فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI AMFANI DA ITA

 

bayyanannen abu ne  cewa tsakanin  ma'anoni da lafuzza akwai dangantaka mai karfi da azurfi, lalle lafuzzan da ake amfani da su cikin kowanne yare kadai dai su kamar gada ce a tsani da ta hanyarsu ake  tsallaka  zuwa ga ma'ana`` hakika an sanya lafuzza tun farko da kebantacciya sanyawa ana kiranta da(wada’u) sanya ta farko a lugga ya zama dole mu fara sanin  kowacce kalma a luggance, hakika ya zama dole mu fara sanin ma'ana da farko, abin da ke daukar nauyin bayanin ma'anonin kalmomi shi ne kamus din yare, sau da yawa ya kan nakalto lafazi daga ma'anarsa ta farko ya zuwa sabuwar ma'ana da wasu ba'ari ke amfani da shi a kankin kansa sai a kira shi da ma'ana ta biyu sannan ya kan sassabawa sakamakon yanda a kayi amfani da shi cikin  ilimai da fannoni da sana'o'i da kuma tsakankanin mutane.

gabanin dilmiya da kutsawa cikin bahasi da ya kebanta da tarbiya, ya zama dole mu san ma'anar kalmar  tarbiyya cikin yare da (isdilahi) yadda aka yi amfani da ita wajen masana halayya dan adam da zamantakewa  da addini da falsafa da wasunsu.

 Kalmar tarbiyya ta samo asali a luggance daga) (رب وربب sannan ta na da wasu ma'anoni daban-daban wani lokacin takan zuwa da ma'anar siyasa  mai tarbiyyar al'umma wanda ke  shugabantar su ya na sama da su wani karo kuma da ma'anar mulki ai mamalakin wani abu ko ya mallaki kasa kuma shi ne shugaban wata jama'a sarki, haka a kan fadi تربب الأرض))  wannan ma'ana ga wanda yayi da'awar cewa wannan fili na sane, ita kalmar (رب)  masdar ne cikin harshen larabci wadda jam'inta shi ne  أرباب وربوب

: shugaba mamallaki

sannan ita kalmar na daga sunayen Allah ubangijin talikai ko kuma dangata wani abu ya zuwa gare shi kamar ince ubangiji na wanda ya raine ni ko kuma ace shugaban matukan jirgin ruwa, Kalmar ربوبة) (وربوبية sunaye ne daga رب akan kiran malami masani ubangiji da الرباني  haka ma  ta kan zuwa da ma'anar mai gyara kamar ace wanda ya tarbiyantar da abu da ma'ana gyara shi ko ace ya raini yaro har sai da ya yi hankali saboda kalmar rabbi tana da ma'anar mai kawo gyara

sannan ta na zuwa da ma'anar karuwa kamar فرب النعمة ni'ima da ma'anar ya karata wani lokaci takan zuwa ma da ma'anar zama cikin wani wuri.

Wani lokacin takan zuwa da ma'anar tattarwa kamar a ce :  ربا الشیء,

ya tattara wani abu  ko kuma a ce :تربب القوم  mutane sun tattaru , akan kira ruwan mai tarin yawa da الربب الماء الكثير , ko kuma a cewa katon da da الربة الضخمة , ko kuma ace : wannan matattarar jama'a ne da مرب القوم ko kuma الرباب da ma'anar jama'a.

sannan bugu da kari takan zuwa da ma'anar kyakyawan abu tsaftatacce sai a ce : ربا الدهن  ai ya tsaftatace man ya kyawunta shi ko kuma الرباب da ma'anar ruwa mai dadin sha, ko farin hadari sai a kira shi da ربابة da dai sauransu.

 

ya zo cikin littafin mufradat ragib:

cewa kalmar rabbi cikin asalin tarbiyya shi ne farar da wani abu daga hali zuwa hali ya zuwa haddin kamala a kan ce: ربه رباه رببه kamar yadda ya zo cikin fadinsu:

 لأن يربني رجل من قريش خير من أن يربني  رجل من هوازان

 bakuraishe yayi mini tarbiyya ya raine ni shi ya fi alheri da ace wani mutum daga hawazan ya yi mini tarbiyya.

rabbi masadari ne na aro ga  wanda ya yi aiki ba a fadin kalmar رب kai tsaye ba tare da jingina ma ta wata kalmar ba kamar ace رب الدار mai gida, ko kumaرب الإبل  mai gidan wannan rakumi kamar yanda abdul mudallib ya fadawa rundunar sarki abrahata da suka rusa ka'aba suka kama masa rakuma sai y ace :

 أنا رب الإبل وللبيت رب يحميه

hakika muna iyayen gidan  wadannan rakuma amma shi wannan gida na da nasa ubangijin da zai bas hi kariya, ba fadin wannan kalma kai tsaye face ga Allah madaukaki wanda ya dauki nauyin kula da maslahohin ababen halitta

بَلْدَةٌ طَيِّـبَةٌ وَرَبٌّ غَفُور[1] 

gari dadin zama da ubangiji mai yawan gafara. 

 kan haka ne fadinsa madaukaki:

[2] وَلا يَأمُرَكُمْ أنْ تَتَّخِذُوا المَلائِكَةَ وَالنَّبِيِّينَ أرْبَاباً 

bai umartar ku da rikar mala'iku da annabawa iyayengiji, ababen bautawa da kuke raya cewa sune masu halitta  sanadin sababai majibancin maslahohin bayi,  kari kan haka akan kiransa da

رَبِّ العَالَمِينَ[3] 

 ubangijin talikai.

رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الأوَّلِينَ[4]     

ubangijinku da iyayenku na fari 

  wani sa'ilin akance mai gida ko mai doki ubangijin gida ubangijin doki, kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki

اذْكُرْنِي عِنْدَ رَبِّكَ فَأنسَاهُ الشَّيْطَانُ ذِكْرَ رَبِّه[5]   

 ka ambace ni wajen ubangijinka sai shaidan ya mantar da shi tunawa dubangijinsa  (ka koma zuwa ubangidanka ) 4.

hakama akan yi amfani da kalmar tsakanin dayan ma'aurata idan ya kebanci tarbiyyar dan da tsohon mijin matarsa (agola) ubangiji ya na fadi:

وَرَبَائِبُكُمُ اللاَّتِي فِي حُجُورِكُم[6]

da agolan da suke cikin dakunanku.

haka takan zo kan hadarin da ke da mamakon ruwa saboda shi hadari na zubar da ruwa ya zama sanadin rayuwa tsirrai .

amma kalmar tarbiyya cikin isdilahi : babban malami na biyu farabi cikin littafinsa me suna (neman rabauta) cikin bayanin tarbiya da ta'alimi ya ce: ta'alimi shine samar da falaloli na nazari cikin al'ummu da birane, amma ladabtarwa shi ne samar da hanyar darajoji na halitta da sana'o'i na ilimi cikin al'ummu, shi ta'alimi ya na kasancewa kadai cikin magana, amma tarbiyantarwa shi ne al'ummu birane da ayyukan dukkanin halittu su juya su zama malakarsu dabi'arsu ilimi da basu iya rabuwa da shi wanda himmarsu za ta dinga yunkura wajen aikata ta, wannan ayyuka su mamaye zukatansu ta yanda zasu wayi gari kamar masu soyayya da su.

wajen wasu ba'ari koyarwa ya ratayu da hankalin nazari ma'ana abin da za'a iya sanin wani abu ta hanyarsa, ita kuma tarbiyya ta ratayu da hankalin aiki ma'ana abin da ake aiki da shi.

 [1] Saba'i:15

[2] Ali Imran:80

[3] Fatiha:2

[4] Shu'ara:26

[5] Yusuf:50

[6] Nisa'i:23