فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

IYALI A LUGGANCE

 

kalmar   (iyali) ta samo asali ne daga kalmar الأسر ma'ana daurewa tufkewa kamar fadin larabawa na daura siddi haka ana kiran fursunan yaki daga wannan ace masa asir sannan akayi amfani da kalmar cikin dukkanin wanda aka kayyade aka tsare shi duk da a zahiri su iyali ba daure suke da igiya ba  a zahiri, domin iyalin mutum sune wanda suka dogara da shi da karfafa.

wani ba'ari daga mutane na raya cewa iyali ba komai ba ne face sakamako halittar sha'awa ta jinsi da bukatuwar dan adam na dabi'arsa, kuma bai da banbanci da ragowar dabbobi cikinta, ta kasancewa biye da abin da sha'awa ta halitta ke shiftawa ta kaishi  zuwa ga karkata dabi'ar halittarsa sha'aninsa bai da wani banbanci da ire irensa cikin duniya dabbobi.

kamar yadda wasu  daban ke raya cewa iyali daidakun jama'a daga jagorori ke samar da su, saboda samar da iyali na hannun mutum mai kawo gyara, yana da hakkin karawa ko ragewa cikin assasawa ya na iya canjawa  yadda zuciya ta so masa .

wasu ne masa kallon wani tsari mai cin gashi kansa sabanin wasunsa daga tsarin zamantakewa.

gaskiyar ala'amari shi ne shi iyali wani abu ne da yake da dangantaka mai karfin gaske da akidun wannan al'umma da wayewar al'adunta da tarihinta da abin da ta ke tafiya kai cikin siyasarta tattalin arziki tarbiyya da alkalanci, abubuwan da suke kewaye da ita daga yanayi cikin fannoni daban-daban na bangaren rayuwa, shi daidai ya ke da kowanne gaba cikin rayayyen jiki, tsarin iyali baya daga kirkirar daidaikun mutane.

fagen iyali tun zamani baya ya kasance ya na nufin dangancewa ya zuwa dangi da sanya mata alama tunawa da wannan dangi.

wajen mutanen kasar girka da rumawa iyali na nufin  wani tsari da dukkanin makusanta ke shiga karkashinsa  mazaje  sune ke hada kan dangi, haka bayi da iyayayen gijinsu da bayin matayensu wanda shugaban da ke rikarsu matsayin `ya `ya, ko ma ya yi da'awar su matsayin makusanta sai su wayi gari matsayin bangare cikin wannan dangi su dinga amsa sunan wannan dangi a basu damar shiga cikin sha'anin addini da na rayuwar yau da gobe, ma'ana iyali wajen girkawa da rumawa ya tsayu kan da'awa ba kusanci na jini ba, uba wajen mutane girka zamanin da ya shude shi ne mai zabar wanda zai haifa masa da cikin taron danginsa idan dangin suka goyi baya sai wannan da ya shiga danginsu a riskar da shi ciknsu su dinga kidaita shi daga gare su , amma idan suka ki goyon baya to dangantakarsu ta yanke da mahaifinsu da danginsu.

hakaal'amarin ya kasance cikin larabawa gabanin muslunci, hatta dukiyar dangi ta kasance mallakar kowa daga mutanen danginta ma'ana mallaka ce  a ma'anance ba ta mutum guda ba shari'a mai tsarki da ta zo sai ta canja tsarinsu wajen iyakance iyali , tayi wurgi da kufaifayinsa cikin abin da ya rataya da kisasi,  shari'ar muslunci ta iyakance kisasi kisa kadai kan wanda ya aikata kisan a wani wurin kuma ya bar musu wasu dokokinsu na dangi cikin abin da ya ratayu da diyyar laifin da akayi cikin kuskure.

tsarin iyali da dangi a wajen larabawa gabanin muslunci shi ne da'awa sabanin dangantakar jini,  shari'a muslunci ta rushe wannan tsari na da'awa cikin fadinsa madaukaki:

وَمَا جَعَلَ أدْعِيَاءَكُمْ أ بْنَاءَكُمْ ذَلِكُمْ قَوْلُكُمْ بِأ فْوَاهِكُمْ وَاللهُ يَـقُولُ الحَقَّ وَهُوَ يَهْدِي السَّبِيلَ  [1]  

kuma bai sanya hankakarku su zama diyanku ba wannan dai maganar ku ce kawai da bakunanku Allah na fadin gaskiya kuma shi ne mai shiriyarwa ga hanya ta gari.  

 haka kuma ya haramta mutum ya yi da'awar wani mutum matsayin uba koma bayan mahaifinsa:

ادْعُوهُمْ لآ بَائِهِمْ هُوَ أقْسَطُ عِنْدَ اللهِ فَإنْ لَمْ تَعْلَمُوا آبَاءَهُمْ فَإخْوَانُكُمْ فِي الدِّينِ وَمَوَالِيكُم[2]ْ 

ku kiraye su ga mahaifansu shi ne mafi adalci wajen Allah idan kuma baku san mahaifansu ba to `yan'uwanku a addini da dimajojin.

 shari'a ta tabbatar da cewa da na shimfida ne (uba.

daga nan ne iyali suka dinga tsukewa da raguwa akwana a tashi ya zuwa wannan zamani da muke ciki, iyali ya na nufin miji da mata da `ya`yansu su ake kira da iyalin aure.

amma ayyukan iyali suna biye da fadin iyali da tsukewa, iyalin a zamanin da ya shude sun tattaro mafi yawancin al'amurran rayuwar zamantakewa sai dai daga baya ta samu tawaya kadan kadan har a ka wayi gari tarbiyyar iyali da koyar da su ya takaitu a wuyan iyali kadai

sannan kusanci cikin dangi da cigabansa da tsarinsa al'ummu sun yi saba ni cikinsa , akwai wadanda suke ganin hakan daga uwa mace  ana kiransa tsari na uwantaka, domin wajensu tushen kusanci na dangi shi ne uwa ita kadai, ana riskar da da  ga dangin mahaifiyarsa sannan suna la'akari da dangin uba matsayin bare ga da. wannan shi ne tsarin da ya kasance cikin kabilun kasar astiraliya. daga cikinsu akwai kuma mai ganin hakan na gangarowa ne daga uba mahaifi sun dauki uba shi ne tushe shi kadai ana riskar da da ya zuwa dangin mahaifinsa ana kiran wannan tsari da tsarin iyalin ubantaka sannan cikinsu akwai masu gani tushen dangi daga uba da uwa ya ke tare da fifita bangaren uwa kan na uba, akwai masu ra'ayi fifita bangaren uwa kan na uba, akwai kuma masu ganin duk daya ne babu wani bangare da ya rinjayi daya kamar yadda aka nakalto daga turai amma gaskiyar magana shi ne bangaren uba ya rinjayi bangaren uwa  sannan akwai wadanda ke da ra'ayin cewa tushen dangi ya dori kan wani abu daban sabanin wadannan kamar yadda suka yi riko da al'adarsu cewa yayin da yaro ke jujjuyawa cikin mahaifiyarsa zai ayyana kansa da bangaren da zai kasance, wani lokaci bangaren uba wani lokacin kuma bangaren uwa kamar yadda ya kasance cikin zamani da suka shude. saboda haka ya bayyana cewa tushen dangi cikin wannan mutane bai kasance daga jini ba,  haka bai da banbanci tsakanin uwa da uba kadai dai al'amarin na biye tsarin zamantakewar kowacce al'umma cikinsu .

saboda muhimmacin mas'alar iyali ita ce ke mamayar lamba ta farko cikin mas'alolin zamantakewar al'umma masu muhimmanci domin ita ce sinadarinta na farko, saboda kowacce al'umma na farawa daga adadin wasu iyalai domin da'ira ce guda biyu da baza su taba rabuwa da juna ba, saboda magana kan iyali ba surutu ne kawai mara ma'ana  a'a hakan ya kasance ne saboda tsananin bukatuwar jama'a ya farlanta bahasi kanta, magana game da ita ta fuskanin mahangar muslunci ba bakon abu bane,  hakikanin muslunci ya dace da ita saboda dabi'ar ta yi daidai da ita daga warware matsaltasalinta gwargawadon yadda ya dace da dabi'arta, hakan ne dalilin da ya sanya magance mas'alar bisa hasken shari'arsa ta  adalci a kebance kuma yayinda  ake kaiwa  tsarkakakkiyar shari'armu hari da  yunkuri kawo sauye sauye da  fakewa da hujjars hada kan dokoki  bisa sallamawa tunanin `yan mulkin mallaka kafirai karkashin taken (dokokin halayyar dan adam)

da sannu mai karatu idan ya na biye damu zai riski dacewar mahangar muslunci cikin sanin hakikanin iyali kamar hadin kan zamantakewa, adalci, hikimar shari'a muslunci cikin tsara sha'anin iyali duka cikin bahasin wannan littafi da zai zo nan gaba.

tabbas tsara iyali a muslunce shi ne mafi kammala da gyaruwa daga dukkanin tsarurruka,yana daga cikin babban laifi da kuskuren da ba za'a taba yafewa ba ga dukkanin wanda ke kokarin da yunkurin kawo wani tsari sabanin muslunci cikin kasashen musulmi da al'ummunsu, duk me neman wani addini koma bayan muslunci ba za a taba karba daga gare shi ba.

muslunci bai gafala ba cikin mafi saukin al'amurra ta kaka zai gafala kan batun iyali  wacce ake kirga ta daga mafi muhimmanci tushen al'umma cikin rayuwa bil adama bisa dogaro da abin da ke tattare da ita na daga muhimman dalilai wajen kasancewarta. hakika iyali sune tubalin farko wajen kasantar da al'umma, idan iyali suka gyaru suka aminta to al'umma su zasu gyaru da su samu aminci, saboda wanzuwar al'umma da katangatarta ya dogara ne da wanzuwar iyali da katangartuwarsu , rabautar al'umma da cigabansu da wayewarsu ya jingina ga lafiyar iyali da rabautarsu , mafi yawancin matsalolin mu a cikin wannan zamani sakamakon yanayin tabarbarewar iyaline tushen yawancin matsaltsali da rigingimu cikin rayuwar daidaikunmu da jama'a na komawa ga iyali iyali ke shimfida al'umma da  cikata da daidaikunta, lafiyar wadannan daidaiku ta bangaren jiki hankali ruhi da sulukinsu yana jingine ne da kubutar wannan iyali daga ciwo da mummuna gado da tabarbarewa da kaucewa hanya ta gari, kiyayya da rigingimu.  saboda shi ne yanayi na farko da daidaikunta zasu taso ciki, cikin wannan yanayi zai dinga yin mu'amalarsa tunaninsa ruhinsa tausayi da sauransu, cikinsa zai ginu daga gare shi zai karbi dokoki da al'adun al'ummar yasan shari'a da tsare tsare da dokokin zamantakewa wadda ta ke cikin al'umma sannan shi ne zai yanke hukunci mai zurfi da yanayin dangantakarsa da ita, girmamawa da matsayarsa kanta, saboda haka muslunci ya himmatu matuka kan batun iyali.

shi ya sa ya sanya  tsare tsare wanda iyali za su ginu kai, tare da sanya shari'o'i daban-daban wadda a kanta ya  iyakance hakkoki da wajiban daidaikun wannan iyali ta fuskanin wani sashensu, haka ma muslunci bai kasa gwiwa ba wajen sanya mafita da warwara ga dukkanin matsaltsali da rigingimu da ka iya bijirowa wannan iyali cikin rayuwarsu ta yau da gobe ,

iyali sune matattarar jama'a tubalinta na gina al'umma sune tsanin da al'ummu masu girma ke tsayuwa kanshi. ginshikin ginuwar iyali kuwa shi ne auren da aka yi nasara cikinsa wanda ke kulla karfafaffiyar dangantaka da fahimtar  da mutunta juna tsakanin ma'aurata, ya kuma katange su daga rashin mutunta juna, sannan kuma alakarsu ta kara karfafa cikin samun azurtuwa da `ya`yaye  da zasu zama fure cikin gidansu su cika zukatansu da farin ciki da bushara da kauna.

mutum an halicce cikin jama'a ma'ane a dabi'ance bai iya rayuwa shi kadaiba tare da da kasantuwa cikin jama'a sai kadan daga cikin wanda suka ratse daga dabi'ar daga aka halicce su kai , saboda haka dole ne mutum ya samar da iyali da zai dinga samun nutsuwa tare da su da kamshim farin ciki .

muslunci ya zo ne shar'anta abin da zai tsare gida ya kiyaye mahalli da tsara al'umma da jama'a , sai ya kewaye iyali da karfaffa katangar  takawa, ya yada ruhin tarbiyya da koyarwa cikinta ya karfafa kafafunta da ilimi da addini, ya karfafa gininta da kyawawan dabi'u da darajoji, ya sanya mata dokoki don kareta daga rarrabuwa, ya sanya hakki ga kowanne mutum guda daga wannan iyali da ke kishinyatarsa wanda ya zama wajibi ya sauke shi ya sanya hakkoki da wajibai tsakanin ma'aurata, wacce karkashinta jirgin rayuwa ke gudana ya zuwa bakin gabar tsira.

da zamu aikata muslunci hakikanin aikatawa cikin rayuwarmu  da mun azurta da rabauta. ya zama tilas mu fito da muslunci zuwa matakin aikatawa mu kiyaye koyarwa hakikanin kiyayewa, da juyar da shi ya zuwa sulukinmu da aiki don tabbatar da amintacciyar rayuwa  yardadda da samar da yanayin fuskantar juna.

maganar gaskiya shi ne da yawa daga rigingimun  iyali da ke kaiwa ya zuwa kotukan shari'a hakan ya faru ne sakamakon jahilcin mutane  ga hukunce hukuncen muslunci  da dokokinsa da abin da ya zo da shi kan tsara iyali nagari, da ace munsan muslunci da ababen da ya zo da su cikin shari'arsa ma'ana kur'ani mai girma da mun rabauta da farin ciki cikin  daidaiku da jama'a, da gida da iyali mai cike da annashuwa sun kasance tare da mu, ya zama dole mu san shari'ar muslunci cikin iyali, domin ta dace da halittar da lafiyayyen hankali. hakika hankalin shari'a bai kasance

 kayyadadde  gama gari ko daskararre ba domin tushen shari'ar muslunci shi ne wahayi daga Allah ba dokokin da wani mutum dan adam ba da ya kirkira. kamar yadda shari'ar muslunci ta goge shari'ar da ta gabaceta ta annabawa, sannan ta kara mata wasu abubuwa dadi kan na baya shi ne kasantuwar muslunci addini kammalalle cikin kowanne gari da zamani.

mutum ya na rayuwa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa kasantuwarsa cikin inuwar iyalin da muslunci ke jagorantarta, me yafi kyawu daga wannan yanayi da uba musulmi ke dawo gidansa da masaukinsa ta yanda zai ga matarsa da `ya`yansa  ya manta da dukkanin abubuwan da suke damunsa da bakin cikinsa ya nutse cikin yanayi lafiyayye da ya cika da alakar `yan adamtaka, to hakan bai samuwa sai cikin iyali musulma da  musluncinsu ya ingantasu saboda ingancin akida da cikakkiyar aikatawa.

idan ba haka ba to hakika iyalai zasu wayi gari cikin barazanar tunanin yammacin turai da kirkirarrun dokokinsu, bakaken musifu suyi ta afkuwa cikin iyalai musulmi daga ranar da suka yaudaru  da zahirin yammacin turai masu fitinarwa.

hakika daruruwan miliyoyin musulmin a kasashen najeriya fakistan da indunusiya  ya zuwa ragowar yankuna rayayyu suna fama da dokokin da basu da alaka da muslunci ta kowacce fuska, hakika basu san dandanon muslunci ba basu san tarihin annabi da tsarkin dokokinsa.  dokokin muslunci wajensu basu kai ga takawa bakin kofar dakunan shari'ar aure da saki ba, ba za'a taba samun kubuta ba sai anyi watsi da wayewa da fahimtar yammacin turai, da dawowa ya zuwa mabubbugar wayewa da fahimtar muslunci.

ta bayyana cewa tunanin mutum ya gaza wajen samarwa dan adam farin ciki da rabauta da mutumtakarsa babu abin da ya rage wa mutum face sallamawa tsarin ubangiji  don kubuta, ba zai kasance ya na fagarniya cikinsa da shan wahala ba.

hakika fikirar ubangiji wacce ya saukar da ita ta hanyar annabawa wacce ta bayyanu cikin shari'ar da ta zo daga sama wacce ubangiji ya so ta zama mai hukunci kan dokokin da mutum ya kirkira, sannan wannan fikira ta ubangiji ta kasance kammalalliya da manzancin mafi girman annabawa cikamakinsu muhammadu dan abdAllah (saw) don ya zama shi ne tsari na har abada wanda zai samarwa da mutum tsira da rabauta duniya da lahira.ya rabauta tsiran gida biyu:

  اليَوْمَ أكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإسْلامَ دِينا[3]ً 

اyaune na  kammala muku addininku na cika muku ni'imar da ke gareni na yardar muku muslunci matsayin addini.

fikira da tunanin ubangiji bai zamo iyakantacce da zamani ko wani bigire sabanin hankali da tunani dan adam wanda iyakantacce ne ajizi, fikirar ubangiji na sanar da mutum cewa shi an halicce cikin mafi kyawun tsari da daidaituwa kuma rayuwarsa ba iya kance ta da iya kwanakinsa cikin ban kasa ba, bari ma dai ita mikakka ce cikin zamani da bigire, hakika ganawarsa da ubangiji ta kasance a duniyar kwayar zarra kuma ya yi imani da ubangijinsa da amsa kiran tauhidinsa, saboda cikin tsarin halittar dan adam akwai akidar samuwar ubangiji tun yarintarsa ya ke tambayar kansa kan ubangijinsa da neman hujja da dalili, yadda al'amarin ya ke shi ne dukkanin wani sababi ya na da wanda ya yi dalilinsa kuma dukkanin wani abu akwai wanda ya kera shi, dukkanin wani yaro ana haifarsa kan halittar tauhidi sai dai daga baya iyayensa su maishe shi yahudu ko banasare ko bamajuse.

 muslunci ya zo don gyara iyali, hakika al'umma ta gari na tasowa kan iyali nagari.

motsin mutum na kasancewa dalilin dayan manhajoji biyu na dan adam da ubangiji, dokokin ban kasa wanda dan adam ya kirkira da dokokin sama na Allah tsarki ya tabbata gare shi  wannan na nuni da cewa fikirar mutum kirkirar tunaninsace amma fikira da tunanin ubangiji daga wahayinsa ke zuwa. saboda haka dole ne mutane su kasance suna da wata manhaja da zata tarbiyantar da su da sanar da su ya ya zasu rayu tare da ubangijinsu da iyalensu da jama'arsu da dabi'ar da suke cikinta, wani lokaci tunanin dan adam kan gazawa ya kai ga inkarin ubangiji to ta kaka zai iya iyakance alakarsa da Allah ? kowa ya san irin makircin da turawan yamma ke shirya wajen tarwatsa iyali da rusheta, hakika kasar amerika wadda ta gina cigabanta da wayewarta kan tushen zahiri,  ta yadda ya kai ta aike da jirgi zuwa sararin samaniya ya yi yawo cikin samaniya amma duk da haka sun gaza wajen gina iyali guda wanda `ya`yanta za su rayu cikin kwanciyar hankali da farin ciki da tausayin iyaye, wajensu da zarar yarinya ta kai shekaru 12 - 14 cikin iyalin da suke kiransu da sunan jaha  sai su bude mata kofa su ce mata ke kin`yantu fita ki aikata abin da ranki ke so ke yanzu ke cikakkiyar macece doka ta baki ikon yin yadda kike so cikin dukkanin abin da ya kebance ki, me kuke tsammani sakamako zai kasance ? yarinya zata fito tana cikin shekarun `yan matancinta ta kutsa kanta cikin jama'ar da ta gurbata da fasadi, kurayen samari gurbatattu  na nan cikin tsimayinta  basu iya bata gutsiren gurasa sai idan ta sadaukar musu da mutuncinta da karamarta, bayan shudewar shekara 1 ko 2 da barinta gida sai ta wayi gari ana kidaya ta cikin miliyoyin matasa da suka afkawa shaye shayen tabar wiwi hashisha da hodar ibilis da sauran kayan maye masu hatsari da zasu dinga ingiza ta zuwa ga karuwanci, wannan shi ne yadda `ya`ya ke kasancewa ya ka ke tunanin iyaye da suke cikin halin tsufa da gazawa ba tsimi babu dabara da ta rage musu. wannan shi ne bala'in da amerika da ragowar kasashen da suka yi inkari da jayayya da ubangiji da addini da kyawawn dabi'u suka samu kansu. hakika sautin masanansu ya daga ya na ta neman dauki wajen dawo da ginin iyali nagari.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 [1]Ahzab:4

 

[2] Ahzab:5

[3] Ma'ida:3