فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI

 

Babban malaminmu shehul Ansari ya bijiro da bahasi kan hukuncin ilimin bugun kasa cikin littafinsa mai suna (almakasibul muharrama ) ya yi la'akari da karbar lada kan ilimin da kasantuwar haramcin yin kasuwanci da ilimin. 

bugun kasa a kankin kansa aiki ne haramtacce, ya ce sanin bugun kasa haramun ne, kamar yanda al'amarin ya kasance cikin littafin jami'ul makasida na muhakkik karaki  shi ilimin sanin taurari shi ne: bada labarin hukunce hukuncen bugun kasa tare da la'akari da jujjuyawar falaki da sadarwar taurari.

bai buya cewa abin da ake nufi da bugun kasa cikin abin da babban malaminmu ya kawo shi ne dai abin da `yan tsubbu keyi tare da da'awar sanin nasibin mutane na rayuwa da makomarsu bisa jujjuyawar tauraro da tafiyarsa bisa la'akari da  motsin falaki, shi ne tafiyar taurari bakwai daga wata da rana da mushtari da zuhuli da adarid da zuhra  da marriku, bisa yanda masana magabata suka tafi kai,  ta yanda suka ce: cibiyar duniya itace kasa, hakika halittu da taurari dukkaninsu suna daura da kasa da jujjuyawa geffenta, amma wajen masanan wannan zamani tare da abin da aka kai ga ganowa  duniyar guda tara ce sabani abin da magabata suka tafi kai kan cewa bakwai ne, tare da karuwar tauraron ( uranus da nabtun ) aka kuma kara gano wani abun sabo shine kasantuwar rana matsayin cibiya, cibiyar komai itace rana kuma gefenta komai ke kewayawa, wannan kekkewaya tare da la'akari da nakaltuwa  yana haifar da dare da rana da fasali hudu sanyi zafi damuna da kaka, da hijira shamsiya da kamariya.

Ana kiran dukkaninsu da (maj'mu'a shamsiya ) abin da ake nufi da sadarwar tauraro shine kusantar sahsenshi ya zuwa sashe ko nesanatar junansu.

 sannan kowanne kusanta da nesanta nada

hukunci kebantacce wajen masana taurari

Sannan babban shehi ya kara bijira zuwa hukuncin bugun kasa da taurari tare da bayani kai dalla-dalla cikin makamai masu yawa  cikin mukamin farko ya yi hukunci da rashin haramcin bada labarin yanayin falaki wanda ya ginu kan tafiyar taurari kamar kisfewar rana da wata da makamancinsu, bari ma dai ya halasta hakan tare da da yin hukunci kai tsaye ko bisa tsammani, sannan mas'alar na daga mas'alar da malamai keda sabani kanta.

muhakkik karaki ya tafi kan halascin hakan tare da karfafarsa da karhancin yin tafiya da yin aure cikin burujin akrab.

Ina cewa kadai yana halasta  cikin wurare kebantattu, idan bugun kasar ya kasance ta fuskanin dalili na biyu ba kasantuwarsa cikakken sababi da illa kan afkuwa wani al'amari ba.

 yawancin malamai sun tafi kan haramci wasu cikinsu sun ce gurbatarsa na daga abubuwan da ake sallamawa cikin addini,wasu kuma sun ce ba dukkaninsa ne haramun ba, kamar yadda riwayoyi suka zo da hani mai tsanani kai da yin umarni da a kona dukkanin littafan bugun kasa, sannan kuma akwai riwayoyin da suka zo da yabo kai, da kuma kasancewarsa daya daga cikin iliman annabawa farkon wanda ya fara magana kansa shine annabi idris (as)

duk da kasantuwar cutarwarsa tafi amfanarwarsa yawa.

babban shehi a mukami na biyu ya na cewa: bada labari kan abubuwan da zasu faru gobe ta hanyar bugun kasa  da yin hukunci da shi tare da jingina ya zuwa tasirin sadarwar taurari cikinsa kai tsaye ko kuma tare da cudanyashi , zahirin fatawa da nassosi karfafaffu ana masa hukunci ne da haramci, hakika muhakkik karaki ya kawo riwaya mursala daga annabi (saw) ya ce:

من صدق منجما أو كاهنا فقد كفر بما أنزل على محمد (ص)

 dukkanin wanda ya gasgata mai bugun kasa ko boka to hakika ya kafirta da abin da aka aikowa muhammadu (saw) wannan riwaya kai tsaye tana hukunci kan haramcin bugun kasa.

.نصر بن قابوس عن الصادق (ع): ان المنجم ملعون,والكاهن ملعون, والساحر ملعون.

 nasru dan kabus daga imam sadik (as) hakika an la'anci mai bugun kasa da boka da  matsafi.

Ya zo cikin nahjul balaga : cewa yayin da imam ali (as) ya yi nufin yin tafiya cikin sashen tafiye tafiyensa na daukaka kalmar Allah,  wani sashe daga sahabbabnsa wani ya ce masa: idan kayi wannan tafiya  cikin wannan lokaci ina jima tsoron karka gaza samun nasarar kan muradanka saboda dogaro da hanyar ilimin taurari.

 imam ya ce masa: shin kana raya cewa kai kana shiryarwa zuwa lokaci idan anyi tafiya cikinsa  za'a ingijewa mutum sharrinsa, sannan kana tsoratarwa da yin tafiya kan wani lokaci wanda idan mutum ya yi tafiya cikinsa zai fuskanci matsala da cutuwa, duk wanda ya gasgata wannan raye-raye to ya karyata alkur'ani, ya wadatu gabarin taimakon Allah cikin neman abin da yake so da ingije abin da yake gudarwa da kinsa, ya ku mutane ku sani sanin taurari ba bakin komai yake ba face wanda ake shiriya ya zuwa teku da ban kasa ta hanyarsa, hakika bugun kasa da taurari yana kira  zuwa bokanci, mai bugun kasa misalin boka yake, boka kuma dai-dai yake da matsafi, matsafi dai-dai yake da kafiri, sannan kafiri kuma na wuta, ku tafi kan sunan Allah.[1]

amma hadisin da ya zo yana hani kan yin tafiya da aure halin burujin akrab:

عن محمد بن حمران عن أبيه عن أبي عبد الله (ع)قال:من سافر أو تزوج والقمر في العقرب لم ير الحسنى.

  ankarbo daga muhammadu dan himran daga babansa daga baban Abdullah (as) ya ce : duk wanda ya yi aure ko tafiya alhalin wata yana burujin akrab ba zai ga alheri ba.

wannan hadisi yana ishara karara kan tasirin taurari cikin alheri da sharri.

amma abin da ake nufi da burujin akrab yana komawa zuwa kalmar tsofaffin masana na kasar babila daga tunaninsu cikin samaniya ga  surori da shakalai  ga taurari tabbatattu ya zuwa tsari guda. wadannan surori wasunsu kammalallum wasunsu tawayayyu, sannan sun kebancewa dukkanin taurarri shakali wanda adadinsu yakai ga (1025) ko (1022) idan muka kyale guda ukun wanda (badalimus) ya cire  saboda tsananin kankantarsu, shi kuma kawaja Abdurrahman sufi ya shigar dasu da rarrabasu daga wadannan taurari (917) da suka shiga cikin wannan surori, ragowar kuma (105) dake  wajenta suna zaune kusa da geffanta, ana kiran kashin farko: cikin sura, kashi na biyu: wajen surori.

Kadai dai sunyi hakan ne saboda ayyana matsugunan wadancan taurari lokacin hisabi, idan suka bada labari sai suce : tauraro mai kewaya rana yana kan sura kaza da kaza ko kan jelarta  ko tsakiyarta, don bayyanar da tauraro mai kewaya duniya  da matsugunisa a samaniya, hakan idan ya kasance cikin sura, amma idan wajentane sai suce: tauraro kaza yana tsugune kusa da kan sura ko kusa da kafarta …..  

Gaba dayan wadannan surori sun kai adadin surori (48)  guda 21 suna yankin arewada buruji sannan guda 15 suna kudancin buruji ragowar 15 din kuma suna kan da'irar burujin.

abin da ya ta'allakantu da maudu'i shi ne (wata cikin burujin akrab ) itace surar da ke fadawa yankin buruji wadda ita ce ma'auni kekkewayar rana da wata da magudanarsu.

 kewayawar rana cikin shekara guda ma'ana kawanaki (365)  da rubu'i

Kewayawar wata cikin wata guda kwanaki (27 ) da awanni 7 da minti 42 sai dai kuma kasantuwar rana tana kauracewa mahallinta cikin  wannan lokuta saboda cudanyarta da wata a farkonsa sai ta dan karu kadan  ya zama tilas wata ya gudana har ya samu damar haduwa da rana karo na biyu don wata ya kamalla cif cif, da hakanne watan hijira kamariyya ke kaiwa kawanaki (29) da awanni 12 da minti 44.

Sannan( mahallin buruji ) shi ne daga da'irori manya manya guda 10  shi ne da'irorin wahami wanda ya karkace daga da'irar tsakiyar rana

Sun karkasa wannan maguda zuwa kashi 12  kowanne kashi na da buruji guda, sannan suka kasa dukkanin fasalai hudu na shekara ya zuwa buruji uku.

1- burujin hamli  cikinsa taurari 13 a wajensa kuma akwai 5.

2- burujin sauru cikinsa  taurari 32 waje kuma 11.

3-burujin jauza'i cikinsa taurari 18 waje 8.

4- burujin saradanu cikinsa taurari9 wajensa 4.

5-buruji asadu cikinsa tauraro 27 waje 8.

6-burujin sunbula cikinsa tauraro 26 waje 6.

7- burujin mizani cikinsa taurari 8 waje 9.

8-burujin akrab cikinsa taurari 21 waje 3.

9- burujin kausu cikinsa taurari 31.

10- burujin jadyu (dan sanuwa) cikinsa taurari 28.

11-burujin dalwu ciknsa taurari 42 waje 3.

12-burujin hutu cikinsa taurari 34 waje 4.

Wadannan sune burujai 12 da wata ke ketasu awanni 13 da miniti 3 da sakonni 54, da wannan kewayawarsa cikin buruji 12 cikin kwanaki 27 da awa 7 da minti 43, sakamakon kasantuwar kowanne burji na da daraja 30 to wata na bakunta cikin kowanne buruji kasa da kwanaki uku, ma'ana kwana biyu da rubu'i .

Masana taurari na cewa : duk wanda aka Haifa cilkin daya daga wadannan buruji 12 to zai kwaikawayi dabi'unsu, misali wanda aka Haifa cikin burujin asadu (zaki) to zai kwaikwayo dabi'unsa. ana kiran wannan da sunan masu tsinkayar abin da zai afku gobe kowanne dayansu yana da mai tsinkaya, sannan kowanne mai tsinkaya yana da fuskoki 3, ya na sanin halayyar rayuwarsa  cikin kowanne, mai tsinkaya kamar yadda aka ambaceshi cikin littafin abi masha'aril falak, Allah shi ne mafi sanin dai-dai da ingancin abin da ake fadi. sannan suna da hanyar hisabin tsinkaya  bisa dogaro da haruffan abjadiya cikin lissafa suna mutum da sunan mahaifiyarsa sai su karkasa shi zuwa 12  duk abin da ya ragu cikin lissafin zai kasance tsinkayarsa.

tsofaffin masana taurari sun ambaci cewa saukar wata cikin kowanne buruji yanada nasa tasirin na musammam basu gushe ba suna kudurce hakan, ana iya cewa babu inkarin hakan matukar Allah ya sanya yayewa da alama cikin izininsa, kamar yadda babu wanda ke inkarin tasirin sauyin yanayi cikin dabbobi da tsirrai.

sannan wannan rana mai tsananin haske tanada nata tasirin mai girma cikin wannan karamar duniyar da muke ciki daga sauyin yanayi halayya da rayuka da kasantuwa da gurbacewa da dai sauran abubuwa da baza mu iya sanin iyakarsu ba.

Kamar yadda cikin hudar wani sashe daga taurari misalin suhailu da haskenshi na da tasiri cikin nunar kayan marmari da kasantar dasu  haka al'amarin yake cikin tafiyar wata,  kowanne wata nada tasiri cikin dabi'a daga tumbatsa da tawaya da tasirin cikin dandanon mutum cikin al'adar mata ta wata wata wadda ke da dangantaka da hijira kamariya da dukkanin dangantuwa, saboda haka bazai yiwu ayi inkarin tasirin sauye sauye da canji  cikin wannan duniyar ba, da kuma cewa akwai dangantaka tsakanin sama da kasa da dangantakar babbar duniyar taurari da karamar duniyar tsirrai da ma'adanai da mutane da dabbobi.

Sun kawo cewa cirar wata zuwa burujin akrab na da tasiri daga cikinsu: yawaita damuwa cikin zukatan mutane, afkuwar fitintinu da rigingimu, yawaitar sace sace, rashin daidaitar al'amura, jinkiri cikin ayyuka, yawaitar cututtuka, taurari suna da tasiri cikin alheri da sharri cikin wani bangare, da basu da tasiri da babu abin da zai kawo Magana kan zargin yin aure ko tafiya cikin burujin akrab.[1] Nahjul balaga sharh ibn abul hadid m 1 sh 124