فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

SON MATA

                                

Soyayya na nufin karkatar badini ya zuwa ga abin da ake so, na da tasiri cikin zuciya da gabbai, sannan yakan sassabawa da sasabawar abin da ya ta'allaka dashi, cikin soyayya akwai son mata hakika son mata kan zama abin yabo wani lokaci, wani lokacin kuma abina zargi, daga farko:

قال رسول الله (ص) أحب من دنياكم ثلاث :الطيب,والنساء,وقرة عيني الصلاة.

1-      manzon Allah (saw) ya ce: ina son abubuwa uku daga duniyarku: turare da mata da sanyin idaniyata sallah.

عن الإمام الصادق (عليه السلام) ، قال  : العبد كلّما ازداد في النساء حبّاً ازداد في الإيمان فضلا

2-An karbo daga imam sadik (as) ya ce : duk sanda bawa ya karu cikin son mata zai karu cikin imani falala.

 عن امام الصادق(ع): من أخلاق الأنبياء(ع)حب النساء

3- Daga imam sadik (saw) yana cewa: daga cikin dabi'un annabawa (as) son mata.

misalin wannan soyayya data kasance mukaddimar sallah, kamar yadda sanya turare shi ma ya kasance haka babu shakka wannan soyayya za ta kasance abun yabawa bari ma dai tana daga abin da ke kara imani da falala, kuma tana cikin dabi'un annabawa.

amma soyayyar mata wadda bata kasance da manufar gabatar da aiki nagari ba, lalle zata zama fitina  da kasancewa abin zargi, kamar yanda zata wayi gari tushen zunubai da jijiyoyinsu kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja cewa abubuwa shida sun kasance sanadin zunubi, daga cikinsu akawi son mata.

قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع الْفِتَنُ ثَلَاثٌ حُبُّ النِّسَاءِ وَ هُوَ سَيْفُ الشَّيْطَانِ وَ شُرْبُ الْخَمْرِ وَ هُوَ فَخُّ الشَّيْطَانِ وَ حُبُّ الدِّينَارِ وَ الدِّرْهَمِ وَ هُوَ سَهْمُ الشَّيْطَانِ فَمَنْ أَحَبَّ النِّسَاءَ لَمْ يَنْتَفِعْ بِعَيْشِهِ وَ مَنْ أَحَبَّ الْأَشْرِبَةَ حُرِّمَتْ عَلَيْهِ الْجَنَّةُ وَ مَنْ أَحَبَّ الدِّينَارَ وَ الدِّرْهَمَ فَهُوَ عَبْدُ الدُّنْيَ[1]ا

4-Sarkin muminai aliyu (as) ya ce : fitina abubuwa uku ne : son mata wanda ya kasance takobin shaidan, na biyu shan giya barasa tarkon shaidan, na uku  son dinare da dirhami kibiyar shaidan, don wanda ke son mata bai zai amfana da rayuwarsa ba, wanda ke son kayan maye aljanna ta haramta gare shi, wanda ke son dinari da darhami ya zama bawan duniya.

Allah ya sanya misalin wannan soyayyar matan cikin zirin son shangiya, da wannan kiyastawa za a fahimci zurfin hatsarin son mata.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : أوّل ما عصي الله تبارك وتعالى بستّة خصال  : حبّ الدنيا ، وحبّ الرئاسة ، وحبّ الطعام ، وحبّ النساء ، وحبّ النوم ، وحبّ الراحة[2]

5-Manzon Allah (saw) ya ce : da abubuwa shida aka fara sabawa Allah madaukaki sune : son duniya, son shugabanci, son abinci, son mata, son barci, son hutu.

Babu karo da juna cikin riwayoyin ko da kuwa soyayyar ta kasance cikin mahanga biyu da la'akari ta fuska biyu, kasantuwar karo da juna da kishinyata akwai sharadin cewa dole ne kafin abubuwa biyu su zamo kishiyoyi juna su kasance ta fuska guda da la'akari ta fuska guda  saboda son mata akwai mai kyawu da mara kyawu.

عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: إِنَّ الْمَرْأَةَ خُلِقَتْ مِنَ الرَّجُلِ وَ إِنَّمَا هِمَّتُهَا فِي الرِّجَالِ فَأَحِبُّوا نِسَاءَكُمْ وَ إِنَّ الرَّجُلَ خُلِقَ من الأرض فانما همتهم في الأرض.[3]

6- an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce: hakika an halicci mace daga maza kuma kadai himmarta daga maza take, ku so matayenku hakika an halicci mazaje daga kasa himmarsu daga kasa take.

عن أبي عبد الله(ع)قال كل من اشتد لنا حبا اشتد للنساء حبا ولحواء.[4]

7- an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce: duk wanda ya tsananta soyayya gare mu to zai tsananta soyayya ga mata da hauwa'u

قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص أُعْطِينَا أَهْلَ الْبَيْتِ سَبْعَةً لَمْ يُعْطَهُنَّ أَحَدٌ كَانَ قَبْلَنَا وَ لَا يُعْطَاهُنَّ أَحَدٌ بَعْدَنَا الصَّبَاحَةَ وَ الْفَصَاحَةَ وَ السَّمَاحَةَ وَ الشَّجَاعَةَ وَ الْعِلْمَ وَ الْحِلْمَ وَ الْمَحَبَّةَ فِي النِّسَاء[5]ِ

8-Manzon Allah (saw) ya ce: mu ahlul baiti anbamu abubuwa bakwai wanda bawani da aka baiwa gabaninmu, kuma ba za'a baiwa wani ba bayanmu ba : kyawu, fasaha, kyauta, jarumtaka, ilimi, hakuri, son mata.

عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: مَا أَظُنُّ رَجُلًا يَزْدَادُ فِي هَذَا الْأَمْرِ خَيْراً إِلَّا ازْدَادَ حُبّاً لِلنِّسَاء[6]

9- Alkafi da isnadinsa daga baban Abdullah (as) ya ce : bana tsammanin wani mutum zai karu cikin wannan al'amari da alheri face ya karu da son mata.

Abin da ya ke nufi da wannan al'amari shi ne shi'anci da sanin imami da kuma rungumar wilayarsu.

الفقيه([151]) ، بسنده عن أبي العباس ، قال  : سمعت الصادق (عليه السلام) يقول  : العبد كلّما ازداد للنساء حبّاً ازداد في الإيمان فضلا[7]

10- Daga littafin alfakihu da isnadinsa daga baban abbas ya ce: naji sadik (as) yana cewa: duk sa'ilin da bawa ya karu cikin son mata zai karu cikin imani da falala.

المصدر نفسه ، عن معمر بن خلاّد ، قال  : سمعت عليّ بن موسى الرضا  (عليه السلام) يقول  : ثلاث من سنن المرسلين  : العطر ، وإحفاء الشعر ، وكثرة الطروقة .

11-daga mu'ammar dan kallad naji aliyu dan musa arrida (as) yana cewa : daga sunnonin manzanni : turare  taje kai,  da yawan kusantar mata.

الكافي([152]) ، بسنده عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : جعل قرّة عيني في الصلاة ، ولذّتي من الدنيا النساء ، وريحانتي الحسن والحسين  (عليهما السلام[8]

12- Alkafi da isnadinsa daga baban Abdullah (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: an sanya sallah sanyin idaniyata,haka an sanya mata jin dadina daga duniya,  kamshina Hassan da husaini (as).

بسنده عن بعض أصحابنا ، قال  : سألنا أبو عبد الله (عليه السلام) : أيّ الأشياء ألذّ  ؟ قال  : فقلنا غير شيء ، فقال هو (عليه السلام)  : ألذّ الأشياء مباضعة النساء .

13-Daga ba'arin sahabbanmu ya ce : mun tambayi baban Abdullah (as) wadanne abubuwa ne sukafi dadada ? sai muka fadi wasu abubuwa, s shi kuma ya ce: mafi dadada cikin abubuwa shi ne kusantar mata.

بسنده عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : ما تلذّذ الناس في الدنيا والآخرة بلذّة أكثر لهم لذّة من النساء ، وهو قول الله عزّ وجلّ  : (  زُيِّنَ لِلنَّاسِ حُبُّ الشَّهَوَاتِ مِنَ النِّسَاءِ وَالبَنِينَ  )([153]) ، إلى آخر الآية ، ثمّ قال  : وإنّ أهل الجنّة ما  يتلذّذون بشيء من الجنّة أشهى عندهم من النكاح لا طعام ولا شراب .

14-An karbo daga baban Abdullah (as) mutane basu danadani dadin wani abu duniya da lahira fiye da dadin mata ba, shi ne fadin Allah madaukaki:

an kayatawata mutane son sha'awa daga mata da `ya`ya 

A wani wajen kuma ya ce : basu jin dadin wani abu a aljanna daga abinci da abin sha mafi ban sha'awa daga kwanciya da mata .

وَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص 1 مَا رَأَيْتُ ضَعِيفَاتِ الدِّينِ نَاقِصَاتِ الْعُقُولِ أَسْلَبَ لِذِي لُبٍّ مِنْكُنَّ

Alfakihu : manzon Allah (saw) ya ce: ban taba ganin masu raunin addini da tawayar hankali mafi zobaitar kwakwale daga gareku ba mata.

ina cewa yana bayyana daga gabadayan riwayoyin masu daraja cewa son mata shi ne son matan aure ba dukkanin mata ba  kamar yadda ya ke a bayyane, sannan tsananin kusanci da daidaita na samuwa daga soyayya, daga nan kuma sai dai-daitar gangar jiki da yawaita kwanciya da juna, hakika hakan na daga cikin abin da ke kara soyayya idan ya kasance kewaye da ladubba da mukaddimomi kamar yadda ya gabata cikin riwayoyi masu daraja.

 [1] Biharul anwar m 100 sh 225

[2] Alkhisal m 1 sh 234

[3] Biharul anwar m 100 sh 227

[4] Biharul anwar m 100 sh 227

[5] Biharu anwar m 100 sh 228

[6] Alkafi m 5 sh 321

[7] Alfakihu m 3 sh 383

[8] Alkafi m 5 sh 321