فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

AUREN SHARI'A

 

dan adam na da sha'awe sha'awe daban-daban daga cikin mafi bayyanarsu shi ne sha'awarsa ta jinsi, hakika mutum dauke ya ke da halittar sha'awa abin da ke nuna hakan shi ne sha'awar kusanta da saduwa ta jinsi hakika mutum namiji ko mace da dabi'arsa ta sha'awa da Allah ya halicce shi da ita ya na karkata zuwa ga jinsin da ya ke kishiyantakarsa ya yi yunkurin kusantarsa, sai dai ita kusantar

  wani sa'ilin tana kasancewa shar'antacciya wadda Allah ya halasta ya kuma yarda da ita ana kiranta da auren shari'a, akwai kuma kishiyar haka wadda ba halastacciya ba wadda ake kiranta da fajirci Allah ya haramta kamar misalin zina.

aure da ma'ana game gari shi ne tsantsar kusanta da jima'i wanda ke karkashin auratayya, sannan yana siffantuwa da hukunce hukuncen shari'a guda biyar: wajibi, haramun, mustahabbi, makaruhi,  halal, ko dai ya kasance wajibi idan ana tsoron afkawar fajirci da haramun  ko kuma haramun kamar aurar macen da  aurartaya haramta gareka misalin uwa kanwa da sauransu, ko kuma mustahabbi kamar auren a kankin kansa bisa zamani da yanayi da wurare kebantattu ta yadda za'a rinjayar da yinsa kan barinsa, ko ku

ma makaruhi ta yadda barinsa ya fi yinsa rinjaye da zama alheri, ko kuma daidaitar yinsa da barinsa ta yadda zai zama halal a irin wannan yanayi da lokaci.

aure da ke wajibi mustahabbi da halal shi ne ake kira da halastaccen aure a shari'a, ko dai ya kasance na dindin ko kayyadadde ko mallakar kuyanga, amma aurar muharrama  ana kiransa da haramtaccen aure, hakika ubangiji ya haramta ya yi alkawalin narkon azaba da tabewa ga wanda ya yi shi ranar alkiyama, kamar yadda ya wajabta haddi da rajamu jefewa anan duniya idan wanda ya aikata hakan ya kasance ya na da aure, ko kuma bulala dari idan bai da aure kamar yadda hakan ya zo dalla dalla cikin hukunce hukuncen fikihun muslunci.

auren shari'a na farko da ya fara kasancewa  tsakanin adamu uba ga dukkanin mutane da hauwa'u uwan garesu, kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja, cikin hakan akwai nuni zuwa ga falsafar aure  a jumlace  zuwa huduba da sadaki.

عن  أبي  عبد الله عليه السلام قال : ان الله  خلق آدم من طین  ثم ابتدع حواء فجعلها في موضع النقرة التي بين وركيه,ذلك لكي تكون المرأة تبعا للرجل,فقال آدم: یا رب ما هذا الحسن الذی آنسنی قربه والنظر الیه؟ فقال الله عز وجل: هذه امتی حواء,افتحبأن تكون معك تؤنسك وتحدثك,وتكون تبعا لأمرك؟فقال نعم يا رب ولك بذلك علي الحمد والشكر ما بقيت, فقال الله عز وجل: فاخلطبها الي,فاءنها أمتي,وقد تصلح لك ايضا زوجة للشهوة,وألقلى الله عليه الشهوة وقد علمه قبل ذلك المعرفة بكل شئ, فقال:یا رب فاءني أخطبها الیك, فما رضاك لذلك؟فقال الله عز وجل رضايا أن تعلمها معالم ديني, فقال: ذلك لك علي يا رب ان شئت ذلك لي, فقال الله قد شئت ذلك,وقد زوجتكها فضمها اليك[1]

an karbo daga baban abdullah (as)  ya na cewa : Allah mai girma da daukaka ya halicci adamu daga yunbu sannan ya kirkirar masa hauwa'u ya sanyata a mahalin tsakankanin matsugunansa domin ta zama biyayya ga da namiji, sai adamu ya ce: ya ubangiji wacce kyakkyawar halitta ce wannan da kusanatarta da kallonta ke debe mini haso? sai ubangiji ya ce: ya adamu baiwa ta ce hauwa'u, shin ko kana son ta kasance tare da kai ta dinga debe maka haso da dinga hira tare da kai ta  kasance mai biyayya ga umarninka ? sai adamu ya ce na'am ya ubangiji, ka cancanci yabo da godiya kan haka tsawon rayuwata, sai Allah madaukaki ya ce: nemi aurenta daga gareni hakika ita baiwa ta ce kuma ta dace da zama matarka don sha'awa, sai Allah ya sanya masa sha'awa kuma gabanin haka ya sanar da shi sanin dukkanin wani abu, sai adamu ya ce: ina neman aurenta daga gareka, meye yardarka kan haka, sai ubangiji ya ce: yarda ta ka sanar da ita ilimin addini na, sai adamu ya ce: idan kana son hakan to zanyi  sai ubangiji ya ce: na yarda  na aurar da ita gareka dauketa ta zama taka 1.

sannan aure na biyu ya kasance ga diyan adamu (as) ba kamar yadda majusawa (la) ke fadi cewa auren `yan'uwan juna uwa daya uba daya , bari dai ga yadda al'amarin ya zo cikin hadisi : cikin littafin manla yahduruhu fakihu:

رَوَى زُرَارَةُ «3» عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع أَنَّ آدَمَ ع وُلِدَ لَهُ شَيْثٌ            

 أَنَّ اسْمَهُ هِبَةُ اللَّهِ وَ هُوَ أَوَّلُ وَصِيٍّ أُوصِيَ إِلَيْهِ مِنَ الْآدَمِيِّينَ فِي الْأَرْضِ ثُمَّ وُلِدَ لَهُ بَعْد شَيْثٍ يَافِثُ فَلَمَّا أَدْرَكَا أَرَادَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ أَنْ يُبْلِغَ بِالنَّسْلِ مَا تَرَوْنَ وَ أَنْ يَكُونَ مَا قَدْ جَرَى بِهِ الْقَلَمُ مِنْ تَحْرِيمِ مَا حَرَّمَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ مِنَ الْأَخَوَاتِ عَلَى الْإِخْوَةِ أَنْزَلَ بَعْدَ الْعَصْرِ فِي يَوْمِ خَمِيسٍ حَوْرَاءَ مِنَ الْجَنَّةِ اسْمُهَا نَزْلَةُ فَأَمَرَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ آدَمَ أَنْ يُزَوِّجَهَا مِنْ شَيْثٍ فَزَوَّجَهَا مِنْهُ ثُمَّ أَنْزَلَ بَعْدَ الْعَصْرِ مِنَ الْغَدِ حَوْرَاءَ مِنَ الْجَنَّةِ وَ اسْمُهَا مُنْزَلَةُ فَأَمَرَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ آدَمَ أَنْ يُزَوِّجَهَا مِنْ يَافِثَ فَزَوَّجَهَا مِنْهُ فَوُلِدَ لِشَيْثٍ غُلَامٌ وَ وُلِدَ لِيَافِثَ جَارِيَةٌ فَأَمَرَ اللَّهُ

عَزَّ وَ جَلَّ آدَمَ حِينَ أَدْرَكَا أَنْ يُزَوِّجَ ابْنَةَ يَافِثَ مِنِ ابْنِ شَيْثٍ فَفَعَلَ فَوُلِدَ الصَّفْوَةُ مِنَ النَّبِيِّينَ وَ الْمُرْسَلِينَ مِنْ نَسْلِهِمَا وَ مَعَاذَ اللَّهِ أَنْ يَكُونَ ذَلِكَ عَلَى مَا قَالُوا مِنْ أَمْرِ الْإِخْوَةِ وَ الْأَخَوَاتِ[2]

  daga zuraratu daga baban abdullah (as) hakika adamu na da wani diya wanda ake kiransa shissu wanda hakikanin sunansa hibbatullah,shi ne wasiyyi na farko da aka yi masa wasiyya daga `ya`yan adamu,  bayan shissu an kara haifa ma adamu da mai suna yafis, yayin da ya girma sai ya nufi ya isar abin da zaku gani cikin tsatso, da kuma kasancewa cikin abin da alkalami ya bushe kansa cikin haramcin abin da Allah ya haramta daga auren `yan uwan juna uwa daya uba daya, bayan la'asar ranar alhamis ubangiji ya aiko da mace daga aljanna me suna nuzla ya umarci annabi adamu da ya aurar da ita ga dansa shissu, sannan washegari ya kara aiko da wata me suna manzilla ita ma ya umarci adamu ya aurar da ita ga yafis ya ko aura musu, sannan aka haifawa shissu da namiji shi kuma yafisu aka haifa masa mace, yayin da wadannan `ya`ya suka girma sai ya umarci adamu da ya aurar da `yar yafisu ga dan shissu sai  adamu (as) ya aikata hakan, to daga wannan tsatso ne aka haifi zababbu daga annabawa da manzanni, Allah ya kiyaye ace wai auren `yan uwan juna ne ya kasance kamar yadda majusawa suke fadi.

 daga manla yahadurul fakihu:

 ِّ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: إِنَّ اللَّهَ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى أَنْزَلَ عَلَى آدَمَ حَوْرَاءَ مِنَ الْجَنَّةِ فَزَوَّجَهَا أَحَدَ ابْنَيْهِ وَ تَزَوَّجَ الْآخَرُ ابْنَةَ الْجَانِّ فَمَا كَانَ فِي النَّاسِ مِنْ جَمَالٍ كَثِيرٍ أَوْ حُسْنِ خُلُقٍ فَهُوَ مِنَ الْحَوْرَاءِ وَ مَا كَانَ فِيهِمْ مِنْ سُوءِ خُلُقٍ فَهُوَ مِنِ ابْنَةِ الْجَانّ

ِ. da isnadinsa daga baban jafar (as) ya ce: Allah mai girma da daukaka ya aiko wa adamu mace daga aljanna sai ya aurar da ita ga daya daga `ya`yansa, dayan kuma ya auri  diyar aljanni, kyawun da ke kasancewa cikin mutane da kyautatar dabi'a to ya kasance daga wannan hurul inin ne da diyan adamu ya aura, sannan idan munanar dabi'a ne to daga `yar wannan aljanni da diyan adamu ya aura  ne.

zamu iya hada hadisan guda biyu sannan hada hadisi da daya hadisin don fitar da sakamako shi ya fi kyawu da cewa mun yi wurgi da su baki daya, Allah matsarkaki ya aurar da `ya`yan adamu karo biyu karon farko da hurul ini matayen aljanna karo na biyu kuma da hurul ini guda daya da aljana daya, ko kuma dai shi auren na farko ya kasance ga `ya`yaye biyu daga adam, sannan na biyun kuma ya kasance ga wasu `ya`yayen daban.

ِ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: ذَكَرْتُ لَهُ الْمَجُوسَ وَ أَنَّهُمْ يَقُولُونَ نِكَاحٌ كَنِكَاحِ وُلْدِ آدَمَ وَ إِنَّهُمْ يُحَاجُّونَّا بِذَلِكَ فَقَالَ أَمَّا أَنْتُمْ فَلَا يُحَاجُّونَكُمْ بِهِ لَمَّا أَدْرَكَ هِبَةُ اللَّهِ قَالَ آدَمُ يَا رَبِّ زَوِّجْ هِبَةَ اللَّهِ فَأَهْبَطَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ لَهُ حَوْرَاءَ فَوَلَدَتْ لَهُ أَرْبَعَةَ غِلْمَةٍ ثُمَّ رَفَعَهَا اللَّهُ فَلَمَّا أَدْرَكَ وُلْدُ هِبَةِ اللَّهِ قَالَ يَا رَبِّ زَوِّجْ وُلْدَ هِبَةِ اللَّهِ فَأَوْحَى اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ إِلَيْهِ أَنْ يَخْطُبَ إِلَى رَجُلٍ مِنَ الْجِنِّ وَ كَانَ مُسْلِماً أَرْبَعَ بَنَاتٍ لَهُ عَلَى وُلْدِ هِبَةِ اللَّهِ فَزَوَّجَهُنَّ فَمَا كَانَ مِنْ جَمَالٍ وَ حِلْمٍ فَمِنْ قِبَلِ الْحَوْرَاءِ وَ النُّبُوَّةِ وَ مَا كَانَ مِنْ سَفَهٍ أَوْ حِدَّةٍ فَمِنَ الْجِنّ

ِyazo cikin littafin alkafi mai daraja da isnadinsa daga baban jafar (as) na ce masa: majusawa na cewa aure kamar auren `ya`yayen adamu ne suna kafa hujja da hakan, sai ya ce: amma ku ba zasu kafa muku hujja da hakan ba, yayin da hibbatul ya girma sai adamu ya ce:ya ubangiji ina rokonka da ka aurarda hibbatullah, sai Allah ya sauko da hurul ini daga aljanna, sai ta haifa masa `ya`ya hudu sai Allah ya mayar da wannan hurul ini, yayin da dan hibbatul ya girma sai adamu ya kara rokon Allah da ya aurar da dan hibbatullah, sai Allah ya yi wahayi ga adamu da ya yi magana da wani mutum daga aljannu wanda ya kasance shi musulmi ne ya na da `ya`ya hudu mata sai ya aurar dasu ga `ya'yan hibbatullah, dukkanin abin da ya kasance daga kyawu da hakuri to daga fuskanin hurul ini nan ne da kuma jini annanbta, abin da ya kasance daga wauta da zafi da fusata to daga aljanni ne, domin cewa su aljannu an halicce su daga wuta, رُ cikinsu akwai zafi da fusata.

a abin da ya zo cikin alkur'ani  game da auren shari'a da sashen hukunce hukuncensa kamar haka cikin jumlar wadannan ayoyi :

وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ (5) إِلَّا عَلَى أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ (6) فَمَنِ ابْتَغَى وَرَاءَ ذَلِكَ فَأُولَئِكَ هُمُ الْعَادُونَ[3]

1-wadanda ke katange farjinsu face ga matayensu ko abin da damansu tamallaka to su ba ababen zargi bane dukkanin wanda ya nemi koma bayan haka to wadancan sune masu ketare haddi.

masu ketare haddin iyakokin ubangiji da wannan ake kafa hujja kan haramcin fitar da maniyi ta hanyar da ba shari'a ta tanade ba .

wani wajen kuma ya na cewa :

وَجَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَا لِيَسْكُنَ إِلَيَه[4]ا

2-ya sanya matarta daga gareta don samun natsuwa ya zuwa gareta.

وَأَنْكِحُوا الْأَيَامَى مِنْكُمْ وَالصَّالِحِينَ مِنْ عِبَادِكُمْ وَإِمَائِكُمْ إِنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ (32) وَلْيَسْتَعْفِفِ الَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّى يُغْنِيَهُمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِه[5]

3-ku auri gwauraye daga gareku da salihai daga bayinku da kuyangunku idan sun kasance fakirai talakawa to Allah zai wadata su daga falalarsa* hakika Allah ma yalwaci ne masani.

 gwauraye jam'i ne gwauruwa ai gwauruwar da bata da miji daga budurwa da bazawara haka lamarin yake kan namiji, sannan ayar tana magana ne da ga waliyyai da shugabanni (idan sun kasance talakawa ) ma'ana kada ku sanya talauci ya zamanto dallin da zai hana aure, (su kame ) abin da ya shahara cikin tafsirin wannan gaba shi ne danne sha'awa, kamar yadda annabi ya ke cewa: ya ku jam'ar samari dukkanin wanda ya samu dama da iko cikinku ya yi aure, wanda ko bai da iko kan haka to ya lazimci azumi, hakika azumi na rage kaifin sha'awa, ayar farko ta zo game da hana yin wurgi da watsi aure saboda haka babu karo da juna tsakaninta da wannan hadisi .

وَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعْ مِنْكُمْ طَوْلًا أَنْ يَنْكِحَ الْمُحْصَنَاتِ الْمُؤْمِنَاتِ فَمِنْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ مِنْ فَتَيَاتِكُمُ الْمُؤْمِنَاتِ وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِإِيمَانِكُمْ بَعْضُكُمْ مِنْ بَعْضٍ فَانْكِحُوهُنَّ بِإِذْنِ أَهْلِهِنَّ وَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ مُحْصَنَاتٍ غَيْرَ مُسَافِحَاتٍ وَلَا مُتَّخِذَاتِ أَخْدَانٍ فَإِذَا أُحْصِنَّ فَإِنْ أَتَيْنَ بِفَاحِشَةٍ فَعَلَيْهِنَّ نِصْفُ مَا عَلَى الْمُحْصَنَاتِ مِنَ الْعَذَابِ ذَلِكَ لِمَنْ خَشِيَ الْعَنَتَ مِنْكُمْ وَأَنْ تَصْبِرُوا خَيْرٌ لَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيم[6]

4-dukkanin wanda bai samu wadata da ikon aurar muminai to ya aura daga abin da hannayen damanku suka mallaka daga kuyangu muminai  Allah ne mafi sani daga imaninku sashenku daga sash, ku auresu da izinin iyayensu ku basu ladayensu bisa sanannen abu kamammu ba masu su zina ba da rikar abokanni,  idan aka aure su suka zo alfasha mabayyaniya  to akwai kansu rabin abin da ke kan `ya`ya daga azaba, wancan daga wanda ya ji tsoron wahala daga gareku, kuyi hakuri shi yafi zama alheri gareku , Allah me yawan gafara ne da rahama.

Allah ne mafi sani gameda imaninku )

ma'ana abin da kadai a ka kallafa muku yin  la'akari da shi shi ne zahirin mutum, saboda haka dukkanin mace ko namijin da ya bayyana muku imaninsa to kuyi masa hukunci da shi, aurensu ya halasta ko ba ababen tuhuma ba ne idan sun kasance munafukai (sashenku daga sashe )  dukkkanin bil adam ka da ku ki aurar kuyanga domin jinsi namiji da mace da imani sune ababen dubawa.

حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ مِنَ الرَّضَاعَةِ وَأُمَّهَاتُ نِسَائِكُمْ وَرَبَائِبُكُمُ اللَّاتِي فِي حُجُورِكُمْ مِنْ نِسَائِكُمُ اللَّاتِي دَخَلْتُمْ بِهِنَّ فَإِنْ لَمْ تَكُونُوا دَخَلْتُمْ بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ وَحَلَائِلُ أَبْنَائِكُمُ الَّذِينَ مِنْ أَصْلَابِكُمْ وَأَنْ تَجْمَعُوا بَيْنَ الْأُخْتَيْنِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَحِيمً وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ النِّسَاءِ إِلَّا مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ كِتَابَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَأُحِلَّ لَكُمْ مَا وَرَاءَ ذَلِكُمْ أَنْ تَبْتَغُوا بِأَمْوَالِكُمْ مُحْصِنِينَ غَيْرَ مُسَافِحِينَ[7]

5- (kada ku aura daga abin da  da iyayenku suka aura daga mata sai da abin da ya gabata hakika hakan alfasha ne da kyama ya munana ya zama hanya*an haramta maku uwayenku da `ya`yayenku da `yan'uwanku mata da goggwaninku da innoninku da `ya`yan dan'uwa da `ya`yan `yar'uwa  da uawayenku da suka shayar da ku nono da `yan'uwanku mata na shan nono  da uwayen matanku da agolanku wadanda su ke cikin dakin matayenku da ku ka sadu da su idan kuma ba ku kasance kun sadu da su to babu laifi kanku * da matayen `ya`yanku wadanda suke daga tsatsonku* kada ku hada tsakanin `yan'uwa biyu mata sai abin da ya gabata , hakika ubangiji mai yawan gafara da jin-kai da tsararru daga mata face dai abin da hannun damanku ya mallaka* ku kare littafin Allah an halasta  muku koma bayan haka, ku nema da dukiyoyinku kuna masu yin aure ba masu yin zina ba

(sai abin da ya gabata ) ma'ana a jahiliya hakika an yi muku uzuri cikin abin da ya rigaya ya faru, (tsararru daga mata ) ai matayen aure matukar suna cikin igiyar aure da wadanda suke halin idda (face abin da hannun damanku ta mallaka ) ai kuyangu da kuka mallaka ta hanyar saya ko kyauta ko gado ko yaki, ya na shiga cikinsa idan aure ya lalace tsakaninsu da abin da hannunku ya mallaka ya zama lazimi kowaccensu ta yi idda  (ku tsare littafin Allah ) ai littafin Allah farilla ne kanku.

ubangiji madaukaki na cewa :

وَلَا تُمْسِكُوا بِعِصَمِ الْكَوَافِر[8]

6-ka da ku riki auren mata kafirai

  وَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تُقْسِطُوا فِي الْيَتَامَى فَانْكِحُوا مَا طَابَ لَكُمْ مِنَ النِّسَاءِ مَثْنَى وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ذَلِكَ أَدْنَى أَلَّا تَعُولُو[9]ا

7-idan kun ji tsoron ba za ku iya adalci cikin marayu ba to ku auri abin da ya dadada gareku daga mata biyu biyu ko uku uku ko hudu, idan kun ji tsoron ba ku iya adalci to ku auri guda daya ko kuma abin da hannun damanku ta mallaka, hakan shi ya fi kusa daga da ku tsallake haddi.

:عن محمد بن الحسن، قال: سأل ابن أبي العوجاء هشام بن الحكم، فقال

أليس الله حكيما؟ قال: بلى، هو أحكم الحاكمين.

قال: فأخبرني عن قوله عز و جل: فَانْكِحُوا ما طابَ لَكُمْ مِنَ النِّساءِ مَثْنى‏ وَ ثُلاثَ وَ رُباعَ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَواحِدَةً أليس هذا فرض؟ قال: بلى.

قال: فأخبرني عن قوله عز و جل: وَ لَنْ تَسْتَطِيعُوا أَنْ تَعْدِلُوا بَيْنَ النِّساءِ وَ لَوْ حَرَصْتُمْ فَلا تَمِيلُوا كُلَّ الْمَيْلِ «1» أي حكيم يتكلم بهذا؟ فلم يكن عنده جواب، فرحل إلى المدينة، إلى أبي عبد الله (عليه السلام)، فقال: «يا هشام في غير وقت حج و لا عمرة؟» قال: نعم جعلت فداك، لأمر أهمني، إن ابن أبي العوجاء سألني عن مسألة لم يكن عندي فيها شي‏ء قال: «و ما هي»؟ قال: فأخبره بالقصة.

فقال له أبو عبد الله (عليه السلام): «أما قوله عز و جل: فَانْكِحُوا ما طابَ لَكُمْ مِنَ النِّساءِ مَثْنى‏ وَ ثُلاثَ وَ رُباعَ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَواحِدَةً يعني في النفقة، و أما قوله: وَ لَنْ تَسْتَطِيعُوا أَنْ تَعْدِلُوا بَيْنَ النِّساءِ وَ لَوْ حَرَصْتُمْ فَلا تَمِيلُوا كُلَّ الْمَيْلِ فَتَذَرُوها كَالْمُعَلَّقَةِ «2» يعني في المودة».

قال: فلما قدم عليه هشام بهذا الجواب و أخبره، قال: و الله، ما هذا من عندك.

8-alkafi da isnadinsa daga muhammad dan hassan ya ce:  dan auja'I ya tambayi hisham dan hakam ya ce masa: shin Allah ba mai hikima ba ne ? sai ya ce: na'am shi ne mafi hikimar masu hikima, sai ya bani labari da fadin Allah ( ku aura daga abin da ya dadada gare ku daga mata bibiyu,uku-uku, hudu-hudu, idan kun ji tsoron rashin iya tsyar da adalci tu ku tsaya ga daya.

baza ku taba iya yin adalci tsakanin mata ba ko da kuwa kunyi kwadayin hakan * kada ku karkata dukkanin karkata kuyi wurgi da ita kamar ratayayya. 

 wanne mai hikima ne zai dinga irin wannan maganar, sai  hikam ya kasa bashi amsa, take ya nufi madina wajen baban abdullah (as) sai imam ya ce masa mai ya kawo madina a wannan lokaci da ba na hajji ba ko umara, sai hisham ya ce: raina fansarka wani al'amari muhimmi ya kawo ni, hakika dan abul auja'i ya tambaye ni wata mas'ala wanda na gaza ba da amsa, sai imam  ya ce: mecece mas'ala ? sai ya bashi labari abin da ya faru,  imam (as) ya ce: masa amma fadinsa:

  ku aura daga abin da ya dadada gareku daga mata biyu biyu uku uku  hudu hudu idan kunji tsoron ba zaku iya adalci ba to ku auri guda daya, ayar tana magana ne kan ciyarwa, amma fadinsa ( baza ku taba iya adalci tsakanin mata ba koda kunyi kwadayin hakan kada ku karkata dukkanin karkata ku barta kamar ratayayya.

ma'ana cikin soyayya, sai ya ce: yayin da hisham ya komawa dan abul auja'i da wannan jawabi ya bashi labari sai abul auja'ai ya ce : wallahi wannan jawabin ba daga gareka ya ke ba.[10]

sannan gina iyali na kammala kadai kan tsuhen auren mai asali :

 [11]وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُمْ مِنْ أَنْفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِتَسْكُنُوا إِلَيْهَا

9-daga ayoyinsa ya halitta muku mata daga gareku don ku samu natsuwa zuwa garesu )

hadafi na farko da asasi kan aure shi ne samun natsuwa wanda da sannu zai haifar da kyakkyawan sakamako cikin `ya`ya da ma`aurata,  ma fi muhimmanci sinadarin samun gamsuwa  da amfana da wannan natsuwa shi ne zaman lafiyar gida wanda ke samuwa ta dalilin kaunar juna da tausayi wanda Allah ya sanya shi cikin halittar dan adam.

 وَجَعَلَ بَيْنَكُمْ مَوَدَّةً وَرَحْمَة[12]

ya sanya kauna da rahama

 sai dai tare da haka ya umarci mutum da ya motsa don kar ya zama (jabar) tilastawa ya yi kira ya zuwa kayakkayawar mu'amala cikin fadinsa:

وَجَعَلَ بَـيْنَكُمْ مَوَدَّةً وَرَحْمَة[13]   

10-kuyi musu mu'amala da kyautatawa. 

sannan a na ladabtar  dukkanin mara da'a daga cikinsu maza da mata, ba'a yarda da wulankanta mace ba don tana mace , bari madai mace dai-dai take da namiji cikin tarbiyya da koyarwa fagen ladabi daraja da karamci.

وَالْمُؤْمِنُونَ وَالْمُؤْمِنَاتُ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ يَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنْكَر[14]

11-muminai maza da mata sashensu masoyan sashe suna umarni da kyakkyawa da hani da mummuna.

mace na da sako cikin muslunci ta hanyar rikonta ga hijabi da muslunci, sannan alakar namiji da mace ba ta halasta face cikin wasu wurare kayyadaddu iyakantattu da muslunci ya tsara,  wannan alaka ba ta kasance saki ba kaidi kan nau'in mutum,   ta kasance kayyadaddiya iyakantacciya da wasu kaidodi da shar'ia ta farlanta su   tana sassabawa cikin jumlacewarta da faifaicewa da sassabawar zamani da al'umma.

 [1] Was'ilul shi'a m 20 sh 24

[2] Manla yahduruhu alfakihu m 3 sh 381

[3] Almuminun:7

[4] A'araf:189

[5] Nurr:32-33

[6]Nisa'i:25

[7] Nisa'i: 22-24

[8] Mumtahana;10

[9] NISA'I:3

[10]Kitabul alwafi m 12 sh 792

[11] Rum:21

[12] Rum:21

[13] Nisa'i:19

[14] Tauba:71