فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

WANE NE MAI TARBIYA ?

 

 mai tarbiya na farko cikin duniyar halitta da dabi'a da abin da ke kunshe bayanta shi ne Allah matsarkaki , hakika shi ne ubangijin talikai, hakika kalmar رب da abubuwan aka keto daga gare ta sun zo cikin kur'ani har kusan wurare (980) kur'ani ya tattaro mutanen farko da wanda za su zo daga baya hakika shi kur'ani ya tattara dukkanin abin da ke cikin littafan sama da addinan ubangiji, shi littafi ne mai gadi kan littafan sama  da kasa, shi ya tattara dukkanin iliman magabata da wanda za su zo daga baya, sannan an tattara abin da ke cikin kur'ani cikin surar fatiha, surar ta fara da fadinsa madaukaki:

الحَمْدُ للهِ رَبِّ العَالَمِينَ[1] 

 (godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai)

sai ya siffanta kansa da ubangijintaka, hakika shi ne mai tarbiya na farko ga dukkanin duniyoyi madaukaka da akasinsu, da abubuwa mujarradai marasa jiki da masu jiki, saboda kare dokokin sabubba wanda ke jagorantar wannan duniya sai Allah ya sanya

فَالمُدَبِّرَاتِ أمْر[2]ا

   sa'annan su kasance masu shirya gudanar da al'amari.

 ta kasance sanadin samuwar abubuwa da dokokin tarbiya ke jagorantarsu dukkanin wannan kadai ya kasance bisa rahamarsa duniya da lahira.

 Sannan tarbiya ta yi tajalli da dauko iliman ubangiji cikin annabawa (as) hakika su annabawa sune mabayyanar tarbiyyar ubangiji hakika ya aiko su don tarbiyar mutane da shiriyar dasu da tsayar da adalci da daidaito hakika annabi ya kasance mabayyanar ubangijintakar ubangiji, bauta zinare ne wanda zurfafarsa ubangijntaka, annabi muhammadu ya kasance cikamakin annabawa shugaban manzanni bawan Allah manzonsa .

sannan bayan annabawa wasiyyai da imamai (as) sun kasance kan tafarkinsu da hanyarsu da shiriyarsu, sun kasance mabayyanar tarbiyar ubangiji da annabi, an daura nauyin tarbiyyar mutane da shiryar da su a wuyayensu, sannan kuma bayansu nauyin ya koma kan malamai domin sune magada annabawa da wasiyyai cikin iliminsu da dabi'unsu da dukkanin matsayin da suke da shi, hakika su anayi musu hukunci da magadan da aka dora musu nauyin tarbiyyar mutane bayan sun tsarkake kawunansu da badininsu da ilimantuwa sannan sai su fito ya zuwa ga mutane  zuwa ga abin da zai rayasu su rungumi daukar nauyin tarbiyantarda su tarbiyya ingantacciya ta gargaru.

da hukuncin malamai nagargaru  iyaye maza da mata sune suke tarbiyya cikin iyali da dangi kamar yadda malamai suke tarbiyya a fagen makarantu da fagagen koyarwa, haka al'amarin ya ke cikin ragowar fagagen rayuwa, haka ma cikin ragowar mutane dole a samu wani mai tarbiyantarwa da koyarwar saboda hakan na daga sunnar ubangiji kuma ba za ka taba samun sauyi ko canji cikin sunnar ubangiji

wadannan da muka kawo dukkaninsu mabayyana ne na ubangijin talikai a mukamin tarbiyya, abin da sukayi tarayya ciki shi ne tarbiyya amma sukan banbanta a bangaren fadadawarta da tsukewa bisa la'akari da fadin duniyar da take cikin kowanne dayansu.

misali cikin ilimin mandiki mas'alolin nazari dole su tuke ga badihiyat (sanannun abubuwa ) ma'ana zatin abubuwa saboda shi zatin abu bai bukata kawo dalili kansa,ba don hakan ba da ya lazimta maimaici da tasalsul wanda gurbatattu ne a mahalinsu, saboda haka iliman nazari na tukewa ya zuwa mukaddimar badihiyya na zati  haka al'amarin ya ke cikin tarbiya da mai yinta  hakika ita ma tana tukewa ga tarbiya ta zati wacce ta ke tarbiyya ce ta ubangiji da ta bubbugo daga rububiyarsa girmansa ya girmama, iyaye masu tarbiyya ne da suke komawa ga malamai cikin tarbiyantar da kawukansu, su kuma malamai na koma ga annabawa da imamai (as) wanda ke dauke da tarbiyyar zati hakika su kuma imamai (as) suna komawa ga Allah ubangijin talikai domin shi ne mai tarbiyya na farko, sai tarbiyyarsa ta halitta cikin halittu da ta shari'a su yi tajalli cikin halittunsa, haka cikin annabawa malamai da iyaye, tarbiyya da ke bijira wadda a ke tsiwirwirarta a wannan lokaci na tukewa ya zuwa tarbiyyar ta zati tabbatacciya  sai a lura.

 [1] Fatiha:2

[2] Annazi'at:5