فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA

 

dukkanin wani aiki da dukkanin wani abu mai yiwuwa yana da farko da karshe, kamar yadda ya kasance ga dukkanin aikin mutum akwai abin da ke sanya shi yi da hadafinsa kan aikin, dukkanin wanda ya ke son yin aure, to babu makawa akwai dalilan  kankin kansa da tunani da  ruhi da suka tunkuda shi ga yin hakan, haka ba'a rasa tsarkakkun dalilansa kan haka domin kada aikinsa ya zama wargi musammam abu mai muhimmanci irin aure ga samari matasa da wanda ye nufin yin aure da samar da iyali da sallamawa hukuncin rayuwa.

idan muna son sanin wannan dalilai  da sakamako da hadafin cikin mas'alar aure daga mahangar addinin muslunci, kadai hakan na kasancewa idan mun kalli maudu'in daga tushen shari'ar muslunci da tushen fahimtarsa da ilimansa, ma'ana kur'ani mai karamci da sunna mai daraja ma'ana fadi ma'asumi aiki da abin da ya yanke shawara kai.

gabanin bayanin haka babu laifi muyi ishara zuwa ga asalin halittar mutum da kuma cewa hadafi kansa shi ne ya kiyaye amana, kuma ya kasance mabayyana ga sunayen Allah kyawawa da siffarsa madaukakiya, sannan yayi tajalli cikin ilimin ubangiji don ya zama halifan Allah a ban kasa, kamar yadda muka ba da labarin hakan cikin kur'ani daga fadinsa mai girma:

وَإِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلَائِكَةِ إِنِّي جَاعِلٌ فِي الْأَرْضِ خَلِيفَةً قَالُوا أَتَجْعَلُ فِيهَا مَنْ يُفْسِدُ فِيهَا وَيَسْفِكُ الدِّمَاءَ وَنَحْنُ نُسَبِّحُ بِحَمْدِكَ وَنُقَدِّسُ لَكَ قَالَ إِنِّي أَعْلَمُ مَا لَا تَعْلَمُونَ[1]

 yayin da ubangijinka ya ce da mala'iku lalle ni zan sanya halifa a cikin kasa  sai suka ce yanzu zaka sanya cikinta wanda zai yi barna cikinta kuma mu muna tasbihi tare da gode maka da tsarkake ka, sai ya ce musu lalle ni nasan abin da baku sani ba. 

إِنَّا عَرَضْنَا الْأَمَانَةَ عَلَى السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَالْجِبَالِ فَأَبَيْنَ أَنْ يَحْمِلْنَهَا وَأَشْفَقْنَ مِنْهَا وَحَمَلَهَا الْإِنْسَانُ إِنَّهُ كَانَ ظَلُومًا جَهُول[2]

اlalle mu mun bijiro da amana ga sammai da kasa da duwatsu sai suka ki daukarta kuma suka ji tsoro  daga gareta sai mutum ya dauketa  hakika shi mai yawan zalunci da yawan jahilci ne.

  أَلَمْ تَرَوْا أَنَّ اللَّهَ سَخَّرَ لَكُمْ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَأَسْبَغَ عَلَيْكُمْ نِعَمَهُ ظَاهِرَةً وَبَاطِنَة[3]

shin baku ga cewa Allah ya hore muku abin da ke cikin  sammai  da kasa ya yalwata ni'imarsa kanku ta zahiri da badini.

وَلَقَدْ كَرَّمْنَا بَنِي آدَمَ وَحَمَلْنَاهُمْ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ وَرَزَقْنَاهُمْ مِنَ الطَّيِّبَاتِ وَفَضَّلْنَاهُمْ عَلَى كَثِيرٍ مِمَّنْ خَلَقْنَا تَفْضِيلً[4]ا

hakika mun karrama bil adama mun dauke su kan kasa da teku muka azurta shi daga abubuwa dadada muka fifita shi kan da yawa daga abin da muka halitta fifitawa.

وَعَلَّمَ آدَمَ الْأَسْمَاءَ كُلَّهَا ثُمَّ عَرَضَهُمْ عَلَى الْمَلَائِكَةِ فَقَالَ أَنْبِئُونِي بِأَسْمَاءِ هَؤُلَاءِ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ (31) قَالُوا سُبْحَانَكَ لَا عِلْمَ لَنَا إِلَّا مَا عَلَّمْتَنَا إِنَّكَ أَنْتَ الْعَلِيمُ الْحَكِيمُ (32) قَالَ يَا آدَمُ أَنْبِئْهُمْ بِأَسْمَائِهِمْ فَلَمَّا أَنْبَأَهُمْ بِأَسْمَائِهِمْ قَالَ أَلَمْ أَقُلْ لَكُمْ إِنِّي أَعْلَمُ غَيْبَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَأَعْلَمُ مَا تُبْدُونَ وَمَا كُنْتُمْ تَكْتُمُونَ[5]

 ya sanar da adamu sunaye dukkaninsu sannan ya bijirosu kan mala'iku ya ce ku bani labari da sunayensu idan kun kasance masu gaskiya , sai suka ce tsarki ya tabbatar maka babu sani gare mu face abin da ka sanar damu hakika kai ne masani mai hikima  sai ya ce ya adamu ka basu labari yayin da ya basu labari sunayensu  sai ya ce ashe ban gaya muku lalle ni nasan gaibun sammai da kasa  na san abin da kuke bayyanawa da boyewa.[6]

الَّذِي أَحْسَنَ كُلَّ شَيْءٍ خَلَقَهُ وَبَدَأَ خَلْقَ الْإِنْسَانِ مِنْ طِينٍ (7) ثُمَّ جَعَلَ نَسْلَهُ مِنْ سُلَالَةٍ مِنْ مَاءٍ مَهِينٍ (8) ثُمَّ سَوَّاهُ وَنَفَخَ فِيهِ مِنْ رُوحِهِ وَجَعَلَ لَكُمُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ وَالْأَفْئِدَةَ قَلِيلًا مَا تَشْكُرُونَ[7]

  shi ne wanda ya kyawunta halitta kowanne abu ya fara da halitta mutum daga yunbu  sannan ya sanya `ya`yansa daga wani asali na ruwa wulakantacce  sannan ya daidaita shi ya yi hura cikinsa daga ruhinsa ya sanya muku ji da ganunuwa da zukata , godiyarku tayi kadan.

لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنْسَانَ فِي أَحْسَنِ تَقْويم[8]

ِlalle mun halicci bil adam bisa mafi kyawun tsayuwa.

وَلَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنْسَانَ مِنْ سُلَالَةٍ مِنْ طِينٍ (12) ثُمَّ جَعَلْنَاهُ نُطْفَةً فِي قَرَارٍ مَكِينٍ (13) ثُمَّ خَلَقْنَا النُّطْفَةَ عَلَقَةً فَخَلَقْنَا الْعَلَقَةَ مُضْغَةً فَخَلَقْنَا الْمُضْغَةَ عِظَامًا فَكَسَوْنَا الْعِظَامَ لَحْمًا ثُمَّ أَنْشَأْنَاهُ خَلْقًا آخَرَ فَتَبَارَكَ اللَّهُ أَحْسَنُ الْخَالِقِين[9]

 lalle mun halicci mutum daga tsantsa daga yunbu  sannan muka sanya shi digon maniyyi cikin matabbbata natsattsiya  sannan kuma muka halicce shi gudan jini sannan muka halitta gudan jinin tsoka  sannan muka halicci tsokar ta zama kasusuwa sannan muka lullube kasusuwan da nama sannan mu kage wata halitta albarkun sun bayyana mafi kyawun masu halitta.

 Allah matsarkaki ya yi halitta halitta mai kyawu.

الَّذِي أَحْسَنَ كُلَّ شَيْءٍ خَلَقَه[10]

ُshi ne wanda ya kyawuntawa komai halittarsa.

bai ya bi kansa cikin abin da ya halitta ba face kan halittar mutum

   فَتَبَارَكَ اللَّهُ أَحْسَنُ الْخَالِقِين[11]

 albarku sun bayyana Allah mafi kyawun halitta masu halitta.

hakan idan ya yi nuni ga wani abu to ya na nuni ga girman mutum da karamci hakika shi ya hore musu komai don su dauki amanar ubangiji

وَصَوَّرَكُمْ فَأَحْسَنَ صُوَرَكُم[12]

 ya surantaku ya kyawunta surarku.

 falsafar rayuwa da sirrin halitta shi ne ilimi, sannan ribarsa tsoron Allah, Allah matsarkaki ya na cewa:

[13] وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ

  ban halicci mutum da aljannu sai don bautata.

a dunkule sirrin rayuwa da falsafar mutumtaka shi ne makasudin kamala da kammaluwa shi ne kowanne abu ya kai ga kamalarsa da ya ke nema, ma'ana ya kai ga narkewa cikin Allah matsarkaki ya zama madubi ga sunanyensa kyawawa da siffofinsa madaukaka, kamalar mutum na da dalilai na shari'a da dabi'a, kamar yadda suka zo cikin nassosin addini da hujjojin hankali, daga mafi muhimmanci dalilai shi ne aure, hakika anyi bayanin aure  da bayanai daban-daban daga cikinsu: aure wata alaka ce da ke tabbatu da da kullawa tsakanin miji da mata ko kuma masu wakiltarsu wanda ta hanyarsa jindadi juna ke halasta a shari'ance da hukuncin lafiyayyar dabi'a, daga baya kuma wajibai da hakkoki su biyo su hau kan mijin da matar, zuriya ta bubbugo daga gare shi tsakanin miji da matar da wanda ke danganewa da su ta hanyar nasaba da surutaka.a wani fadin kuma shi ne cewa shi aure wata alaka ce ta shari'a tsakanin namiji da mace da ake sunnanta don tsare nau'in mutum da abin da ke biyo bayansa na daga tsarin zamantakewa.

wasu kuma sun ce cikinsa akwai samun kwanciyar hankali  da karfafarta kan ibada, cikin debe haso da mata akwai hutu da gushewar bakin ciki da samun sauki cikin zuciya.

wasu kuma sunce : shi aure garkuwa ne da ke katange mutum daga hadare hadaren dabi'a da tunkude tarkon sha'awa da kiyaye farji da mutunci da katange mutum daga fadawa halaka da fajirci da alfasha .kalmar aure a larabci : ma'anarta saduwa a wani fadin kuma tana da ma'ana kullawa  wasu kuma sunce tana da ma'ana da tayi tarayya cikinsu biyun.

a shari'ance  shi ne cewa : kullawa ce ta lafazi da ke mallaka saduwa, na daga majazi na lugga ta babin kiran sababi da sunan musabbab cikinsa akwai falala mai tarin yawa.

saboda haka aure wata alaka ce ta shari'a da kulla alaka tsakanin namiji da mace,  kuma ta hanyarsa ake kiyaye wanzuwar nau'in dan adam, sannan dukkanin shari'o'in sama sun halasta shi,  muslunci ya karfafa shi  ubangiji ya mustahabbantar da shi ya na da matsayi muhimmi cikin tsarin zamantakewa, ubangiji da kansa ya rungumi lura da kyaye shi da cikakkiyar kulawa ta yanda ya fitar da ka'idojinsa dalla-dalla  ya iyakance hukunce hukuncensa tun da farko, ya tabbatar da jin dadin juna tsakanin ma'aurata.

 sannan ya kara jebanta masa kulawa ta musammam ya kuma kewaye shi da muhimmantarwa daga farko har ya zuwa ga tikewa ga kabari ko waninsa, ubangiji bai baiwa mutane damar yin yanda sukaga dama ba cikinsa ta hanyar sanya dukkanin tsarin da hukunci da dokoki da asalai da zukatansu keso, bari ma dai ubangiji ya jebance shi saboda falala daga gare shi da tausayin bayinsa, sai ya sanya masa asalai da tsare-tsare da hukunce hukunce  saboda ya san cewa bayinsa kasassu ne wajen iya samar masa da tsarin daya dace da shi wanda karkarfan tsarin zamantakewa zai ginu kai  da rauni bai iyu kutsawa cikinsa, don aure ya rabauta da irin wannan kulawa tsarkakka wanda ke sanyawa ma'aurata su ji cewa su suna da dangantaka tsarkakka da addini ya tattaro shi da tsarkinsa cikin kowacce kiftawar ido cikin marhalolinsa,  kowanne dayansu ya samu natsuwa ya zuwa abokinsa cikin zabi da yarda, a dabbaka hukunce hukuncensa cikin cikin kwanciyar hankali da hutun zuciya.

وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُمْ مِنْ أَنْفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُمْ مَوَدَّةً وَرَحْمَةً إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَاتٍ لِقَوْمٍ يَتَفَكَّرُون[14]

 daga ayoyinsa ya halitta muku daga gareku mataye don ku samu natsuwa ya kuma sanya kauna da jin kai tsakaninku  lalle ne cikin wadancananka akwai ayoyin ga wanda suke tunani.

kamar yadda cikin hadisi daga annabi mafi girma (saw):

عن النبيّ الأعظم محمّد (صلى الله عليه وآله)  : ما استفاد امرؤٌ فائدة بعد الإسلام أفضل من زوجة مسلمة ، تسرّه إذا نظر إليها ، وتطيعه إذا أمرها ، وتحفظه إذا غاب عنها في نفسها وماله[15]ا

 ( mutum bai ta ba fa'idantuwa da wata fa'ida ba bayan muslunci fiye da mata musulma wadda ke faranta masa rai idan ya kalleta, tana masa biyayya idan ya umarce ta, tana kare mutuncinsa cikin kanta da dukiyarsa idan ya faku daga barinta )

a wata riwayar kuma (dukkanin wanda ya yi aure to ya tabbatar da rabin addininsa sai ya ji tsoron Allah cikin daya rabin da ya rage .

 [1] Bakara:30

[2] Ahzaba:72

[3] Lukman:20

[4] Isara'i:70

[5] Bakara: 31-33

[6] Bakara:31-33

[7] Sajada:7-9

[8] Attini:4

[9] Almuminun:12-14

[10] Sajada:7

[11] Almuminun:14

[12] Gafir:64

[13] Azzariyat:56

[14] Rum:21

[15] Kanzul  irfan sayyuri m 3 sh 4