WALKIYA DAGA HASKEN ZAHARA (AS)

 

 Hakika Allah matsarkaki ya bamu labari cikin littafinsa mai girma da cewa maksudin halitta da falsafar rayuwa da sirrin halitta da hadafi daga kasantattu da masu iya kasncewa kadai shi ne bauta da saninsa matsarkaki madaukaki, sannan sanin nafsu din mutum da hakikanin dan adam wanda saboda shi ka halicce shi domin ya halifanci ubangijin talikai cikin kyawawan sunayensa da madaukakan siffofinsa ya kuma kasance mihwari cikin duniyar kasantuwa da zama igiyar dangantaka tsakanin ubangiji da halittu.

Abin da ake muradi daga rayuwa mudlak da ma'arifa mudlaka , da sanin nafs da ubangiji da halitta, domin tabbatuwa ibadar shari'a wacce take ginuwa kan zabin mutum ya kuma zama igiyar sadarwa cikin duniyar mulk cikin bakan nuzuli da su'udi tsakankanin duniyoyin malakutiyya nuraniyya da suka gabata daga duniya mafi daukaka da kaskantatta kamar misalin duniyar haskaye ashbahu da ar'wahu da zarru wanda ake kira da duniyar daukar alkawali tsakanin duniyoyin malukutiyya masu riska.  Kamar misalin duniyoyin kabari da barzahu da ranar kiyama ko jahimu ta wuta.

Wadannan Ma'arifofi basu tabbatuwa musammam ma sanin Allah matsarkaki- face ta hanyar wahayi da kur'ani, sannan lallai mahaskakan hankula sun bushe gaban girma da girmamar Allah, tunanin bil adam cikin fagen tsarkakarsa da zatinsa da siffarsa da ayyukansa baya bakin komai face wahami ababen watsi

 «كلّ ما ميّزتموه بأوهامكم في أدقّ معانيه مخلوق مصنوع مثلكم مردود إليكم »

Dukkanin abin da kuka mayyaze shi da wahamanku cikin mafi dandakar ma'anarsa abu halitacce misalinku mai komawa gare ku.

 

Da fitila mai haske wacce take haskaka hanyar masu suluki zuwa hasken haskaye da:

 (نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأرْضِ )

hasken sammai da kasa.[1]

kadai dai hakan na cikin mishkat kwaryar zuciya wacce ta haskaka da hasken wahayin littafinsa da ya saukar ga annabinsa (s.a.w)

 (كِتَابٌ أنزَلْنَاهُ إلَيْکَ لِتُخْرِجَ النَّاسَ مِنَ الظُّـلُمَاتِ إلَى النُّورِ) .

Littafine da muka saukar da shi zuwa gareka domin ka fitar da mutane daga duffai ya zuwa ga haske.[2]

 

Amma mtum wanda ada bai kasance komai ba, sai Allah ya halicce shi ya hura ruhinsa cikin sa domin ya kasance ruhin duniya da halifantar da shi cikin sunayen Allah da dora masa ilimin Allah, Allah ya sanar da shi abin da bai sani b, ya bashi kunne domin ya saurari ayoyinsa masu daraja saukaka, ya bashi gani domin ya ga ayoyin hikimarsa mai haske, ya halicce shi daga ruwa cudanyayye domin ya jarraba shi, daga ruwa wulakantacce domin ya kai ga ibadarsa da saninsa da yakininsa, ya san yakini da ainul yakin da hakkul yakin ya zuwa tsakanin zira'i biyu ko mafi kusa da haka

(فَـتَبَارَکَ اللهُ أحْسَنُ الخَالِقِينَ ).

Albarkun Allah sun bayyana mafi kwarewar masu halitta.[3]

 

Mutum bai iya cimma burinsa, ibadarsa bata saukaka gare shi, saninsa bai tabbatuwa face da tsarkaka da koyarwa daga, da adini mai kima mai sauka daga madaukaki mai girma, da shar'antawa daga gare shi da tablig din annabawa a manzanninsa, domin su kira mutane zuwa ga tauhidi da tsayar da adalci, da shiyarda su zuwa ga hanya madaidaiciya.

Hadafi da manufar halitta da ribar aiko annabwa da manzanni kadai dai shi ne ibada da ma'arifa da samun arzikin duniya da lahira wanda yake kunshe cikin addinin Allah wanda ke kan shiriya bai karkace ba, aiko annabawa da saukar da litattafai hakika sun kammala shari'a sama manzanci ya cika da cikamakin annnbawa shugaban manzanni Muhammad bn Abdullah (s.a.w) lallai shi cikamaki ga abin da ya gabata makulli ne ga wanda zai fuskanto   

(فَأقِمْ وَجْهَکَ لِلدِّينِ حَنِيفآ فِطْرَةَ اللهِ الَّتِي فَطَرَ النَّاسَ عَلَيْهَا)

Ka tsayar da fuskarka ga addini kana karkata ga gaskiya halittar Allah wacce ya halicci mutane kanta.[4]

 Addinin muslunci mabayyani ya cika da wilayar sarkin muminai Ali (as) a halifofi goma sha daya daga bayansa wadanda cikamakinsu shi ne Mahadi daga iyalan Muhammad

 

(اليَوْمَ أكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإسْلامَ دِينآ)

A yau ne na kammala muku addininku gare ku na cika ni'imata kanku na yardarm muku muslunci a matsayin addini.[5]

Sai annabi mafi girma (s.a.w) birnin ilimi Ali kofarta duk wanda yake nufi birni da ma'arifa da ilimi da ibada da hikima to ya shigo ta kofarta, domin babu hanyar shiga birnin annabta na Allah wanda ya tattaro ilimai mutanen farko da na karshe face daga wannan kofa ta Ali (as) lallai shi hanyar ce madaidaiciya, kuma shi ne labari mai girma, da Kalmar takawa, shne igiyar karfaffa, shi ne kofar Allah wacce daga gare ta ake zuwa wajensa. Shi ne sababi sadadde tsakanin sama da kasa, shi isma ne daga kuskure da bin son rai, dukkanin wanda ya je masa ya tsira dukkanin wanda ya juya masa baya daga wilayarsa da imamancinsa ya nutse ya halaka.

Arziki baki dayan mutane na cikin ma'arifa da bautar Allah daga hanyar sakonnin sama wanda suka misaltu cikin annabta mafi girma da kuma dawwamuwarta har zuwa tashin kiyama cikin imamanci mafi girma.

Sannan igiyar sadarwa ga kowacce al'umma tsakanin annabta da imamanci har zuwa ranar tashin kiyama ba kow abace face shugabar mataye Fadima Zahara (as) lallai ita ta tattaro tsakanin hasken annabta da imamanci, ita daga tsatson manzon Allah Muhammad (s.a.w) kuma itace matar waliyin Allah sarkin muminai Ali (as) mahaifiyar A'imma zababbu goma sha daya daga cikin su Mahadi muntazar wand akai alkawarin dawowarsa (as) da zai cika kasa da adalci bayan ta cika da zalunci da danniya, ita bishiya ce da jijyarta ta tattaba reshenta yana sama tana bada abin cinta kowanne lokaci da izinin ubangijinta.

Fadima Zahara ta kasance mishkat din hasken Allah tun daga Adamu har zuwa cikamakin annabawa daga shugaban wasiyyai har zuwa cikamakin wasiyyai amincin Allah ya kara tabbata gare su baki dayansu, ta kasance daen lailatul kadari wanda cikin sa aka yaye halittu daga saninta, lallai ba a san girman matsayinta lallai an jahilci hakkinta.

ولأيّ الاُمور تُدفن ليلا         بضعة المصطفى ويُعفى ثراها

بنت من ، اُمّ من ، حليلة من         ويلٌ لمن سنّ ظلمها وأذاها

Da wannan dalili aka binneta tsakar dare tsokar Musadafa sannan   aka bushe aka bushe gurbin kabarinta.

Ita wannan `yar wace ce mahaifiya wace ce atar wace ce azaba ga wanda ya sunnanta zaluntarta da cutar da ita.

Tabbas kowa ya yi ikirarin daga mai yarda da mai sabawa kai hatta wadancan wadanda sukai suka cikin riwayoyin da suka cikin falalar Ahlil-baitin isma: sai dai cewa wand abaya magana daga son rai manzon Allah mafi girma (s.a.w) cikin hakkinta ya ce:

«فإنّما هي ـفاطمة ـ بضعة منّي يُريبني ما أرابها، ويؤذيني ما آذاها»،

Kadai dai ita Fadima tsoka ce daga gare ni dukkanin abin da ke kokwantanta yana mini kokwanto, dukkanin abin da ya cutar da ita yana cutar dani

 وقال  9: «فاطمة بضعة منّي ، فمن أغضبها أغضبني » .

A wani wajen ya ce: Fadima tsoka ce daga gare ni dukkanin wanda ya fusata ta ya fusata ni.

Fadima ta kasance tsokar Musdafa yanki mai albarka daga farkon abin da Allah ya halitta da mafi daraja wanda ya yi furuci, ita ismullahi A'azam ce cikin kyawawan sunayen Allah, ita misali ce mafi daukaka cikin madaukakan misalai, dukkanin wanda ya fiusata ta ya cutar da ita ya cutar da Allah da manzon Allah (s.a.w) dukkanin wanda ya fusata Allah da manzon Allah (s.a.w) Allah da Mala'iku da mutane baki dayansu sn tsine masa har tashin kiyama, dukkanin wanda ya fusata Fadima ya cutar da ita bayan wafatin babanta?!

Allah madaukakin sarki cikin kur'ani mai girma yana cewa:

 

 (إنَّ الَّذِينَ يُؤْذُونَ اللهَ وَرَسُولَهُ لَعَنَهُمُ اللهُ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَأعَدَّ لَهُمْ عَذَابآ مُهِينآ) .

Lallai wadanda suke cutar da Allah da manzonsa Allah ya la'ancesu cikin duniya da lahira ya kuma yi musu tanadin azaba wulakantacciya.[6]

Hakika ya tabbata daga bangarori biyu sunna da shi'a cewa lallai manzon Allah mafi girma (s.a.w) ya cewa Fadima Zahara (as):

«إنّ الله يغضب لغضبکِ ويرضى لرضاکِ » .

Lallai Allah yana fushi da fushinki yana kuma yarda da yardarki.

Ba komai wannan magana ta annabi ke shiryarwa ba face kan ismar Zahara (as) sakamakon dayantuwar fushin Fadima da fushin Allah mudlakan, hakama yardar Allah da yardarta sun hade ta fuskanin idalaki.

Fadima ta kasance mahallin sirrin Allah, mahaskakar hasken taurarin sama wilaya da imamanci, ma'ajiyar asrarun littafin shiriya da farin ciki.

 (فِيهَا يُـفْرَقُ كُلُّ أمْرٍ حَكِيمٍ ).

Cikin ta ake raba dukkanin wani al'amari mai hikima.[7]

ورأى الرسول في ليلة معراجه كتب على باب الجنّة : «فاطمة خيرة الله».

Manzon Allah cikin daren da yaje mi'iraji ya ga an rubuta kan wata kofar aljanna: Fadima ce mafi alherin halittar Allah.

  ta kasance zuciyar Musdafa sanyin idonsa hasken da yake tafiya gabansa ranar da:

 (يَسْعَى نُورُهُمْ بَـيْنَ أيْدِيهِمْ ) ،

Haskensu yana tafiya gabansu.[8]

 «فأوّل شخص يدخل الجنّة فاطمة »،

Mutum na farko da zai fara shiga aljanna itace Fadaima.

«زارک آدم ومن دونه من النبيّين ».

Adamu ya ziyarce da wasunsa daga annabawa.

و(لَقَدْ مَنَّ اللهُ عَلَى المُؤْمِنِينَ إذْ بَعَثَ فِيهِمْ رَسُولا مِنْ أنْفُسِهِمْ ) .

Hakika Allah ya yi tautayi kan muminai yayin da ya aiko da mmanzo cikin su daga kawukansu.[9]

Ga wannan mmanzo mafi girma (s.a.w) Allah kyautar kausar Fadima Zahara

 (إنَّا أعْطَيْنَاکَ الكَوْثَـرَ.

Lallai mu mun baka kyautar kausara.[10]

Sai dai cewa wannan kausar ta Allah hakika an karya kashin awagarta an kwace mata hakkinta, an zubar da cikin jararinta shahidi, ta zamanto kamar hiyali ta kasance tana cewa:

«صبّت عليّ مصائب لو أنّها         صُبَّت على الأيام صرن لياليا»

 

Musibu sn sauka kaina da ace zasu sauka kan kwanaki da sun za


[1] Nuru:35

[2] Ibrahim:1

[3] Muminun:14

[4] Rum:30

[5] Ma'ida:3

[6] Ahzab:57

[7] Dukkan:4

[8] Tahrim:8

[9] Alu imrana:164

[10] Kausar:1