فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE

 

Allah ya halicci matum cikin halin kasancewarsa mai zabi, ya kuma shiryar da shi hanya, kodai ya yi godiya ko kuma ya kafirce,  bai da wani abu sabanin abin da ya yi fafutika kai, shi ne wanda ke  zabarwa kansa hanyar alheri ko ta sharri, wannan ma'anar na gudana cikin dukkanin bangarorin rayuwarsa da inda ta fuskanta, sai dai cewa da ludufi daga Allah matsarkaki ta hanyar manzanni da annabawa da littafan da suka zo daga sama an sanar da shi abin da bai sani ba, an kuma nuna masa sahihiyar hanya mikakka, an sanya masa alamomi da isharori  cikin hanyarsa ta rayuwa, don gudun kada ya bace ya rude cikin duhun kwazazzabon  jahilci.

daga cikin abin da ubangiji ya sanar da shi cikin rayuwar aure da samar da iyali shi ne tunda farko  ya nuna masa cewa akwai wasu dalilai da illoli na ciki da na waje da suke tasiri cikin tarbiyyar iyali da kasantuwarsu ta fuskanin hukuntawa da sababi wadanda dukkaninsu tawayayyu ne  basu zama cikakku ba cikin tasirin, ana kiransu da dokokin al'ada da gado,  kadai an kirasu  hakan don saukakawa, domin dokokin sababi da musabbabi da lissafi dokoki ne na hakika basu canjawa, amma dokokin jeka nayika kamar dokokin mutum da ya kirkira dokokine da suke karbar canaji, abin da ake kira da dokokin gado, an kira su da hakan ne saboda rashin wadancananka, kamar yadda yake yiwuwa  mukasa dokoki ya zuwa na dabi'a wanda ke karbar canji da na shari'a wanda basa canjawa,

ma'abota imani da jabaru(tilastawa) bisa rayawarsu dake kan bata sun tafi kan dokar gado, sai dai cewa wannan ra'ayi nasu abin wurgine kamar yadda hakan ya tabbata a mahallinsa.[1] hakika siffofin gangar jiki da ruhi na iyaye na da tasiri cikin siffar danda aka haifa. 

Hakika bayyanannen abune cewa daga cikin tsarin halitta shi ne tasirantuwa da wata siffa daga siffofin mahaifa ya zuwa ga dan da suka haifa bisa tsarin kwayar halitta,

Kamanni da halayyar mahaifa na da tasiri cikin kamannin `ya`ya maza da mata.

Misali uwa ma'abociyar hassada takan gadarda wannan halayya ya zuwa ga `yarta, haka uba marowaci matsolaci yana gadarda wannan dabi'a ya zuwa dansa, haka al'amarin ya ke cikin kyawawan dabi'u kamar jarumataka, karamci, tausayi, kauna, haikika wadannansiffofiyawanci ana gadonsu daga iyaye, kamar yadda ubangiji ke cewa:

 وَالْبَلَدُ الطَّيِّبُ يَخْرُجُ نَبَاتُهُ بِإِذْنِ رَبِّهِ وَالَّذِي خَبُثَ لَا يَخْرُجُ إِلَّا نَكِدً[2]ا

 gari mai kyawu yana fitar da tsirransa da izinin Allah amma wanda ya munana baya fitar da komi face wahala.

Saboda haka ka lura da inda zaka sanya digon maniyyinka domin hakika jijiya ta na naso, ta yiwu jijiya anan kamar ishara ne ya zuwa kwayar halitta, halayya da siffar mahaifa haka suke sunada tasiri cikin tarbiyyar yara da halayyarsu, babu wanda ke inkarin haka kamar yadda riwayoyi masu tarin yawa suka nuni kan haka, hakika ubangiji ya sanya iyakoki ga aure ga duka bangare biyun bangaren miji da bangaren mata, saboda dalilai na tasirin gangar jiki da  ruhi  cikin iyaye kan `ya`ya, sai dai duk da haka bai kasance tasiri dari bisa dari ba bai kuma kasance cikakken dalili wanda bai yiwuwa a ratse masa ba, sauda yawa munga iyaye munana sun  haifi `ya`ya nagari, hakama mun sami iyaye nagari sun haifi `ya`ya marasa tarbiyya, sai kaga wasu lokutan kyakkyawa ya fito daga mummuna ko mummuna ya fito daga kyakkyawa, ko kuma rayayye ya fito daga matacce, matacce ya fito daga rayayye, da wannan tasirantuwar dari bisa dari ne da bazai taba yiwuwa a tsallake a ratse masa ba,  da tarbiyya da koyarwa sun wayi gari matsayin wargi da wasa.

bari madai sau da yawa mun sami cewa daga ladubba abin da ya iya canja al'umma cikin wani zamani, kamar yadda aka sanya dokokin al'ummu, haka shi ne  mafi bayyanar dalili kan cewa gado bai tilasta mutum kan ayyukansa na'am yana da tasiri a jumalace ta wani sashen  saboda haka ne ma muslunci ya himmatu da mas'alar gado da  irin tasiri da inda aka taso yake da shi, haka tasirin halittarshi  daga mafi muhimmancinsu


[1] Masa'alar jabar da iktiyar na da ga cikin masa'alolin ilimin kalam da falsafa masu wahalar gaske, sunada tsohon tarihi. Maganar gaskiaya shi ne abin da ya zo daga daga imamai(as)cikin hadisin iama sadik (as): babu jabar babu tafwid sai dai cewa al'amari ne da ke tsakaknin al'amura biyu.

Sai dai cewa su asha'ira sun tafi kan jabar(tilastawa) su kuma mu'utazilawa sun tafi kan tafwidi(fawwalawa) haka cikin masana falsafa akwai wadanada suka tafi kan ra'ayin jabar wanda ake kiran ra'yin nasu da jabarul falsafi. Haka madiyun na zamani suna wannan ra'ayi wanda ake kiransa da jabarul madi wanda ke dora ayyukan mutum kan illoli na zahiri na mada da ta ke kasancewa daga kankin kansa  da ruhinsa, iata ce mai gina hakikanin mutum ta kasantar da shaksiyyarsa ta  tura shi  zuwa ga aiki da ya dace ga wannan shaksiyya ta sa, ita kowacce kwarya na yayyafin abin da ke cikinta ne , mutum duk da kasantuwarsa `yan tacce a zahiri, sai dai cewa iadan akai duba ya zuwa zawiyyarsa uku ta mutum  zamu mu san cewa babu tsira face mika wuya ya zuwa abin da ransa da ruhinsa ke karta gare shi sabubba uku da ke kasantar da mutumtakarsa a tunanance da suluki da aiki sune:

1 – gado

2 – wayewa

3 – muhalli

Hakika cikin kashin farko wato gado `ya`ya na gadon mahaifansu  maza da cikin madaukakan dabi'u ko kaskantattun halaye munana.

Hakika halaye na tasowa ta hanyar gado ta hanyar dabbobi masu fitar da maniyyi cikin uba cikin uwa kuma ta hanya kwai ya zuwa ga dansu da suka haifa. Da uwa da ubane mutumtakar da ke kasantuwa da sulukinsa.

Ai na biyu wato sakafa da ta'alim lalle suna da tasiri mai girma cikin mutumtakar mutum hakika  shi dasu ne yak e dagawa zuwa tauhidi ko karkacewa da bata, da motsi da jumudi, kwadayi da kana'a,da dai makamantan haka daga ruhoiyat da ke hukunci na musammamn da su mutum ke karkata zuwa suluki ayyananne.

Amma kasha na uku wato muhalli: lalle mutum haifaffen muhallinsa ne cikin sulukinsa da halayyarsa saboda haka ne ma muke ganin sabani suluki cikin al'ummu gwargwadon sabanin muhallin da suke rayuwa.

Kan wadannan sabubba ne mutum ke harrakawa kuma kowanne irin aiki ke kwarara daga gare shi, kai hatta iradar mutum wadda ake kirga ta alamin zabinsa  iota ta samu sakamakon wancan muhalli da ya taso ciki, yayinda  wadannan sabubba suka kasance sun fita daga zabinsa to haka ma abin da zai tuke garesu.

Amsa ga wadannan abubuwa a bayyane ta ke, babu shakka cikin tasirin wadannan sabubba cikin kasantuwa mutumtaka sai dai ba ta yadda za su raba mutum da zabi ba, idan bah aka ba falsafar aiko annabawa za ta rushe, haka ma dukkanin fafutikar masu tarbiyya da ayyuka bayi salihai masu kwao gyara za su ta fi a iska a wofi. Su dai wadannan sabubba bas u fita da ga kasantuwarsu mukaddima da shimfida da ke bukatar abubuwa bisa dabi'arta sai dai cewa bayan akwai `yancin mutum da zabinsa, kamar yadda laruira ke shaida hakan, mutum nawa yay i galaba kan dabi'un da ya ta so cikin muhallin da aka haife shi da kafiri amma kuma ya canja ya zama musulmi, da ba shi'a ba ne yay i bincike ya koma shi'a, hakika ma'abota wancan ra'ayi sun tafka kuskure cikin cudanya abin da ake kira da ijab da ikhtida'I da cikakkiya illa wadda ma'alul dinta ba zai taba yiwuwa ya sabawa illarsa ba , dakuma illa tawayayyiya wadda ita na hukunci ne idan abin da zai hukunci ya samu, sai idan wani abu ya shiga tsakani ya kawo cikas.

Su `ya`ya ye nay o gadon siffofi na ruhi da halaye a jumlace daga iyayensu.

 

[2] A'araf:85