فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE

AURE                          

Allah madaukakin sarki na cewa : 

يُرِيدُ اللَّهُ أَنْ يُخَفِّفَ عَنْكُمْ وَخُلِقَ الْإِنْسَانُ ضَعِيفً[1]

 Allah na nufin saukaka muku an halicci mutum cikin rauni.

خُلِقَ الْإِنْسَانُ مِنْ عَجَل[2]

an halicci mutum daga gaggawa

إِنَّ الْإِنْسَانَ خُلِقَ هَلُوعًا (19) إِذَا مَسَّهُ الشَّرُّ جَزُوعًا (20) وَإِذَا مَسَّهُ الْخَيْرُ مَنُوعً[3]ا

ا  lalle mutum an halicci mai tsananin kwadayi  idan sharri ya sameshi sai ya kasance mai yawan kuka da raki  idan alheri ya same shi sai ya kasance mai yawan rowa.

وَإِذَا مَسَّكُمُ الضُّرُّ فِي الْبَحْرِ ضَلَّ مَنْ تَدْعُونَ إِلَّا إِيَّاهُ فَلَمَّا نَجَّاكُمْ إِلَى الْبَرِّ أَعْرَضْتُمْ وَكَانَ الْإِنْسَانُ كَفُورً[4]ا

idan cutarwa ta sameku ciki teku sai ku manta da abin da ku ke kira face shi sa'ilin da ya tserarta da ku ya zuwa kan kasa  sai kuka bijire mutum ya kasance mai yawan butulci.

فَإِذَا رَكِبُوا فِي الْفُلْكِ دَعَوُا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ فَلَمَّا نَجَّاهُمْ إِلَى الْبَرِّ إِذَا هُمْ يُشْرِكُون[5]

yayin da suka hau cikin jirgi suka kira suna masu tsarkake addini yayin da ya tseratar da shi ya zuwa kan kasa sai gashi suna shirka.

إِذَا أَذَقْنَا الْإِنْسَانَ مِنَّا رَحْمَةً فَرِحَ بِهَا وَإِنْ تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ فَإِنَّ الْإِنْسَانَ كَفُور[6] 

 

idan muka dandanawa mutum rahama daga garemu sai yayi farin ciki da ita idan kuma wani mai muni ya samesu bisa abin da hannuwansu suka gabatar hakika mutum mai tsananin kafircine. 

قُتِلَ الْإِنْسَانُ مَا أَكْفَرَه[7]

an tsinema mutun kafiri me ya yi kafircinsa.  

إِنَّ الْإِنْسَانَ لِرَبِّهِ لَكَنُود وَإِنَّهُ عَلَى ذَلِكَ لَشَهِيد[8]

lalle  mutum mai tsananin butulci ne ga ubangijinsa  kuma shi mai shaida ne kan haka.

mutum ya kasance mafi jayayya cikin kowanne abubuwa.

إنَّا عَرَضْنَا الأمَانَةَ عَلَى السَّمَوَاتِ وَالأرْضِ وَالجِبَالِ فَأ بَـيْنَ أنْ يَحْمِلْنَهَا وَأشْفَقْنَ مِنْهَا وَحَمَلَهَا الإنْسَانُ إنَّهُ كَانَ ظَلُوماً جَهُولا[9]

Lalle ne mu mun bijiro da amana ga ahalin sama da kasa da duwatsu duka suka ki yarda da su dauka suka tsorata amma sai mutum ya dauka lalle shi mai yawan zaluntar kansa ne mai yawan jahilci.

وَكَانَ الإنسَانُ أكْثَرَ شَيْء جَدَلا[10]

Mutum ya kasance mafi yawan jayayya daga kowanne abu.   

misalin wadannan ayoyi masu karamci na ishara da kan hakikanin mutum bisa la'akari kansa mai yawan umarni da mummuna, hakika shi kamar yadda ya ke dauke da hankali wanda da shi ne zai kai ga ubangijinsa, hakika shi mai gogayya ya zuwa gare shi ne kuma tabbas zai gana da ubangijinsa ya zuwa mahallin tsakankanin baka ko mafi kusa daga haka, gare shi ne al'amurra ke komawa, makoma na gare shi hakika dukkanin mu ya zuwa gare shi zamu koma, mutum da haskakakken hankalinsa ke tafiya kan hanyar Allah da siradinsa, sai dai cewa cikinsa an halicci rai mai umarni da mummuna don ya zama ya tattaro tsakanin kishiyoyin juna, ko dai yabi son rai sai zuciyarsa ta zama kamar dutsi ko kuma tafi ma dutsi kekashewa, ya kasance kamar dabbobi ko mafi batan hanya daga dabbobi, ko kuma ya filfila cikin samaniyar darajoji cikin matsugunin gaskiya wuri sarki mai kudura mala'iku suyi masa hidima da matayen aljanna.

kadai hakan na kasancewa da jin kan ubangiji, abin nufa shi ne tsoron Allah me ya sanar da kai gameda tsoron Allah.

يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْسٍ وَاحِدَةٍ وَخَلَقَ مِنْهَا زَوْجَهَا وَبَثَّ مِنْهُمَا رِجَالًا كَثِيرًا وَنِسَاء[11]

  ya ku mutane kuji tsoron ubangiji wanda ya halicceku daga rai guda ya halicci daga gareta matarta ya kuma yada mazaje masu yawa da mata.

يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُمْ مِنْ ذَكَرٍ وَأُنْثَى وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوبًا وَقَبَائِلَ لِتَعَارَفُوا إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِير[12]

ٌya ku mutane hakika lalle ne mu mun hallicceku daga mace da namiji muka sanya ku al'ummu da kabilu don kusan juna hakika mafi karamcin cikinku wajen Allah shi ne mafi tsoronsa lalle ne Allah masani ne da kididdigawa.

yawancin zunubai daga gwaurantaka suke da galabar sha'awar jinsi, kan haka ne muka samu  nassosi addini da ke kwadaitar da samari kan yin aure da kuma cewa dukkanin wanda ya yi aure to ya tabbatar da rabin addininsa sai ya ji tsoron Allah cikin daya rabin.

 

عن الإمام الصادق (عليه السلام) ، قال  : جاء رجل إلى أبي فقال له  : هل لك زوجة  ؟ قال  : لا ، قال لا اُحبّ أنّ لي الدنيا وما فيها وأ نّي أبيت ليلة ليس لي زوجة ، قال  : ثمّ قال  : إنّ ركعتين يصلّيهما رجل متزوّج أفضل من رجل يقوم ليله ويصوم نهاره أعزباً ، ثمّ أعطاه أبي سبعة دنانير ، قال  : تزوّج بهذه ، وحدّثني بذلك سنة ثمان وتسعين ومائة ، ثمّ قال أبي  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : اتّخذوا الأهل فإنّه أرزق لكم[13]

1-an karbo daga sadik (as) ya ce : wani mutum ya zo wajen babana sai ya ce masa: shin kana da mata ?  sai ya ce: a'a, sai imam ya ce : ban san ace inada duniya da dukkanin abin da ke cikinta in kwanta dare daya alhalin banda mata, sannan ya kara da cewa: lalle raka'a biyu da mai aure  da ya yi tafi falala daga tsayuwar daren  gwauraye ya kuma kasance sun wayi gari cikin azumi, sannan babana ya bashi dinare 70 ya ce masa kaje kayi aure da wannan. Sannan babana ya a ce: manzon Allah(saw) y ace: kuyi aure lalle shi aure arzikine gareku.  dukkanin wanda bai  samu iko ba kan yin aure to ya zama wajibi kan malamai su samar masa da abin da zai yi aure daga asusun baitul mali  kamar yadda ya kasance shi aure na dada arziki.

قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : تزوّجوا فإنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله) كثيراً ما كان يقول  : من كان يحبّ أن يتّبع سنّتي فليتزوّج ، فإنّ من سنّتي التزويج ، واطلبوا الولد فإنّي اُكاثر بكم الاُمم غداً  

2-sarkin muminai aliyu dan abu dalib (as) na cewa : kuyi aure hakika manzon Allah ya kasance yana yawaita fadin cewa : dukkanin wanda ke son bin sunna ta to ya yi aure domin daga cikin sunna ta shi ne aure, ku nemi diya hakika zanyi alfahri daku ranar alkiyama.

عن الرضا (عليه السلام) ، قال  : إنّ امرأة سألت أبا جعفر (عليه السلام) فقالت  : أصلحك الله ، إنّي متبتّلة ، فقال لها  : وما التبتّل عندك  ؟ قالت  : لا اُريد التزويج أبداً ، قال  : ولِمَ  ؟ قالت  : ألتمس في ذلك الفضل ، فقال  : انصرفي فلو كان في ذلك فضل لكانت فاطمة (عليها السلام) أحقّ به منكِ ، إنّه ليس أحد يسبقها إلى الفضل[14]

3- an karbo daga imam rida (as) ya ce:wata mace ta tambayi baban jafar (as) tace Allah ye maka gyara lalle ni baiwar Allah ce mai yankewa kauna  daga kowa ya zuwa ga ubangiji, sai baban jafar ya ce mata me ye yankewar ki ? sai tace ni bana son aure har abada, sai ya ce: me yasa ? sai ta ce ina neman daraja da yin hakan, sai ya ce : tafi ki bamu waje da cikin hakan akwai daraja da fatima (as) tafi cancanta da aikata hakan daga gareki lalle babu wani mutum da zai gabaceta cikin daraja.

kamar yadda sarkin mumiani ali (as) ya kasance ma'aunin ayyuka lalle ne fatima (as) tamkace gare shi kuma shugabar matan aljanna, bisa gwauranta da kin yin aure bai sanyawa mutum wata daraja da kamala.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : من تزوّج فقد أحرز نصف دينه ، فليتّقِ الله في النصف الباقي[15]

4- manzon Allah (saw) na cewa dukkanin wanda ya yi aure ya tabbatar da rabin addinisa ya ji tsoron Allah cikin daya rabin.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : من أحبّ أن يلقى الله طاهراً مطهّراً فليلقه بزوجة

5- wani fadin kuma ya ce : dukkanin mai son ganawa da Allah ya na tsarkakakke mai tsarkakewa to ya yi kokarin ganawa da shi alhalin ya na da aure,

وقال  : شرار موتاكم العزّاب

6- a wani hadisin kuma ya ce : mafi kaskancin mamatanku gwagware.

وفي حديث آخر  : رذّال موتاكم العزّاب

7-a wani hadisin kuma ya ce: wukantattun mamatanku su ne gwauraye.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : النكاح سنّتي فمن رغب عن سنّتي فليس منّي

8-aure sunnata ne dukkanin wanda ke kyamar sunna ta baya daga gareni.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : تناكحوا تكثروا فإنّي اُباهي بكم الاُمم يوم القيامة ولو  بالسقط  

9-ku yiyyi aure ku yawaita lalle ni zan yiwa al'ummu alfahari da ku ranar kiyama koda kuwa da dan da akayi barinsa.

wannan hukunci mai gamewa ne har zuwa ranar kiyama yana mai kishiyantar masu cewa a takaita hayayyafa kamar yadda ya ke cikin wannan zamani da muke ciki, sai dai cewa an riwaito cewa karancin iyali na daya daga cikin sauki, dukkanin me son rayuwa cikin sauki ba kunci ta fuskanin tattalin arziki, to yalwarsa wani lokaci kan kasancewa cikin kudi da dukiya, wani lokacin kuma cikin karancin iyali da  `ya`ya, sannan alfaharin manzon Allah (saw) da adadi ne kamar yadda  zahiri  abin da za'a fahimta shi ne cewa alfahari wani lokacin na kasancewa da yawan adadi, wani lokacin kuma da yanayi sau da yawa kana samun mai karancin iyali amma ka ga ya samu damar tarbiyantar dasu fiye waninsa.

sannan babu  karo da juna cikin hadisan biyu domin cewa rashin yawan iyali daya daga cikin yalwa ne cikin tattalin arziki, wanda ke da iko da dukiya ya hayayyafa da yawa annabi(saw) zai alfahari da shi  hatta dan da akayi barinsa daga cikin abin da ke ishara ya zuwa cewa aure na kawo kamala shi ne:

عن رسول الله (صلى الله عليه وآله) ، قال  : من تزوّج فقد اُعطي نصف العبادة[16]

10-Abin da aka riwaito daga manzon Allah (saw) dukkanin wanda ya yi aure hakika an bashi rabin ibadarsa.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : المتزوّج النائم أفضل عند الله من الصائم القائم العزب

11- manzon Allah(saw)ya ce: mai auri da yake barci ya fi daraja wajen Allah daga tuzuru mai azumi mai tsayuwa dare.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : يفتح أبواب السماء بالرحمة في أربع مواضع  : عند نزول المطر ، وعند نظر الولد في وجه الوالدين ، وعند فتح باب الكعبة ، وعند النكاح

12- wani fadin kuma ya ce : ana bude kofofin sama da rahama cikin wurare hudu : yayin zubar ruwan sama, lokacin da da ke kallon fuskar mahaifansa, yayin bude kofar ka'aba, da lokacin daurin aure.

وقال (صلى الله عليه وآله) لرجل اسمه عكّاف  : ألك زوجة  ؟ قال  : لا يا رسول الله ، قال  : ألكَ جارية ، قال  : لا يا رسول الله ، قال  : أفأنت موسر  ؟ قال  : نعم . قال  : تزوّج وإلاّ فأنت من المذنبين

13-Manzon Allah (saw) ya cewa : wani mutu da ake kiransa akkaf shin kana da mata ? sai mutum ya ce banda mata ya manzon Allah, sai ya kara tambayarsa kana da baiwa ? sai ya ce a' a ya manzon Allah, sai ya kara tambayarsa shin kana yalwar hannu ? sai ya ce na'am

sai manzon ya ce masa ka yi aure idan ba haka ba kai mai zunubi ne.

وفي رواية  : تزوّج وإلاّ فأنت من رهبان النصارى

 14- a wata riwayar kuma ka yi aure in ba kayi ba kai baruhubane ne na nasara, ko kuma dan'uwan shaidanu.

قال (عليه السلام)  : شراركم عزّابكم ، والعزّاب إخوان الشياطين

15-manzon Allah (saw) ya ce : mafi sharrin cikinku gwagwarenku, su gwauraye `yan'uwan shaidanu ne.

وقال (عليه السلام)  : خيار اُمّتي المتأهّلون ، وشرار اُمّتي العزّاب

16-ya ce : mafi alherin cikin al'ummatu ma'aurata, mafi sharrinsu gwagware.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : من أحبّ أن يكون على فطرتي فليستن بسنّتي ، وإنّ من سنّتي النكاح

17- duk mai son kasancewa kan dabi'a ta to ya raya sunnata, kuma hakika daga cikin sunna ta aure.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : زوّجوا أياماكم ، فإنّ الله يحسن لهم في أخلاقهم ، ويوسّع لهم في أرزاقهم ، ويزيدهم في مروّاتهم

18-wani gurin ya ce : ku aurar da gwagwarenku, hakika Allah zai kyawunta musu  cikin dabi'unsu, ya yalwata musu arzikinsu, ya kara mutunci.

وقال  : ما بني في الإسلام بناء أحبّ إلى الله عزّ وجلّ وأعزّ من التزويج

 ya ce ba ayi wani gini a muslunci mafi soyuwa wajen Allah[1] Nisa'i:28

[2] Anbiya:37

[3] Ma'arij:19-20

[4] Isra'I:67

[5] Isra'i:65

[6] Shura:48

[7]Abasa:17

[8] Adiyat:6-7

[9] Ahzab:72

[10] Kahfu:54

[11] Nisa'i:1

[12] Hujrat:13

[13] Biharun anwar m 100 sh 217

[14] Biharul anwar m 100 sh 219

[15] Masdarin da ya gabata

[16] Biharul anwar m 100 sh 220