فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

KARUWAR ARZIKI

 

وقال (صلى الله عليه وآله)  : « التمسوا الرزق بالنكاح

9-Manzon Allah (saw) ya ce: ku nemi arziki ta hanyar yin aure.

عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع فَقَالَ لَهُ هَلْ لَكَ مِنْ زَوْجَةٍ فَقَالَ لَا فَقَالَ أَبِي وَ مَا أُحِبُّ أَنَّ لِيَ الدُّنْيَا وَ مَا فِيهَا وَ أَنِّي بِتُّ لَيْلَةً وَ لَيْسَتْ لِي زَوْجَةٌ ثُمَّ قَالَ الرَّكْعَتَانِ يُصَلِّيهِمَا رَجُلٌ مُتَزَوِّجٌ أَفْضَلُ مِنْ رَجُلٍ أَعْزَبَ يَقُومُ لَيْلَهُ وَ يَصُومُ نَهَارَهُ ثُمَّ أَعْطَاهُ أَبِي سَبْعَةَ دَنَانِيرَ ثُمَّ قَالَ لَهُ تَزَوَّجْ بِهَذِهِ ثُمَّ قَالَ أَبِي قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص اتَّخِذُوا الْأَهْلَ فَإِنَّهُ أَرْزَقُ لَكُم[1]

10-Alkafi da isnadinsa daga baban Abdullah (as) wani mutum ya je wajen baban Abdullah (as) sai babana ya ce masa shin kana da aure sai mutum ya ce: a'a, babana ya ce: bana son duniya da dukkanin abin da ke cikinta ya kasance ni na kwana dare daya alhalin banda mata, sannan ya kara cewa raka'a biyu da mai aure zai sallaceta tafi falala daga tsayuwar daren tuzuru da azumce rana, sai ya bashi dinare bakwai ya ce : ka yi aure da wannan,  ya ce: manzon Allah (saw) ya ce ku riki iyali hakika su arzikinku ne.

المصدر بسنده عن جعفر بن محمّد عن أبيه عن آبائه (عليه السلام) قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : من ترك التزويج مخافة العيلة فقد أساء ظنّه بالله . إنّ الله عزّ وجلّ يقول  : (  إنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللهُ مِنْ فَضْلِهِ[2]   

11-daga baban jafar (as) daga babanninsa ya ce : manzon Allah (saw) ya ce : duk mutumim da yaki yin aure saboda tsoron talauci lalle ya munanta zatonsa ga Allah, hakika Allah mai girma da daukaka ya na cewa: idan suka kasance talakawa Allah zai wadatasu daga falalarsa.

ـ الفقيه ، بسنده ، قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : من سرّه أن يلقى الله طاهراً مطهّراً فليلقه بزوجة ، ومن ترك التزويج مخافة العيلة فقد أساء الظنّ بربّه عزّ وجل[3] .

12-Daga littafin alfakihu da isnadinsa manzon Allah (saw) na cewa: dukkanin wanda ya ke faranta masa ace ya hadu da ubangiji ya na tsarkakakke mai tsarkakewa  to ya hadu da shi yana mai aure, dukkanin wanda ya bar aure saboda tsoron talauci lalle ya muzanta zatonsa da ubangijinsa mai girma da daukaka.

عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ ص فَشَكَا إِلَيْهِ الْحَاجَةَ فَقَالَ تَزَوَّجْ فَتَزَوَّجَ فَوُسِّعَ عَلَيْه.وقال:اتخذوا الأهل فانه أرزق لكم,وقال:تزوجوا للرزق فان لهن البركة.[4]

13-.Alkafi da isnadinsa daga baban Abdullah (as) ya ce : wani mutum ya zo wajen annabi (saw) sai ya kai kukan bukatarsa ga annabi, sai annabi (saw) ya ce masa kayi aure, sai mutum ya yi aure Allah ya yalwata masa arziki  a wani fadin manzon  Allah (saw) ya ce : kuyi aure don neman arziki hakika albarka na tare da mata.

  duk wanda ya kasance talaka  daga cikin tasirin canjin yanayi cikin aure shi ne samun karin arziki, kamar yadda ubangiji ke fadi ( idan sun kasance talakawa Allah zai wadatasu daga falalarsa ) yayin da saurayi ya yi aure da farko zai ga cewa an dora nauyi kan wuyansa to anan nefa zaka ga ya daura damara da dagewa wajen yin aiki tukuru, sai kaga arzikinsa na ta karuwa, Allah na azurta wanda ya so ba tare da lissafi ba ya sanya albarka cikin wanda ke yin aiki da tsarkakakkiyar niyya da dogaro da shi, baya tsoron talauci da yawan iyali  hakika arzikin kowa na hannun Allah, kamar yadda ya zo cikin Karin Magana cewa: dukkanin wanda aka azurta shi da hakora to za a azurta da gurasar da zai tauna.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : « من ترك التزويج مخافة العيلة فقد أساء الظنّ بربّه ، لقوله سبحانه وتعالى  :  إنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللهُ مِنْ فَضْلِه

14-manzon Allah(saw):duk wanda ya ki yin aure saboda tsoron talauci lalle ya munana zato ga Allah, saboda fadin Allah: idan sun kasance talakawa Allah zai wadata su daga falalarsa. 

Lalle mumini ya kyawunta zato ga ubangijinsa, hakika Allah matsarkaki na cewa: ni ina wajen zaton bawana mumini, kuma Allah na son masu tawakkali, shi motsi da fita nema suna kan bawa albarka kuma na wajen ubangiji kamar yadda ya zo cikin karin magana.

قال (صلى الله عليه وآله)  : تزوّجوا النساء ، فإنّهنّ يأتين بالمال

15-manzon Allah (saw)ya na cewa : ku auri mataye hakika su suna kawo dukiya.

 Allah ma'abocin albarka ya na albarkantakar ma'aurata masu mika al'marinsu gare shi da tawakkali, matar da ka aura takan zama sanadin samun dukiya da kudade na halaliya da arziki tsaftatacce mai amfani.

عَنْ إِسْحَاقَ بْنِ عَمَّارٍ قَالَ: قُلْتُ لِأَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع الْحَدِيثُ الَّذِي يَرْوِيهِ النَّاسُ حَقٌّ أَنَّ رَجُلًا أَتَى النَّبِيَّ ص فَشَكَا إِلَيْهِ الْحَاجَةَ فَأَمَرَهُ بِالتَّزْوِيجِ فَفَعَلَ ثُمَّ أَتَاهُ فَشَكَا إِلَيْهِ الْحَاجَةَ فَأَمَرَهُ بِالتَّزْوِيجِ حَتَّى أَمَرَهُ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ فَقَالَ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ ع [نَعَمْ] هُوَ حَقٌّ ثُمَّ قَالَ الرِّزْقُ مَعَ النِّسَاءِ وَ الْعِيَال[5]

16-Alkafi da isnadinsa daga is'hak dan ammar ya ce: na cewa baban Abdullah (as) shin hadisin  da mutane keta rawaitowa gaskiya ne cewa wani mutum ya zo wajen annabi ya kai kukan bukatarsa sai annabi ya umarce shi da yin aure, mutumin ya aikata, ya kara dawowa wajen annabi karo na biyu ya kara kai kukan bukatarsa annabi ya kara umartarsa da yin aure, ya maimaita hakan har karo na uku annabi dai yana kara umartarsa da aure ? sai baban Abdullah (as) ya ce: na'am gaskiya ne, sai ya ce: arziki na tare da da mata da iyali.

Galibi cikin al'amarin aure shi ne daduwar arziki, sai dai cewa a wasu  kadan daga cikin lokuta wanda bai fiye afkuwa ba karuwar arziki kan kasance cikin rabuwar aure da saki, cikin misalin wannan sai akomar da al'amari ya zuwa annabi ko imami masana ga hakikanin al'amurra, bai halasata ga wani mutum idan ya riski kunci cikin farkon rayuwarsa ta aure ya fara tunanin yin saki saboda wani nassi da ya ke da shi daga wani hadisi kwaya daya rak, saboda wannan hadisi bai iya jayayya da hadisai masu tarin yawa da suka zo suna ishara kan cewa aure yana kara arzik , saboda haka sai a lura.

عَنِ ابْنِ أَبِي لَيْلَى قَالَ حَدَّثَنِي عَاصِمُ بْنُ حُمَيْدٍ قَالَ: كُنْتُ عِنْدَ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع فَأَتَاهُ رَجُلٌ فَشَكَا إِلَيْهِ الْحَاجَةَ فَأَمَرَهُ بِالتَّزْوِيجِ قَالَ فَاشْتَدَّتْ بِهِ الْحَاجَةُ فَأَتَى أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع فَسَأَلَهُ عَنْ حَالِهِ فَقَالَ لَهُ اشْتَدَّتْ بِيَ الْحَاجَةُ فَقَالَ فَفَارِق.[6]

17-Alkafi da isnadinsa daga baban laila ya ce : asim dan hamidu ya bani labari ya ce : na kasance wajen baban Abdullah (as) sai wani mutum ya zo wajensa ya gaya masa bukutarsa, sai ya umarce shi da yin aure, ya ce sai bukatar ta kara tsananta, ya kara zuwa wajen baban Abdullah(as) ya tambaye shi halin da ya ke ciki sai mutumin ya ce : bukatar ta tsananta kaina, sai imam ya ce: ka saketa.

18-daga baya mutumin ya zo wajen imam (as) imam ya tambayeshi halin da ya ke ciki, sai ya ce : nayi kudi halin da na ke ciki ya kyawunta, imam ya ce : hakika na umarce ka da al'amura biyu da Allah ya yi umarni da suوَأنكِحُوا الأيَامَى مِنْكُمْ   (ku auri mata marasa miji daga gareku ) ya zuwa[7]وَاللهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ   

 Allah mayalwaci ne masani.

  wata ayar kuma ya ce: وَإنْ يَتَفَرَّقَا يُغْنِ اللهُ كُلاّ مِنْ سَعَتِه[8]ِ   (idan suka rabu Allah zai wadata kowannensu daga yalwarsa.

 [1] Alkafi m 5 sh 329

[2] Nurr:32

[3]Alfakihu m 3 sh 385

[4] Alkafi m 5 sh330

[5] Alkafi m 5 sh 330

[6] Alkafi m 5 sh 331

[7] Nurr:32

[8] Nisa'i:130