskakawa

(يَاأَيُّهَا آلنَّبِيُّ إِنَّا أَرْسَلْنَاکَ شَاهِداً وَمُبَشِّراً وَنَذِيراً * وَدَاعِياً إِلَى آللهَ بِإِذْنِهِ وَسِرَاجاً مُّنِيراً)[8]

Yakai wannan Annabi lallai mu mun aiko ka shaida kuma mai bushara da gargadi* mai kira zuwa ga Allah fitila mai haskaka.

Mafi tausasa daga abin da ke cikin kasantattu wanda da shi komai yake yayewa ya bayyana, sai manzo mafi girma ya kasance rahama ga talikai kuma illa ta gaya ga halitta, kuma lirrafin sa haske ne cikin sa akwai faiface bayanin komai, lallai haske yana bushara da sababbin sasannida tafiyar da duhu, lallai shi alami ne na wanzuwa, kamar yanda yake sababin bayyanar ta, sai a lura sosai, domin ka san kiyastawa tsakanin hasken Allah da fitila mai haskaka lallai shi yana karkashin hasken Allah (hakika haske daga Allah ya zo muku da kuma littafi mabayyani).