Hattamawa

Wannan Kenan daga fiye kyawawan halaye guda dari daga dabi’un Annabawa da sulukin su mai albarka karkashin hasken ayoyin kur’ani mai daraja, abin da muka ambata bai wuce cikin cokali ba daga tafki, kamar dai takun farko ne ga wanda ya nufi zurafafawa cikin wannan tafki mai zurfi, kamar yanda yake sinadari na farko ga muhadarorin muslunci ga malaman addini, ga bangaren masu wayar da kai da daliban jami’a, musammam ma ma’abota hawa mimbarori da masu karanta ta’aziya cikin tarukan zaman makoki da muhadarorin watan Ramadan lallai wannan dan karamin littafi zai amfanar, inama ace uba zai dinga karantawa dansa tare da yi masa sharhi asraran da suke boye cikin daga ilimi da janibin sakafa, da abin da ubangiji yayi masa ilhama daga ilimin sa ladunni wanda yake munajati da bayin sa da shi ya tattauna da zatin hankulan su da shi, bayan tsarkakar zukatan su daga datti da zunubai. Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai.

Gareshi muka dogara madalla da wakili.

Bawan Allah Assayid Adil-Alawi

Hauzatul ilmi Qum mukaddasa.

Mai fassara Umar Salihu.