فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

AUREN DABI'A

 

 daga cikin dokoki da sunnar dabi'a da ikon kan dukkanin halitta bari ma dai kan dukkanin wani abu koma bayan Allah matsarkaki shi ne dokar nau'i don ya zama dalili kan dayantakar Allah da dabantakarshi  shi ne kasantuwarsa daya rak wanda bai da kishiya babu misalinsa babu wani irinsa bai da nau'i.

dukkanin wani mai da'awa dole ne ya zo da shaida ba a karbar da'awa ba tare da ita ba  kamar yadda ya kasance cikin shari'ar Allah da dokoki dan adam, ana kiranta a shari'ar islama da shaida ta shari'a  tana kasancewa  shaidu biyu adalai, da ita da'awa ke tabbata ta zama gaskiya.

Allah matsarkaki yana da shaida a dabi'ance da ke shaida kan dabantakarsa da dayantakarsa, shi ne dokar kasantuwar komai nau'i hakika shi ya halicci kowanni abu tagwai nau'i  bibiyu don ya zama daga cikin ayoyinsa bisa cewa shi dayane rak tal bai da kishiya. domin  nau'i na tilasta cudanya da wani wanda hakan na bayyana bukatuwa da talautuwa, kuma hakan na korewa kasantuwa da wanda samuwarsa take ba wajibi ba a kankin kansa da zatinsa, bari ma dai ita bukatuwa na daga kebantacce abu da ya kebanta cikin wanda samuwarsu bata zama wajibi ba, shi Allah matasarkaki mawadaci ne abin godiya, babu cudanya cikinsa, bai da kishiya, shi samuwa ne tsantsa dayanda bai da na biyu, kwaya daya tal da ba cudanya cikinsa ya na nuni game da dokokin nau'i cikin littafi mai karamci da hikima:

[1] أوَ لَمْ يَرَوْا إلَى الأرْضِ كَمْ أ نْبَـتْنَا فِيهَا مِنْ كُلِّ زَوْج كَرِيم 

shin ba zasu yi duba zuwa ga kasa ba da yawa muka tsirar cikinta daga dukkan nau'i me kyawu.

اهْتَزَّتْ وَرَبَتْ وَأ نْبَـتَتْ مِنْ كُلِّ زَوْج بَهِيج[2] 

sai ta girgiza kuma ta kumbura ta tsirar daga dukkanin nau'i mai ban sha'awa.

وَمِنْ كُلِّ شَيْء خَلَقْنَا زَوْجَيْنِ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ[3] 

kuma daga kowanne abu mun halicci nau'i biyu tsammaninku zakuyi tunani.

  [4]وَأ نَّهُ خَلَقَ الزَّوْجَـيْنِ الذَّكَرَ وَالاُ نْثَى 

hakika shi ya halicci nau'i biyu sune mace da namiji.

[5] سُبْحَانَ الَّذِي خَلَقَ الأزْوَاجَ كُلَّهَا مِمَّا تُنْبِتُ الأرْضُ   

tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci nau'uka dukkaninsu daga abin da kasa ke tsirarwa.

وَاللهُ جَعَلَ لَكُمْ مِنْ أنفُسِكُمْ أزْوَاجا[6] 

Allah ya sanya muku matayen aure daga kawukanku.

وَمِنْ آيَاتِهِ أنْ خَلَقَ لَكُمْ مِنْ أنفُسِكُمْ أزْوَاجاً لِتَسْكُـنُوا إلَيْهَ[7]ا  

yana daga ayarsa ya hilttar muku mataye daga kawukanku do ku samu natsuwa ya zuwa garesu.

وَاللهُ خَلَقَكُمْ مِنْ تُرَاب ثُمَّ مِنْ نُطْفَة ثُمَّ جَعَلَكُمْ أزْوَاجا[8] 

Allah ya halicce ku daga kasa sannan daga digon  maniyi sannan ya sanya ku surkin maza da mata.

وَمِنَ الأ نْعَامِ أزْوَاجا[9]ً 

(daga dabbobi maza da mata ) 

[10] هُوَ الَّذِي خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْس وَاحِدَة وَجَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَا    

 shi ne wanda ya halicce ku daga rai guda ya sanya ma'aurata daga gareta.

خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْس وَاحِدَة ثُمَّ جَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَ[11]ا 

  ya halicce ku daga rai guda sannan ya sanya ma'uarata daga gareta.

يَا أ يُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْس وَاحِدَة وَخَلَقَ مِنْهاَ

زَوْجَهَ[12]ا

ya ku wadanda sukayi imani kuji tsoron Allah  wanda ya halicce daga rai guda ya halicci ma'aurata daga gareta ).

daga cikin ayoyinsa da a ke kafa dalili da dasu kan dayantuwar Allah da kasantuwarsa daya rak tal kuma shi bai da na biyu  shi ne kasantuwar kowanne wanne abu nau'i biyu, hakika ubangiji duk da cewa ya halicci mutum daga rai guda sai dai cewa ya halittar masa mace, ya halicci adamu (as) ya halicci hauwa'u daga ragowar yinbun halittar adamu ta kuma kasance mata gare shi.

daga abubuwan ke kara tabbatarda abubuwa nau'i biyu ne mace da miji, kasantuwar kasa da sama nau'i , dare da rana , kasantuwar duk wani tamata  da maza daga tsirrai da dabbobi mutane  kai hatta ruhi wanda ya kasance daga digon maniyyin namiji da jiki wanda ya kasance daga digon maniyyin mace dukkansu daga nau'ine.

dokar kasantuwar kowanne abu  nau'i biyu  mace da namiji ta gudana hatta kan sassan jikin dan adam misali jijiyoyin da suke cikin kwakwalwa sun kasance daga nau'in mace da namiji, barbarar halitta shi ma na gudana kan dokokin nau'i mace da namiji, daga gare shi yake haifar da duniyoyin badini da na ruhi  da zuciya misaliyya da  hisssiya, a duniyar jikkuna dab'ia da sinadarai abubuwa uku ke haifuwa da kasantuwa sune: ma'adanai tsirrai da dabbobi daga cikinsu kwai mutum, daga barbara akwai abin da ke kebanta da kammalallen mutum da duniyar dabi'a, sannnan cikakken mutum babu banbanci cikin kasantuwar mace ko namiji shi `ya`yan bishiyar samuwa ne, shi hadafi ne na harka guda biyu samuwa da samarwa, mace ta na da matsayin wajen halittar ubangiji ita kamar bishiya ce da jijiyarta ta tabbata  reshenta ya daga sama tana ba da kayan marmarinta kowanne lokaci, kammalallen mutum cikakke idan ya kasance daga namiji  matsayin mabayyanar hankalin game gari ne  idan kuma ya kasance mace  mabayyana ce ta surar ruhi game gari ragib isfahani cikin littafin mufradatul kur'ani ya na cewa:  ana amfani da Kalmar زوج kan dukkanin dayan cikin biyun nau'in masu abokantakar juna namiji da mace,  haka cikin dabbobi da wasunsu kamar huffi da takalmi fade da dukkanin abin da ya cudanya da wani da yake kama da shi ko kishiyar nau'in [13]

 ubangiji madaukakin sarki na cewa :

فَجَعَلَ مِنْهُ الزَّوْجَـيْنِ الذَّكَرَ وَالاُنثَى[14] 

sai ya sanya daga gare shi nau'i biyu mace da namiji

 

[15] وَزَوْجُكَ الجَنَّةَ 

 ka zauna aljanna da matarka.

[16] هُمْ وَأزْوَاجُهُمْ 

su da matayensu. 

 [17] احْشُرُوا الَّذِينَ ظَلَمُوا وَأزْوَاجَهُمْ 

ku tara wadanda suka yi zalunci da abokan hadinsu.

إلَى مَا مَتَّعْنَا بِهِ أزْوَاجاً مِنْهُم[18]   

ya zuwa abin da muka jiyar dasu dadi nau'i nau'i daga garesu.

سُبْحَانَ الَّذِي خَلَقَ الأزْوَاجَ[19] 

tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci nau'i nau'i.

وَمِنْ كُلِّ شَيْء خَلَقْنَا زَوْجَيْنِ[20]   

daga dukkanin wani abu mun halicci nau'uka biyu.

saboda haka Allah madaukaki shi kadai ne bai da abokin cudanya sannan dukkanin halittun da suke duniya nau'uka ne saboda suna da kishiya ko akwai wanda ke kamanceceniya dasu da cudanya ba zasu gushe da cudanya ta wani fuska ba. Abin da ya sa mu kawo nau'uka don ya zama tunatarwa da cewa dukkanin wani abu ko da kuwa bai da abin da ke kishiyantarsa da kamanceccniya da shi to bai kubuta daga daga jauhari da aradi da wadancan nau'uka biyu cikin fadinsa:

أزْوَاجاً مِنْ نَبَات شَتَّى[21]

nau'i nau'i daga tsirrai daban-daban..

ma'ana nau'o'i masu kamanceceniya da juna , haka cikin fadinsa:

مِنْ كُلِّ زَوْج كَرِيم[22]

   daga dukkanin nau'i mai karamci

[23]  ثَمَانِيَةَ أزْوَاج 

nau'o'i guda takwas.

وَكُـنتُمْ أزْوَاجاً ثَلاثَة[24] 

  ( kuma kun kasance nau'i uku )

 ai abokanan cudanya uku sune wanda Allah ya fassara su cikin fadinsa :

وَإذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْ[25] 

 (kuma idan rayuka aka cudanya su da jikkunansu )

Ance an cudanya kowa da tare da wadanda suka yiwa biyayya ko dai wuta ko aljanna, misalin fadinsa madaukaki:

احْشُرُوا الَّذِينَ ظَلَمُوا وَأزْوَاجَهُم[26]

Ku tara wadanda suka yi zalunci da abokanan cudanyansu   

 saboda kwanne irin abu cikin duniyar dabi'a bai gushewa daga nau'i  dokar auratayya ko kuma ace nau'antaka  zartacciya ce kan duniyar dabi'a .

 

 

 

 

 

 

 

 

 [1] Shu'ara:7

[2] Hajji:5

[3] Azzariyat:49

[4] Annajajamu:45

[5] Yasin:36

[6] Annahli:72

[7] Rum:21

[8] Fadir:11

[9] Shura:11

[10] A'araf:189

[11] Zumar:6

[12] Nisa'i:1

 1 mufradat ragib: sh 230

[14] Alkiyamat:39

[15] Bakara:35

[16] Yasin:56

[17] Assafat:22

[18] Alhijir:88

[19] Yasin:36

[20] Azzariyat:8

[21] Azzariyat:49

[22] Shu'ara:7

[23] An'am:8

[24] Waki'a:7

[25] Takwir:7

[26] Assafat:22