فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

KASHE-KASHEN AURE

 

 daga mafi muhimmancin wadancan kaidodi kashe kashen da ya halasta cikinsa, da wadanda basu halasta tsakaninsu da adadin mataye da mazaje  da abin da shi aure ke kammala da hakkoki da wajibai wadanda aka dora kan wuyan ma'aurata cikin wannan alakar ta aure da shari'a da al'ada.

fagen wannan kashe-kashe ya na sabawa da sabawar jama'a, daga kaidodi akwai abin da ke komawa ya zuwa sabani cikin addini, misali cikin al'ummomi musulmi bai halasta wanda ba musulmi ya auri musulma ba ko da kuwa ya kasance daga ahlul kitabi kamar yadda bai halasta musulmi ya auri wadda ba musulma ba ko da kuwa ahlul kitabi ce, haka bai halasta ya auri mushrika mai bautar gumki kamar yadda ya zo cikin fadin Allah:

وَلا تَنكِحُوا المُشْرِكَاتِ حَتَّى يُؤْمِنَّ وَلأمَةٌ مُؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِكَة وَلَوْ أعْجَبَتْكُمْ وَلا تُنكِحُوا المُشْرِكِينَ حَتَّى يُؤْمِنُوا وَ لَعَبْدٌ مُؤْمِنٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِك وَلَوْ  أعْجَبَكُمْ [1]

12-kada ku auri mata mushrikai har sai sun yi imani  kuyanga mumina ta fi alheri daga mushrika ko da kuwa wannan mushrika ta kayatar da ku  kada ku auri mazaje mushrikai har sai sun yi imani  lalle bawa mumini shi ne mafi alheri daga bawa mushriki ko da kuwa ya kayatar da ku.

daga kaidodi akwai  wanda ke komawa ga jinsi mutane, misali wajen yahudawa zamanin da ya shude sun kasance suna haramta aure tsakaninsu da kan'aniyawa saboda su yahudawa suna ganin kansu matsayin zababbun Allah, kuma suna la'akari da kan'aniyawa a matsayin kaskantattun halittun Allah don su samu damar mayar da su bayi, kuma dukkanin mutane  al'amarinsu ya kasance haka bai inganta su gurbata banu isra'ila da surutaka ba, kuma sun kasance suna raya cewa wannan kaskanci ya samo asali daga addu'ar da annabi nuhu (as) ya yi kan dansa hamu da tsatsonsa, hakika ya zo cikin سفر التكوين cewa nuhu ya sha giyar inibi wanda shi da kansa ya dasa bishiyar wannan inibi bayan ruwan dufana ba tare da ya san cewa wannan inibi yana sanya maye ba, sai ya fita daga hayyacinsa tsiraicinsa ya bayyana fili, yayin da dansa hamu ya ga tsiraicinsa sai ya yi masa isgili ya dauki labarin ya kaiwa ragowar `yan'uwansa samu da yafisu sai dai cewa su sun fishi ladabi da tarbiyya  sai suka dauki kyalle suka dinga tattakawa da baya da baya don kada idonsu ya kai  ga ganin tsaraicin mahaifinsu suka lullube shi da wannan kyalle suka suturce shi, yayin da nuhu ya dawo cikin hayyacinsa ya ji labarin matakin da `ya`yansa suka dauka kansa sai ya tsinewa kan'an dan hamu da `ya`yansa ya yi addu'a da Allah ya sanya su bayi ga samu da yafisu.

kamar yadda aure tsakanin girkawa da ragowar kabilu wanda suke kiransu  da barbar ya ke  cikin wannan zamani, haka al'amarin ya ke cikin rumawa lamarin ya kai ga daya  cikin sarakunansu ya sanya doka wanda ya kai ga ukubar hukuncin kisa  ga dukkanin ba rumen da ya auri wadda ba ba rumiya ba, haka larabawan jahiliya suka kasance basa aurar da balarabiya ga wanda ba balarabe ba, kai lamarin ya kai ga  kabila ba ta aurar wanda ba dan kabilarta ba saboda suna ganin kansu mafi daraja daga waninsu,  cikin ba'arin mazhabobin muslunci kamar mazhabar abu hanifa na ganin wanda ba balarabe bai da ce da auren balarabiya ba haka ma wanda ba bakuraishe bai cancanci auren bakuraishiya ba.

haka ma cikin amerika da kasashene turai sun kasance suna haramtawa ba'amerike ya auri wadda ba ba'amerikiya ba,  haramatawa bakar fata ya auri farar fata, haka al'amarin ya ke cikin kasar jamus.

daga kaidoji akwai wanda ke komawa ga sabani  matsayi, misali a kasar indiya auratayya bai inganta tsakanin barahima da ragowa mutane musammam ma kason da suke ganinsu kaskantattu, hakan na komawa ga sabanin jinsi, kamar yadda ya kasance cikin rumawa suma sun zama suna haramta auren `ya`yan manya da ragowar mutane, a mazhabar hanafiya wanda danginsa suke kaskantu bai cancanci auren `yar babban dangi ba, haka mai karamar sana'a kamar wanzami da dan shara bai cancanci `yar wanda suke da babbar sana'a ba kamar manyan `yan kasuwa a kasar masar bai gushe ba dangin dake ganin kansu babban dangi suna ganin abin kunyane su auri `yar kananan dangi duk yadda suka kai da dukiya da matsayi cikin jama'a.

daga kaidoji akwai wanda ke komawa ga kusanci babu wata jama'a da suka kubuta daga gare shi, akwai kashe kashe daga muharramai kamar yadda ya ke a muslunci, kamar uwa da `ya da `yar'uwa da `yar'uwan uba da na uwa, ma'ana ya na haramta ga mutum ya auri asalinsa komai nisansu, kamar uwa, kaka, haka idan sun sauko kasa kamar diya da jika, reshen mahaifinsa can kasa  kamar `yar'uwa da `ya`yan `yar uwa da `ya`yan `yar'uwarsa da dan uwansa, da reshensa da ke kai tsaye ga kakanninsa kamar goggo da goggon babansa da goggon kakansa daga babansa da babarsa duk yadda ya kai da yin nisansu, kamar yadda kur'ani ya yi ishara:

[2] حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ

 an haramta muku uwayenku da `ya`yayenku da `yan'uwanku  mata da goggoniku da innoninku da `ya`yan dan'uwa da `yar dan'uwa.

daga kaidodi akwai wanda ke komawa ga surutaka, dukkanin wanda ya aura daga wani dangi zai wayi gari daya daga cikin wannan  dangi sai shari'a ta haramta hada mata `yan'uwan juna daga wannan dangi cikin aure lokaci guda, kamar yadda ya haramta  aurar mahaifiyar matarsa haka ma ya haramta mahaifinsa ya auri matarsa, saboda haka asalin matarsa ya na haramta gare shi duk yadda ya kai ga nisa da reshenta duk yadda ya kai ga saukowa kasa, da matan mahaifinsa da kakanninsa  duk nisansu, ga wannan kashi ne ubangiji ke cewa:

وَلَا تَنْكِحُوا مَا نَكَحَ آبَاؤُكُمْ مِنَ النِّسَاءِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَمَقْتا وساء سبيلا[3]

14-kada ku aura daga abin da babanniku suka aura daga mata sai dai abin da ya gabata , hakika hakan alfasha ne da kyama tafarki ya munana.

daga kaidodi akwai wanda ke komawa ga shan nono, kamar uwa daga shayarwa da asalinta duk yadda suka kai ga nesa, da matar da ku ka sha nono tare, da `ya`yanta duk yadda suka kai ga saukowa kasa da goggo da inna da kuka hadu ta hanyar shan nono, da uwar wadda ta shayar da nono, wannan hukunci na haramci ya na gudana da zarar an kulla aure da macen  da makamancin haka kamar yadda ya zo cikin littafan fikihu.

 [1] Bakara:221

[2]Nisa'i:23

[3] Nisa'i:22-23