amma mufradat din tafsirin ayatun nur haske

 

nuru: wani haske da yadu wanda yake ayyanuwa cikin idanuwa, shi kuma nau'i biyu ne: hasken duniya da hasken lahira, sannan kuma kashi biyu ne: kashin da ake hankaltarsa da idan basira wanda shi ne wanda ya yadu daga al'amuran Allah kamar hasken hankali hasken kur'ani, sai kuma wanda ake riskarsa da ido na zahiri wanda shi ne wanda ya bazu ya yadu cikin abubuwa masu jiki masu haskakauwa kamar rana da wata da taurari.

Daga cikin hasken Allah fadinsa mai girma mabuwayi: 

: (قَدْ جَاءَكُمْ مِنَ اللهِ نُورٌ وَكِتَابٌ مُبِينٌ ) ، وقال : (وَجَعَلْنَا لَهُ نُورآ يَمْشِي بِهِ فِي النَّاسِ ) ،

Hakika daga Allah haske da littafi mabayyani ya zo muku)[1]  ya ce: muka sanya masa haske yana yawo da shi cikin mutane)[2])

 (وَلَكِنْ جَعَلْنَاهُ نُورآ نَهْدِي بِهِ مَنْ نَشَاءُ مِنْ عِبَادِنَا)

Sai dai cewa mun sanya shi haske muna shiryar da wadanda muka so da shi daga bayinmu.[3]

Har zuwa wajen ya ce: daga cikin hasken lahira fadinsa: 

 (نُورُهُمْ يَسْعَى بَـيْنَ أيْدِيهِمْ ) ، وقوله : (آنْظُرُونَا نَـقْتَبِسْ مِنْ

نُورِكُمْ ).

(Haskensu yana kaikawo gabansu)[4] da fadinsa (ku kallemu mu tsona daga haskenku)[5]

Sannan haske wajen masana falsafa: shi ne mabayyani cikin kankin kansa mai kuma bayyana waninsa.

Ya zo cikn littafin biharul anwar cikin babin lallai A'imma sun haskayen Allah sannan ayatun nur da tawili su ake nufi[6]

تفسير القمّي : عن أبي خالد الكابلي قال : سألت أبا جعفر  7 عن قوله

تعالى : (فَآمِنُوا بِاللهِ وَرَسُولِهِ وَالنُّورِ الَّذِي أنزَلْنَا) ، فقال : يا أبا خالد، النور

والله الأئمة من آل محمّد إلى يوم القيامة ، هم والله نور الله الذي أنزل ، وهم والله نور الله في السماوات والأرض ، والله يا أبا خالد لنور الإمام في قلوب المؤمنين أنور من الشمس المضيئة بالنهار، وهم والله ينوّرون قلوب المؤمنين ، ويحجب الله نورهم عمّن شاء فتظلم قلوبهم ، والله يا أبا خالد لا يحبّنا عبد ويتولّانا حتّى يطهّر الله قلبه ، ولا يطهّر الله قلب عبدٍ حتّى يسلم لنا ويكون سلمآ لنا، فإذا كان سلمآ لنا سلّمه الله من شديد الحساب ، وآمنه من فزع يوم القيامة الأكبر.

Ya zo cikin tafsirin kummi daga Abu Khalid kabili ya ce: na tambayi Abu Abdullah (as) dangane da fadin Allah (ku yi imani da Allah da manzonsa da hasken da muka saukar)[7] ya ce: ya Abu Khalid wallahi haske ne daga A'imma Alu Muhammad har zuwa ranar tashin kiyama, su hasken Allah ne wanda ya saukar., su wallahi hasken Allah a sammai da kasa , ya Abu Khalid wallahi tabbas hasken imami cikin zukatan muminai yafi haskaka daga hasken rana mai haskaka cikin yini, sune wallahi suke haskaka zukatan muminai, Allah na hijabance haskensu daga wanda ya so zukatansu su duhunta, wallahi ya Abu Khalid babu bawan da yake sonmu babu wanda yake jibantarmu har sai Allah ya tsarkake zuciyarsa, sannan babu wanda Allahb yake tsarkakewa zuciya sai bayan ya sallama mana ya kasance sallamawa garemu, idan ya kasance sallamawa garemu Allah zai tseratar da shi daga tsananin hisabi, ya kuma amintar da shi daga firgita mafi girma ranar kiyama.

Sannan kuma akwai riwayoyi da suke nuni da cewa su A'imma sun kasance haskaye da suke kewaye da al'arshin Allah cikin babin nassoshin da sukai magana kansu cikin bihar.[8]

 

babin fara halittar hasken manzon Allah (s.a.w) da A'imma (as)[9]

 da babin lallai su daga haske kwaya daya[10] suke, cikin haduwar hasken mnazon Allah (s.a.w) da sarkin muminai Ali (as)[11]

hadisin annabi madia daraja:  duk abin da ya kasance daga hasken Ali (as) ya gangara zuwa dansa Hassan (as), sannan dukkanin abin da ya kasance daga haskena ya gangara cikin husaini (as) haka wannan haske ke kewayawa cikin a'imma daga `ya`yansa har zuwa tashin kiyama[12]    

 

عن الكافي بسنده عن أبي عبد الله  7، قال : إنّ الله إذ لا كان فخلق الكان والمكان ، وخلق نور الأنوار الذي نوّرت منه الأنوار، وأجرى فيه من نوره الذي نوّرت منه الأنوار، وهو النور الذي خلق منه محمّدآ وعليّآ عليهما وآلهما السلام ، فلم يزالا نورين أوّلين ، أو لا شيء كون قبلهما فلم يزالا يجريان طاهرين مطهّرين في الأصلاب الطاهرة حتّى افترقا في أطهر طاهرين عبد الله وأبي طالب 8.

Daga littafin Kafi da isnadinsa daga Abu Abdullah (as) ya ce: lallai Allah lokacinda wata halitta ba ta kasantu ba sai ya halicci kasantuwa da wuri, ya halicci hasken haskaye wanda haskaye suka haskaka daga gare shi, sannan ya gudanar cikin sa daga haskensa wanda daga gare shi haskaye suka haskaku, shi ne hasken da daga gare shi ya halicci Muhammad da Ali amincin Allah ya kara tabbata gare su, basu gushe ba haskaye biyu na farko, ko kuma ace babu wani abu da ya kasantu gabaninsu basu gushe ba tsarkakku masu tsarkakewa suna gudana cikin tsatson tsarkaka har sai da suka rabu cikin mafi tsarkakar tsarkaka biyu Abdullahi da Abu dalib.

Ya zo cikn biharul anwar cikin babin lallai cewa ya sauka cikin sarkin muminai Ali (as) da cewa shi ne Ambato kuma shi ne haske da shiriya a cikin kur'ani   

عن رسول الله  9: يا نور النور، يا منوّر النور، يا خالق النور، يا مدبّر النور، يا مقدّر النور، يا نور كلّ نور، يا نورآ قبل كلّ نور، يا نورآ بعد كلّ نور، يا نورآ فوق كلّ نور، يا نورآ ليس كمثله نور.

Daga manzon Allah (s.a.w) ya hasken haske ya mai haskaka haske, ya mahaliccin haske, mai tafiyar da haske, ya mai kaddara haske, ya hasken dukkanin haske, ya haske gabanin haske, ya haske gabanin haske, ya haske bayan haske, ya haske saman dukkanin wani haske, ya haske da babu wani haske kwatankacinsa.[13]

قال رسول الله  9: إنّ هذا القرآن حبل الله والنور المبين .

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: lallai wannan kur'ani taguwar Allah ce kuma haske mabayyani.

قال الإمام الحسن  7: إنّ هذا القرآن فيه مصابيح النور.

Imam Hassan (as) ya ce: lallai wannan kur'ani cikin sa akwai fitilaaun haske.

قال أمير المؤمنين عليّ  7: تعلّموا القرآن فإنّه أحسن الحديث ، وتفقّهوا فيه ، فإنّه ربيع القلوب ، واستشفوا بنوره فإنّه شفاء الصدور.

Sarkin muminai Ali (as) ya ce: ku koyi kur'ani lallai shi ne mafi kyawun zance, ku nemi fahimta cikin sa, lallai shi dausayin zukata ne, ke nemi waraka da haskensa lallai shi warakar kiraza ne.

 

وقال  7 في وصف النبيّ  9: حتّى أفضت كرامة الله سبحانه وتعالى إلى محمّد  9... فهو إمام من اتّقى ، وبصيرة من اهتدى ، سراج لمع ضوؤه ، وشهاب سطع نوره ، وبرق لمعه .

Cikin siffanta annabi (s.a.w) sai (as) ya ce: har karamar Allah matsarkaki madaukaki ta kwarara zuwa ga Muhammad (s.a.w) shi imamin wanda yaji tsoran Allah ne, shi ne basirar wanda ya shiriya, shi ne fitilar da haskensa ya walka, tauraro ne da haskensa ya huda, kyallawarsa ta walka.

وعنه  7: إنّما مثلي بينكم كمثل السراج في الظلمة ، يستضيء به من ولجها.

Daga gare shi (as) kadai dai misalina tsakaninku kamar misalin fitila ce cikin a cikin duhu, duk wanda ya shigo cikin wannan fitila zai haskaka.

قال الصادق  7: ليس العلم بالتعلّم ، إنّما هو نور يقع في قلب من يريد الله تبارک وتعالى أن يهديه

Imam Sadik (as) ya ce: ilimi bai cikin koy, kadai shi wani haskene da yake fadawa cikin zuciyar wanda Allah madaukaki matsarkaki ya so shiryarwa.

وعن رسول الله  9 ـفي الدعاءـ: اللهمّ اجعل لي في قلبي نورآ، وفي لساني نورآ، وفي بصري نورآ، وفي سمعي نورآ، وعن يميني نورآ، وعن يساري نورآ، ومن فوقي نورآ، ومن تحتي نورآ، ومن أمامي نورآ، ومن خلفي نورآ، واجعل لي في نفسي نورآ، وأعظم لي نورآ.

Daga manzon Allah (s.a.w) cikin addu'a:- ya Allah ka sanya mini zuciyata haske, harshe na haske, idona haske, jina haske, ka sanya haske daga damana, ka sanya haske daga haguna, ka sanya shi daga bayana, ka snaya shi daga gabana, ka sanya haske cikin raina, ka girmama mini haske.

عن الإمام زين العابدين : وهب لي نورآ أمشي به في الناس ، وأهتدي به في الظلمات ، وأستضيء به من الشکّ والشبهات.

Daga imam zainul Abidin (as): ka bani haske da zanyi yawo cikin mutane da shi, in shiriya da shi cikin duhuna, in haskaku da shi daga shakka da shubuhohi.

قال الإمام الصادق  7: طلبت نور القلب فوجدته في التفكّر والبكاء، وطلبت الجواز على الصراط فوجدته في الصدقة ، وطلبت نور الوجه فوجدته في صلاة الليل.

Daga imam sadik (as) ya ce: na nemi hasken zuciya sai na sameshi cikin tunani da kuka, na nemi izinin ketare siradi sai na same shi cikin yin sadaka, na nemi hasken fuska sai na same shi cikin sallar dare.

وعن الإمام زين العابدين  7 ـلمّا سئل عن علّة كون المتهجّدين بالليل من أحسن الناس وجهآـ؟ قال : لأنّهم خلوا بالله فكساهم الله من نوره .

Daga imam zainul Abidin (as) lokaci da aka tambaye shi dalilin kasantuwar masu zage dantse da ijtihadi cikin dare sune suka fi kowa kyawun fuska? Sai ya ce: saboda sun kebanta da Allah sunyi halwa da shi sai ya lullufe su da haskensa.

وعن أمير المؤمنين عليّ  7 قال : ما تركت صلاة الليل منذ سمعت قول النبيّ  9: صلاة الليل نور. فقال ابن الكوّاء: ولا ليلة الهرير؟ قال  : ولا ليلة الهرير.

An karbo daga sarkin muminai Ali (as) ya ce: ban taba barin sallar dare bat un da na ji fadin manzon Allah (s.a.w) cewa: ita sallar dare haske ce, sai ibn kawwa'u ya ce: har daren hariru baka bari ba? Ya ce har daren hariru.

قال أمير المؤمنين  7: إنّ على كلّ حقّ حقيقة ، وعلى كلّ صواب نورآ.

Sarkin muminai Ali (as) ya ce: lallai kan dukkanin wata gaskiya akwai hakika, hakama kan dukkanin wani haske akwai damdagatar.

وقال رسول الله  9: الصلاة نور.

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: sallar haske ce.

وعنه  9: إذا رميت الجمار كان لک نورآ يوم الق

Idan ka yi jifan shaidan zai kasance maka haske ranar kiyama.

وعنه  9: عليک بتلاوة القرآن فإنّه نور لک في الأرض ، وذخر لک في السماء.

Daga gare shi amincin Allah ya tabbata gare shi: na umarceka da karatun kur'ani lallai shi haske ne cikin kasa gareka, taskace gareka a sama.

وقال  9: من قرأ هذه الآية عند منامه (قُلْ إنَّمَا أنَا بَشَرٌ مِثْلُكُمْ يُوحَى إلَيَّ أنَّمَا إلَهُكُمْ إلَهٌ وَاحِدٌ) ، إلى آخرها، سطع له نور إلى المسجد الحرام ، حشو

ذلک النور ملائكة يستغفرون له حتّى يصبح

Amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: duk wanda ya karanta wannan aya lokacin da zai kwanta (kace kadai dai ni mutum irinku ana yi mini wahayi kadai abin bautarku abin bauta ne guda daya)[14] zuwa karshenta, haske zai hudo masa zuwa masallaicin harama cike da wannan haske Mala'iku ne suke nema masa gafara har sai ya wayi gari.[15]

Kadai dai na kawo jumlar daga wadannan riwayoyin da suke magana kan haske domin mu tsinka yi ma'anar haske a tafsirinsa  da tawilinsa cikin kur'ani mai girma da hadisi masu daraja ko da dai atakaice ne, da kuma bayani wasu misadik dinsa kamar annabi (s.a.w) da A'imma tsarkaka, da kur'ani da ilimi da sallar dare da dai abin da ya yi kama da haka, wannan na nufin lallai haske mafhumin kulli tashkiki ne kamar yadda yake a ilimin mandik yana kuma martabobi mikakku cikin mikarsa da kuma masu bijirowa. Tsololuwar kimarsa shi ne annabi mafi girma (s.a.w) wanda hasken Allah matsarkaki yake tajalli cikin sa, sannan misalsalansa.

Allah madaukakin sarki cikin kur'ani yana cewa:     

: (يَوْمَ تَرَى المُؤْمِنِينَ وَالمُؤْمِنَاتِ يَسْعَى نُورُهُمْ بَـيْنَ أيْدِيهِمْ وَبِأيْمَانِهِمْ بُشْرَاكُمُ اليَوْمَ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ذَلِکَ هُوَ الفَوْزُ العَظِيمُ * يَوْمَ يَـقُولُ المُـنَافِقُونَ وَالمُـنَافِقَاتُ لِلَّذِينَ آمَنُوا آنْظُرُونَا نَـقْتَبِسْ مِنْ نُورِكُمْ قِيلَ آرْجِعُوا وَرَاءَكُمْ فَالتَمِسُوا نُورآ فَضُرِبَ بَـيْنَهُمْ بِسُورٍ لَهُ بَابٌ

بَاطِنُهُ فِيهِ الرَّحْمَةُ وَظَاهِرُهُ مِنْ قِبَلِهِ العَذَابُ )  .

Ranar da zaka ga muminai maza da muminai mata haskensu na tafiya gabansu da damansu bushararku yau aljannoni da koramu ke gudana daga karskashinsu suna masu dawwama cikin ta wadancananka shi ne rabauta mai girma* ranar da munafukai maza da munafukai mata zasu cewa wadanda sukai imani ku kallemu mu tsona daga haskenku sai ace ku koma bayanku ku nemi wani hasken sai a buga wani bango tsakaninsu da yake da kofa wacce cikin sa rahama bayansa daga wajensa azaba[16] 

عن رسول الله  9: ثمّ يقول ـيعني الربّ تبارک وتعالى ـ: ارفعوا رؤوسكم ، فيرفعون رؤوسهم ، فيعطيهم نورهم على قدر أعمالهم ، فمنهم من يُعطى نوره مثل الجبل العظيم يسعى بين يديه ، ومنهم من يعطى نوره أصغر من ذلک ، ومنهم من يعطى مثل النخلة بيده ، ومنهم من يعطى أصغر من ذلک ، حتّى يكون آخرهم رجلا يُعطى نوره على إبهام قدميه يضيء مرّة ويطفأ مرّة[17]

Daga manzon Allah (s.a.w): sannan ubangiji matsarkaki madaukai ya ce: :- ku daga kawukanku, sai su daga kawukansu sai ya basu haskensu gwargwadon ayyukansu, daga cikin su akwai wanda ake bashi haskensa misalin dutse mai girma ya dinga tafiya gabansa, daga cikin su kuma akwai ake bashi kasa da haka, akwai wanda ake bashi misalin girman dabino a hannunsa, daga cikin su akwai wanda ake baiwa kada da haka, har na kashe ya kasance mutumin da ake bashi haskensa a kan dan yatsan kafarsa wani lokacin ya haskaka wani lokacin kuma hasken ya mutu.

وفي قوله تعالى : (أوَ مَنْ كَانَ مَيْتآ فَأحْيَيْنَاهُ ) قال : جاهلا عن الحقّ والولاية فهديناه إليها (وَجَعَلْنَا لَهُ نُورآ يَمْشِي بِهِ فِي النَّاسِ ) قال : النور الولاية (كَمَنْ مَثَلُهُ فِي الظُّلُمَاتِ لَيْسَ بِخَارِجٍ مِنْهَا) يعني في ولاية غير الأئمة  : (كَذَلِکَ زُيِّنَ لِلْكَافِرِينَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ.

 

cikin fadinsa madaukaki: (shin wanda ya kasance matacce sai muka raya shi) ya ce: ma'ana wana ya kasance jahili daga sanin gaskiya da wilaya sai muka shiryar da shi zuwa geresu (muka sanya masa haske yana yawo da shi cikin mutane)[18]

Sannan cikin wilayar wadanda ba A'imma ba (haka na muka kawantawa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa)

 

Wannan takaitowa ne kuma bayani ne dunkule daga abin da muka nufi yin bayaninsa cikin kalmar haske amma ragowar kalmomin kamar (mishkatu): bisa abin da babban malami lugga ragibul isfahani ya kawo da waninsa wato ita kalmar mishkatu wani dan rami da yake jcikin bango daki ba da ake amfani da shi wajen ajiye kayayyaki kamarb fitila da makamantanta.

Wasu kuma sun ce mishkatu wani yar karamar huda ce da take cikin fitila da fitilar aci balbal.

Ita kuma Kalmar misbahu: wata fitila ce da take korar duhu da haskenta sai ake ajiye mahallin misbahu, ba misalin fitila kwai bace, sai ta kara haske da haskaka da walkawa kanta.

Ita kuma zujajatu: wani gilashi ne tangararn da ake ganin abubuwa daga bayansa yana kuma fitar da haske iadan ya karba.

Ita kuma Kalmar durriyu: yana daga tauraro mai girma mai yawan haske, shi an tanade shi cikin sammai, wasu mutane sun ce: shi daya daga cikin taurari biyar masu haskaka ne: sune: zuhal mushtari, marriku, zuhratu, adarid. An ce an danganta shi ya zuwa durriyu sakamakon tacewarsa da kyawunsa.

Amma zaitu: wani mai ne da aka ciro daga zaitun.

Sai ta bayyana lallai haske shi mai bayyana a kankin kansa mai bayyana waninsa, da farko ana amfani da shi a hasken zahiri wanda ake gani, sannan kuma ya tattaro dukkanin abin da da wani abu key aye da bayyana da shi, saiake amfani da shi a kan mariskai biyar kan cewa su haske ne, da haske mariskaike bayyana kamar ji gani sansana dandana tabawa ta fuskanin majazi da isti'ara ko kuma ta fuskanin hakika ta biyu, dukkanin wannan da bayanin ma'anar haske mai gani zuwa ga zahirin zatinsa da zatinsa kuma mai bayyanar da waninsa.

Fadin Allah madaukaki      

 (اللهُ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأرْضِ )،

Allah hasken samma da kasa.

Yayin da abubuwa suka kasance masu yiwuwar samuwa kdai dai su samammu ne da zatinsa Allah madaukaki shi ne dalilin dalilai sababin sabubba sai shi ya kasance misdaki mafi cika ga haske, shi ne hasken dukkanin haskaye, akwai wata samuwar haske da abubuwa ke siffantuwa da su shi ne samuwarsu da haskensu na aro majazi isti'ara da aka karbo shi daga wurin Allah madaukaki, ita samuwa da haske wadanda suka tsayu da zatinsa yana samarwa kuma abubuwa suna haskaka da shi.

Allama dabadaba'i cikin tafsirinsa (Almizan) mai kima yana cewa: shi Allah matsarkaki haske ne yana bayyana bayyanar da sammai da kasa da shi, wannan shi ne abin da ake nufi da fadinsa

 (اللهُ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأرْضِ )

Allah hasken sammai da kasa.[19]

ta yanda aka jingina haske zuwa samma da kasa, sannan aka dora shi kan sunan girma (Allahu) kan wannan ne ya kamata ya dora fadin wanda ya ce: lallai ma'anar (Allah ne hasken sammai da kasa) jigon hadafin daga gare shi ne lallai abin da ake nufi da haske ba hasken aro bane majazi na iti'ara da ya tsayu da ita, wanda shi ne samuwa wanda ake dora shi kanta Allah ya tsarkaka daga haka ya daukaka.

Wasu kuma sun ce: ma'anar hasken sammai da kasa lallai Allah mai shiryar da mutanen sammai ne da kasa. Daga wannan ne ake fa'idantuwa cewa lallai madaukaki ba jahilce yake ga wani abu daga abubuwa. Yayin da bayyanar kowanne abu ga kansa ko ga waninsa kadai dai daga bayyanarwarsa madaukaki take mabayyani ga kansa d zatinsa, zuwa wannan hakikar ne fadin Allah madaukaki ke nuni bayan ayoyi biyu   

 (ألَمْ تَرَ أنَّ اللهَ يُسَبِّحُ لَهُ مَنْ فِي السَّمَوَاتِ وَالأرْضِ وَالطَّيْرُ صَافَّاتٍ كُلٌّ قَدْ عَلِمَ صَلاتَهُ وَتَسْبِيحَهُ ) ،

Ashe baka ga lallai Allah yana tasbihi gare shi dukkanin wanda yake sammai da dukkanin wanda yake kasa da tsuntsaye suna sahu-sahu kowanne hakika ya san sallarsa da tasbihinsa.[20]

 

Yayin da babu ma'ana ga tasbihi da saninsa da salla tare da jahiltar wanda akewa tasbihin da sallar, wannan ya yi kama da fadinsa madaukaki:  

 (وَإنْ مِنْ شَيْءٍ إلاَّ يُسَبِّحُ بِحَمْدِهِ وَلَكِنْ لا تَفْقَهُونَ تَسْبِيحَهُمْ ).

Babu wani abu face yana tasbihi gare shi da godiyarsa sai dai cewa baku fahimtar tasbihinsu.[21]

Hakika natija da sakamako sun samu kan cewa abin da akenufi da haske cikin fadinsa madaukaki:

 (اللهُ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأرْضِ )

Allah hasken sammai da kasa.[22]

Haskensa madaukaki ta yanda haske game gari yake hudowa daga gare shi dukkanin wani abu yana haskakauwa da shi, shi yana daidai ga samuwar kowanne abu sannan bayyanarsa cikin kankin kansa da waninsa rahama ce ta Allah gamammiya.

Misalin wadannan ma'anoni na falsafa dandakakku yana da wahalar samun iya fahimtarsu kan misalin wadancan larabawan kauye.

Lallai su jiya a zamanin da ya wuce sun kasance suna bautar gumaka wadanda su suka sassaka su da kansu da hannuwansu daga dabino ta yanda da zasu yunwatu sai su cinye ubangijinsu, kuma sun kasance suna binne `ya`yansu mata da ransu suna kuma tilastasu karuwanci, yau kuma fadin Allah madaukaki yana kwankwasar kunnuwansu:


 (اللهُ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأرْضِ ).

Allah hasken sammai da kasa.[23]

Saboda tausayi da jin kai da shiriya ga mutane Allah yake buga misali gare su don ya zamu kowa da kowa ya amfanu da shi kuma hujja Allah ta cika.

Sai Allah yake buga misali ga haskensa, abin da ake nufi daga wannan haske na biyu haske kebantacce kamar yadda yake a zahiri, lallai jingina Kalmar nuru (haske) zuwa lamiri da yake dawowa ga Allah madaukaki dalili ne kan cewa maksudi ba shi ne siffanta haske ba wanda yake daga hasken Allah, bari da shi haske ne da aka aro wanda Allah yake kwararar da shi domin ya misalta haskensa, ba haske ne gama gari ba wanda aka aro majazi wanda kowanne abu ke samun bayyanuwada shi wanda shi ne samuwa wacce abubuwa ke neman faira daga gare shi tana kuma siffantuwa da shi, dalili kanhaka shi ne fadin Allah bayan cika misali:

(يَهْدِي اللهُ لِنُورِهِ مَنْ يَشَاءُ) .

Allah yana shiryar da wanda ya so zuwa haskensa.[24]

Da ace muradi maksudi shi ne haske gama gari lallai da bazai kebanci wani abu da shi ba koma bayan wani kamar yadda muka ambata a baya, bari maksudi shi ne haske kebantacce ga muminai da hakikar imani da shiriya da imamanci da ma'arifa bisa dogaro da abin da ke bayyana daga kalamin daga ayoyi masu yawa, lallai yadda al'amarin yake shi ne Allah madaukaki ya danganta haske zuwa ga zatinsa kamar yadda ya zo cikin fadinsa: 

(يُرِيدُونَ لِـيُـطْفِئُوا نُورَ اللهِ بِأفْوَاهِهِمْ وَاللهُ مُـتِمُّ نُورِهِ ) ،

Suna nufin bushe hasken Allah da bakunansu Allah mai cika haskensa ne.[25]

Da kuma cikin fadinsa:

 (أوَ مَنْ كَانَ مَيْتآ فَأحْيَيْنَاهُ وَجَعَلْنَا لَهُ نُورآ يَمْشِي بِهِ فِي النَّاسِ كَمَنْ مَثَلُهُ فِي الظُّلُمَاتِ لَيْسَ بِخَارِجٍ مِنْهَا) ، وقوله : (يُؤْتِكُمْ كِفْلَيْنِ مِنْ رَحْمَـتِهِ وَيَجْعَلْ لَكُمْ نُورآ تَمْشُونَ بِهِ ) 

Shin wanda ya kasance matacce sai muka raya shi muka sanya masa haske yana yawo da shi cikin mutane zasu zama daya da wanda misalinsa cikin duhuna shi bamai fita bane daga gare su.[26]

Da fadinsa:

Zai zo muku da rabo biyu daga rahamarsa ya kuma sanya muku wani haske da za ku yi yawo da shi.[27]

 

Da fadinsa:

(أفَمَنْ شَرَحَ اللهُ صَدْرَهُ لِلإسْلامِ فَهُوَ عَلَى نُورٍ مِنْ رَبِّهِ )

Shin wanda Allah ya buda kirjinsa zuwa ga muslunci shi yana kan kan haske daga ubangijinsa.[28]

Wannan shi ne haske wanda Allah ya sanya shi ga bayinsa muminai sun haskakauwa da shi cikin hanyarsu zuwa ga ubangijinsu kuma shi ne hasken imani da ma'arifa da aka shawota daga sako da imamanci.

Sannan Allama daba'daba'i yana cewa: maksudi ba haske na zahiri ba cikin wannan aya kamar yadda wasu suka tafi kai, lallai ayar tana siffantuwa da halin gama garin mumainai gabanin saukar kur'ani da bayansa, kan cewa wannan wata sifface fgare su da suke siffantuwa da ita kamar yadda fadin Allah yake ishara zuwa ga hakan:    

 (لَهُمْ أجْرُهُمْ وَنُورُهُمْ )[29] ، وقوله : (يَـقُولُونَ ربَّـنَا أتْمِمْ لَـنَا نُورَنَا)[30] ،

Ladansu na gare su da haskensu.

A wata ayar kuma ya ce:

Suna cewa ya ubangijinmu ka cika mana haskenmu.

 

Kur'ani bai kasance siffa gare su, na'am idan anyi la'akari da abin da yake yayewa daga gereshi daga ma'arifa to zai koma azuwa ga abin da muka fada.

Sannan cikin kowanne tashbihi dole ne a samar da rukunar tashbihi: mushabbahu, mushabbahun bihi wajahul shabahu, saboda haka mushabbahun bihi ba mishkatu bane kadai bari dai baki dayan abin da aka ambata cikin ayar mushabbahu bihi ne daga fadinsa madaukaki:

 (كَمِشْكَاةٍ فِيهَا مِصْبَاحٌ المِصْبَاحُ فِي زُجَاجَةٍ )،

Kamar tag ace cikin ta akwai wata fitila fitilar cikin gilas.

Wannan yana da yawa cikin misalsalan kur'ani mai girma

Sannan tashbihin:

 

(الزُّجَاجَةُ كَأنَّهَا كَوْكَبٌ دُرِّيٌّ)

kwalaba kai kace ita tauraron ne mai tsananin haske.[31]

Ta fuskanin karuwar walkawar hasken fitila kishantuwarsa cikin tarkibin kwalaba kan fitila sai ta kara masa kyalkyala da wancan a cikin kwanciyar hankali ba tare da rarraurawa ba da filfilawar guguwar iska, saikwalaba ta kasance mai kare haske mai hana iska cutar da shi ita ta zama kamar misalin tauraro mai tsananin haske cikin kyalkyalinta da walkawar haskenta.

 

Tabbatar walkawar haskenta:

Fadinsa madaukaki:

 (يُوقَدُ مِنْ شَجَرَةٍ مُبَارَكَةٍ زَيْتُونَةٍ لا شَرْقِيَّةٍ وَلا غَرْبِيَّةٍ يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ وَلَوْ لَمْ تَمْسَسْهُ نَارٌ)

Ana kunna shi daga bishiya mai albarka zaituna ba ta gabas ba ta yamma ba manta ya kusa haskawa koma wuta bata shafe shi ba.[32]

 

Labari bayan labari ga fitila,ai fitila da take kunnuwa haskenta ya samu daga bishiya mai albarka ta zaitun, ma'ana yana kunnuwa daga mai da aka ciro shi daga zaitun, sannan abin da ake nufi da kasantuwar bishiya ba bagabashiya ba bayammaciya ba, ai ita ba bishiya ce da ta tsiro kamar sauran bisihiyoyi da suke tsirowa.

Babu ita a bangaren gabas babu ita bangaren yamma da har rana zata fada kanta daga dayan daga cikin geffan rana inuwa ta lullubeta cikin daya gefan bata nunar da kayan marmarinta `ya`yanta, manta da aka ciro daga gare ta bai tacewa bata bata kyawwunta haskaka, bari dai ita tana karbar rabonta daga rana tsawon yini sai manta ya kyawunta sakamkon kammaluwar nunar `yay`yanta, sannan abin da ke ishara zuwa ga wadannan ma'anoni fadinsa madaukaki:   

 (يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ وَلَوْ لَمْ تَمْسَسْهُ نَارٌ)

Manta ya kusa haskaka koma da wuta bata shafe shi ba.[33]

Abin da ake nufi da shi a nan shien tacewar mai da kammaluwar tanadinsa don kunnuwa lallai haka ya samo reshe ne daga siffofi biyu: ba bagabashiya ba, ba kuma bayammciya ba.

 

Ance 

 (يُوقَدُ مِنْ شَجَرَةٍ مُبَارَكَةٍ زَيْتُونَةٍ )

Ana kunna shi daga bishiya mai albarka zaituna.[34]

Ma'ana man bishiya mai albarka wacce ita ce bishiyar zaitun ta sham, saboda sham Allah ya albarkaci garin ma'anarsa alheri tabbatacce.

Wasu kuma sun ce an siffantata ne saboda zaitun yana fitar da ganye tun daga farkonsa har zuwa karshensa.

Sannan fadinsa: 

 (لا شَرْقِيَّةٍ وَلا غَرْبِيَّةٍ )

Ita ba bagabashiya bace ba kuma bayammaciya bace.[35]

Ance ma'anarsa ita ba bagabashiya bace da haskawar rana kanta kadai, ba kuma bayammaciya bace da faduwar rana kanta kadai.

Wannan shi ne mafi kyawun adonta, an kuma ce: ma'anarsa shi ne lallai ita tana tsakiyar kogi.

Wasu kuma sun ce wani bigire ne na rana.

Wasu kuma ita ba bishiyar duniya bace.

(يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ وَلَوْ لَمْ تَمْسَسْهُ نَارٌ)

Manta ya kusa haskaka kuma wuta bata shafe shi ba.[36]

 

Ma'ana daga tacewarsa da kyawuntarsa ya kusa ya haska ba tare da wuta ta shafe shi ba ta ruru cikin sa.

Sannan fadinsa (haske kan haske) khabar na mubtada'au da akai hazafi shi lamiri ne da yake komawa zuwa ga hasken kwalaba mafhumi cikin siyakin, sannan ma'anar hasken kwalaba da aka mabata shi ne haske mai girma kan haske haka ma cikin kammaluwar haskaka da kyallawa, wasu kuma sun ce : abin da ake  nufi daga kasantuwar haske kan haske shi ne nininkuwar haske ba yawaituwarsa ba, ba a nufin ayyanannen haske ko wand aba ayyananne ba kan wani haske misalinsa daban, ba kuma ana nufin cewa wani adadin haske ne guda biyu kawai, bari dai lallai shi wani haske ne mai ninninkuwa ba tare da iyakance ninkuwarsa ba, wannan jumla ya yadu cikin maganarmu kamar yadda yake cikin fadinsa madaukaki:  

 (فَارْجِعِ البَصَرَ هَلْ تَرَى مِنْ فُطُورٍ).

Ka mayarda gani shin ka gani daga tsagewa.[37]

Wannan ma'ana bata wofinta ba daga kyawunta, duk da cewa nufar adadantuwa shima baya nesa daga ludufin dandakewa, lallai ga haske mai haskawa daga fitila akwai dangantaka zuwa fitila a asali da hakika.

Dama danganta shi zuwa ga kwalaba ma wacce take kan fitila wannan danganawa ce ta aro da majazi, sai ace hasken kwalaba  wannan yana daga isti'imali majazi ba hakiki ba, sannan hasken yana sassauyawa da sauyawa dangantawar biyu yana kuma yawaita da adadantuwa da adadinsu da yawansu biyun, duk da cewa bisa hakika bai kasance ba face ga fitila, ga kwalaba bisa kallon karuwa dangantawar haske ba hasken fitila wanda shi yana tsayuwa da fitila yana kuma karba daga gare ta.

Wannan ma'ana tayi kyau da tausasa da dadada bisa la'akari da kyawu mai gudana da zatinsa cikin wanda aka misalta shi da shi aka kamanta shi da shi.

Lallai yadda al'amarin yake kamar yadda muka ambata lallai cewa daga cikin abubuwan da suke gasgata haske shi ne hasken imani da ma'arifa, kamar yadda yake lallai daga cikin mafi cikar masadik fitila kamar yadda nan gaba zamu kawo shi ne manzon Allah (s.a.w) mafi girman manzanni, sannan lallai gilashi kwalaba shi ne sarkin muminai Ali (as) yadda ya zo cikin ba'arin madaukakan hadisai, hasken sarkin muminai yana daga hasken manzon Allah (s.a.w) sannan kuma hasken manzon Allah (s.a.w) daga hasken Allah matsarkaki madaukaki yake, ya halicce haske daga haske.

Hasken imani da ma'arifa haske ne na aro majazi mai haskaka da walkawa kan zukatan muminai wand aka tsono daga hasken Allah madaukaki da yake tsaye da shi yake karbo madadi daga gere shi matsarkaki.

Natija ta samu cewa lallai mai misalta shi shi ne hasken Allah da yake haskaka kan zukatan muminai, sannan misali wanda shi ne wanda aka kamantu da shi (mushabbahun bihi) shi ne haske mai haskaka daga gialshi kan fitila, wanda aka kunna daga zaitun tatacce mai kyawu kuma shi ne maudu'in mishkatu (taga) tsagar jcikin bangon gida wanda bai rarraurawa da tasowar iska da guguwa, sannan hasken fitila mai haskaka daga kwalaba da mishkatu  da take tattarashi ta baza shi kan wadanda suke haskaka da shi, yana walkawa da haskakawa kansu cikin kurewar haskaka da kyawu.

Sai aka riki misali da mishkatu don shiryarwa zuwa ga cudanyar haske cikin tsagar tsagar bango da bazuwar haske cikin gidan, da la'akari da kasantuwar mai daga bishiyar zaitun wacce babu ita yamma babu ita gabas don nuni zuwa ga tacewar man da kyawunsa da yake tasiri cikin tacewar haske mai walkawa da haskawa daga ruruwarsa da kyawuntar haskakarsa, bisa abin dake nuni zuwa gakasantuwar mansa ya kusa haskawa ko da kuwa wuta ba ta shafe shi ba-ai kai kace shi daga kammaluwarsa yana bayyana kamalarsa, hatta ko da bai kasance yana da tasiri a waje ba-bisa la'akari da kasantuwar haske kan haske don shiryarwa zuw aga ninninkuwar hasken, ai kasantuwar kwalaba tana samun madadi daga hasken fitila cikin haskawarta.

Bai buya ba cewa wadannan ilimummuka da samuwar kamanceceniya suna da tasiri cikin bayanin masadik abubuwan da suka gasgatu da su da yanayiyyikansu da hakikaninsu, kadai mai kaifin basira da zurfin kirdado ke iya tsinkayarsu lokacin da yake dabbakawa.

Wasu kuma sun ce ma'anar fadin Allah madaukaki (haske kan haske) shi ne hasken shiriya da bayani wanda ya zo da shi daga gare shi.

Wasu kuma sun ce: ma'anarsa shi ne sashensa na haskaka sashe, ankuma ce ma'anarsa shi ne cewa mumini yana jujjuyawa cikin haskaye guda biyar: kalamansa haske, iliminsa haske, mashigarsa haske, mafitarsa haske, matafiyarsa haske zuwa ranar kiyama zuwa shiga aljanna, ance ma'anarsa shi ne haske wutan kan hasken haskekan hasken mai kan hasken fitila kan hasken kwalaba.

Sannan fadinsa madaukaki:   

 (يَهْدِي اللهُ لِنُورِهِ مَنْ يَشَاءُ)

Allah yana shiryar da wanda ya so zuwa haskensa.

Ma'ana yana shiryar da wanda ya so zuwa ga addininsa da imani  da ya aikata masa wani ludufi ta yadda mutum shi da kansa zai zabi imani idan ya san cewa shi ludufi ne.

Wasu kuma sun ce: ma'anarsa shi ne Allah yana shiryar da wanda ya so zuwa ga annabtarsa daga wanda ya san cewa ya cancanceta, idan ya kasance daga ma'abota ayyuka nagargaru masu kyawu. Zabisa ne ba tare da tilashi ba. Wasu kuma sun ce: ma'anar (Allah yana shiryar da wanda ya so zuw aga haskensa) shi ne yana hukunci da imaninsa ga wanda ya so daga wadanda sukai imani da shi.[38]

Allama daba'daba'i mawallafin tafsirin mizan yana cewa cikin fadinsa madaukaki:

 

 (يَهْدِي اللهُ لِنُورِهِ مَنْ يَشَاءُ)

Allah yana shiryar da wanda ya so zuwa ga haskensa..

Sabuntawa ana kafa dalili da shi ka keabantar muminai da hsken imani da ma'arifa da haramtuwarsu wadanda ba muminai daga gare shi, daga siyaki zubin jumlar lallai abin daake nufi da fadinsa madaukaki (wanda ya so) shi ne mutanen da ya ambace cikin fadinsa:

  (رِجَالٌ لا تُلْهِيهِمْ تِجَارَةٌ وَلا بَيْعٌ عَنْ ذِكْرِ اللهِ)

Mazaje ne kasuwancida saye da sayarwa basa shagaltar da su daga barin Ambaton Allah.[39]

Har zuwa karshen ayar, abin nufi da fadin wanda ya so sune muminai bisa siffantuwar cika da kammaluwar imaninsu, sannan ma'ana shi ne lallai kadai Allah ya shiryar da wadanda suka cudanya da kamalar imani zuwa ga haske koma bayan wadanda suka cudanya da kafirci wadanda da sanu daga baya za a kawo batunsu.

Ba ma'anarsa shi ne Allah yana shiryar da wasu ba'ari zuwa ga haskensa da mashi'arsa koma bayan ba'ari, da har za a bukatu cikin cika magana da cewa lallai yana son shiryarwa idan mahallin shiryarwar ya yi tanadin da ya kamata zuwa ga kyawuntar zuciya da tsaftatar hali, hakan yana daga abin dama'abota imani suka kebantu da shi koma bayan ma'abota butulci da kafirci. Sai ka fahimci wannan.[40]

Dalili kan wannan shi ne abin dazai zo daga fadinsa madaukaki:  
 
(وَللهِ مُلْکُ السَّمَاوَاتِ وَالأرْضِ )[41]  

Mulkin sammai da kasa na Allah ne.

Zuwa karshen ayar da bayani mai zuwa insha Allahu.

Maganar mai tafsirin mizan ta kare an wuce mukamin.[1] Ma'ida:15

[2] An'am:12

[3] Shura:52

[4] Tahrim:8

[5] Hadid:13

[6] Biharul anwar:215

[7] Alu imrana:179

[8] Biharul anwar: m 53 sh 29

[9] Biharul anwar: m 8 sh 715, sannan nayi bayani filla-filla dangane halittar hasken A'imma cikin littafin (Anwarul kudsiyya) an buga shi zaku  iya samunsa cikin mausu'a

[10] Biharul Anwar: m 57 sh 196

[11] Biharul Anwar: m 35 sh 394

[12] Mizanul hikima: m 4 sh 3387

[13] Mafatihul jinan na shaik Abbas kummi

[14] Kahfu:110

[15] Mizanul hikima: kalimatun nur

[16] Hadid:13

[17] ()  النور: 41.

[18] An'am:122

[19] Nuru:35

[20] Nur;41

[21] Isra'I;44

[22] Nuru:35

[23] Nuru:35

[24] Nuru:35

[25] saffi:32

[26] An'am:12

[27] Hadid:28

[28] Zumar:22

[29] ()  الميزان :15 134.

[30] ()  التبيان :7 138.

[31] Nuru:35

[32] Nuru:35

[33] Nuru:35

[34] Nuru:35

[35] Muluk:35

[36] Nuru:35

[37] Muluk:3

[38] Mizan: m 15 sh 135

[39] Nuru:37

[40] Tafisrul mizan: m 15 sh 152

[41] ()  النحل : 74.