Cikin inuwar tafsrin kur'ani da tawilin ayar haske

 

Hakika dauki babu dadi tsakanin gaskiya da karya haske da duhu tun lokacin da Allah ya halicci Adamu (as) zababbensa, sannan ya umaraci Mala'iku da su yimasa sujjada, sai iblsi yaki ya yi girman kai ya kasance daga kafirai, sai Allah ya saukar Adamu tare da iblis zuwa doran kasa don ya kasance makiyi ga mutum, lallai annabi Adamu (as) yana wakiltar Allah cikin sunayensa da siffofinsa.

Sannan fada tsakanin Adamu da iblis da mataimakansaya kaure, sannan Allah ya cika hujjarsa mai isarwa kan halittu baki daya da

Shirya gama gari da kebantaciya ta hanyar saukar da litattafai da aiko da manzanni, da tura da annabawa, sannan magadansu wadanda Allah ya umarcesu da kare sakon annabta saukakka daga wasiyyai da salihan malamai, ya kuma banbance gurbatacce daga kyakkyawa ya mayyaze mumini daga kafiri, ya bayyana gaskiya ya bayyanar da ita cikin dukkanin jama'a da kungiya. daga nan muke ganin Allah matsarkaki cikin suratul nuru cikin ayarsa daga fadinsa madaukaki:

 (اللهُ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأرْضِ ) إلى قوله : (وَاللهُ يَهْدِي مَنْ يَشَاءُ إلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ ) ،

(Allah ne hasken sammai da kasa)[1] zuwa fadinsa (Allah yana shiryar da wanda zuwa ga hanya mikakka).[2]

Yana hakaito mana kiyastawa tsakanin muminai da kafirai, da hakikar imani wanda shi ne hakikanin haske da kuma hakikanin kafirci wanda shi ne hakikanin duhu samansa duhu.

Muminai suna fifita da banbanta da shiriya da haske, da kuma cewa lallai sune masu shiryarwa ne ta hanyar ayyukansu nagari zuwa ga haske daga ubangijinsu, da yake fa'idantar da su yake kuma karama musu ma'arifa sanin Allah azza wa jalla, yana kuma shigar da su ya zuwa mafi kyawun sakamako da falala d akarama daga Allah matsarkaki a duniya da lahira. Lallai su yana raya su daddadar rayuwa yana kuma yi musu sakamako da mafi kyawun daga abina suka aikata, sai ya yaye rufi daga zuciyarsu da idanunsu, gabbansu na ciki da waje su haskaka da niyya ta gari gasgatatta da kuma ayyuka kyawawa da aiki nagari, amma kafirai ayyukansu basa shigar da su zuwa ga komai face kalaulauniya da bata da hakika, sannan su suna cikin duhu sahsensa saman sashe Allah bai sanya musu haske ba bai kuma sanya musu imami salihi ba saboda haka basu da haske.

Sannan Allah matsarkaki yana siffantuwa da tausayi da jin kai gama gari ga muminai da kafirai a duniya, sai dai cewa tausayi na jin kai ya kebanta ga muminai duniya da lahira, ya bayyana wannan hakika cikin suratul nur a cikin ayar haske da cewa lallai akwai gama garin haske akwai kuma kebantacce.

Gama garin haske na farko shi ne wanda sammai da kasa ke haskakauwa da shi sai su bayyana cikin samuwa da shi bayan da basu kasance bayyane ba.

Shi haske bayaninsa da hakikaninsa lallai shi ne wanda da kansa yake bayyana kansa kuma yana bayyanar da waninsa kamar misalin hasken da ake iya gani, sannan bayyanar da wani abu ga wani yana bukatar shi mai bayyanarwa ya zama shi bayyananne da a kankin kansa ba daga waninsa ba, shi bayyananne ga zatinsa shie mai bayyanarwa ga waninsa wanda shi ne haske, shi Allah matsarkaki madaukaki shi haske ne kamar yadda cikin kyawawan sunayensa haske ne-yana bayyanar da sammai da kasa da walkawarsa kansu, kamar yadda haskoki na zahiri suke bayyanar da abubuwa masu jiki ta hanyar walkawarsu kansu, sai dai cewa gundarin banbanci tsakanin hasken zahiri da hasken Allah matsarkaki shi ne cewa bayyanar abubuwa da hasken Allah ainahin samuwarsu ne, sannan bayyanar jikkuna da haske na zahiri ba asalin samuwarsu bane, sannan wannan haske gama gari  yana daga rahamar Allah ta tausayi, amma na biyu ma'ana haske kebantacce na daga rahamar Allah ta jin kai wacce mumianai ke haskaka da ita suke shiriya zuwa gare shi da ayyukansu nagargaru.

Amma ma'arifa wacce zuciyarsu da idanunsu zasu haskaka da ita ranar da zukata da idanu ke jujjuyawa, sai su shiriya da shi zuwa ga farin arzikinsu madawwami    

 (وَأمَّا الَّذِينَ سُعِدُوا فَفِي الجَنَّةِ خَالِدِينَ فِيهَا) ،

Amma wadanda suka azurtu zasu shiga aljanna suna dawwama cikin ta.[3]

Sai cikin sa su ga abin da ya faku daga gare su a duniya gani na kwaywar idaniya, cikin aljanna akwai abin da rai ke sha'awa yake dadinta a idanuwa akwai abin da bai taba darsu cikin zuciyar wani ba.

Sannan Allah madaukaki ya misalta wannan haske da fitila fitila cikin kwalaba cikin taga, sannan zai kunnu daga man zaitun cikin gayar tsarkaka da tsaftata sai kwalaba ta fara haske da kyalkyali kai kace tauraron mai tsananin haske. Sai ya ta karu haske kan haske, wannan fitila ce ta Allah da ya ajiyeta cikin gidajen ibada wadanda muminai ke tasbihi wadanda su kasuwanci da sayae da sayarwa basa shagaltar da su da barin ambaton Allah.

Wannan siffa ce ta hasken Allah wanda ya karrama muminai da ita ya kuma hatramtata kan kafirai, ya barsu cikin duhu basa gani, wannan ludufi ne daga duk wanda ya damfaru da shi ya bijirewa duniya kaskantatta to lallai shi Allah zai kebance shi da haskensa, Allah yana aikata abinda ya so, gare shi mulkin yake gare shi makoma, yana hukunci da abin da ya nufa, yana saukar da ruwan sama da sanyi daga girgije guda, yana jujjuya dare da raba, yana sanyawa daga dabbobi wasu masu tafiya jan ciki jan cikin su da kuma wanda yake tafiya kan kafafuwa biyu da kuma wanda ke tafiya kan guda hudu, hakika Allahya halicci komai daga ruwa da kudurarsa da iliminsa mai girma da buwaya-sannan tafsirinyana da ma'anar yaye rufi daga zahirin lafuzza da ma'anoni cikin kur'ani mai girma- shi kuma tawili shi ne yaye rufi daga badini, lallai kur'ani yana dauke da cikkuna, misalinin cikkuna bakwai, kowanne guda na dauke da saba'in, bari ma yana fiye da haka ga wanda iliminsa daga Allah matsarkaki yake, sannan annabi mai fadin wahayi da imami wasiyyi kan tawili, daga tawili da dabbakawa da bayanin masadik fahimtocin kur'ani ma girma, babu wanda ya san tawilinsa face Allah da masu zurfin ilimi wadand sune manzon Allah (s.a.w) da halifofinsa tsarkaka, da duk wanda ya bi sawunsu daga misalinsu zuwa misali daga wadanda suke tsona daga haskensu: wanda shi ne mabayyanar hasken Allah matsarkaki, da wannan ne ma zamu ga a'immarmu gasgatattu sun fassara mana haske da mafi cikar abin da yake gasgatuwa cikin sa kamar yadda wannan ma'anar zata bayyana nan gaba kadan cikin bahasi mai zuwa karkashin kawo wasu hadisai masu daraja cikin mukamin.


[1] Nuru:35

[2] Bakara:213

[3] Hudu:108