فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

YARDA SHARADI NE CIKIN AURE

                          

dukkanin aiki dan adam sai niyya ta gabace ma'ana neman abin da ka ke son cimma, haka na kasancewa karkashin wasu mukaddimom : kamar kamar tunano abin da ka ke niyya, gasgata shi da fa'idarsa, shauki zuwa gare shi, da shaukin da yake cudanye da yunkuri ganin tabbatar da abin a kayi muradi da ganin an samar da shi.

sha'anin aure na bukatar a ce anyi kuduri da niyya tun kafin samun damar zaben wacce za'a aura, daga cikin abubuwan da ke lazimtar aure shi ne ya zama akwai yadda tsakanin saurayi da budurwa, kowanne daya daga cikinsu ya zamanto ya na son yin auren da niyyarsa  ba tare da wani ya tilsta shi ba, da zai zamanto an tiasta mace kan yin auren to da aure ya kasance gurbatacce, auren zai kasance alfasha da haramun har zuwa lokacin da ta yarda  sannanne zai zama halastacce, yarda da shi ko rashinsa na komawa ga ita macenne:

عن صفوان ، عن منصور بن حازم ، عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : تستأمر البكر وغيرها لا تنكح إلاّ بأمرها

1-an karbo daga sufwan , daga mansur dan hazim daga baban abdullah (as) ya ce: ana neman izinin budurwa da wantanta, ba 'a iya aurar da ita sai da izininta.

وقد روي عن أمير المؤمنين عليّ (عليه السلام) أ نّه ذكر حديث تزويجه من فاطمة وأ نّه طلبها من رسول الله (صلى الله عليه وآله) فقال  : يا عليّ ، إنّه قد ذكرها قبلك رجال ، فذكرت ذلك لها فرأيت الكراهة في وجهها ، ولكن على رسلك حتّى أخرج إليك ، فدخل عليها ، فأخبرها وقال  : إنّ عليّاً قد ذكر من أمرك شيئاً فما ترين  ؟ فسكتت ولم تول وجهها ولم ير فيه رسول الله (صلى الله عليه وآله) كراهة ، فقام وهو يقول  : الله أكبر سكوتها إقراره[1]ا

2- an riwaito daga sarkin muminai ali (as) cewa ya ambaci labarin aurensa da Fatima hakika shi ne ya nemi aurenta daga manzon Allah (saw)  sai ya ce masa: hakika gabaninka wasu sun zo nema aurenta, sai na gaya mata  sai na fuskanci ba ta so daga alamomin fuskarta, amma kadan jira in je in zo maka da bayani, sai manzon Allah (saw) ya shiga wajenta  ya bata labari ya ce: hakika ali (as)  ya ambaci wani abu game da al'amarinki amma mai ki ke umarta ? sai ta yi shiru ba ta juya fuska ba kuma bai ga alamun ba ta so ba daga fuskarta ba, sai ya tashi ya na cewa: Allahu akbar shirinta yardarta ne.

وذكر أنّ فتاة جاءت إلى رسول الله (صلى الله عليه وآله) تشكوا أباها فقالت  : يا رسول الله إنّ أبي زوّجني من ابن أخ له ليرفع خسيسته وأنا له كارهة ، فقال (صلى الله عليه وآله)  : أجيزي ما صنع أبوكِ ، فقالت  : لا رغبة لي فيما صنع أبي ، فقال  : إذن فاذهبي وتزوّجي من شئتِ ، فقالت  : لا رغبة لي عمّا صنع أبي

3- an ambaci cewa : wata budurwa ta zo wajen manzon Allah (saw) tana kai kukan babanta ta ce : ya manzon Allah (saw) babana ya aurar da ni daga diyan dan'uwansa saboda kawar da kin jininsa  amma ni ban son mijin, sai manzon Allah (saw) ya ce: ki halasta abin da babanki ya aikat , ta ce ni ban kaunar abin da babana ya aikata, sai ya ce mata: idan haka ne zaki iya tafiya ki auri duk wanda kike so  sai ta ce: ni banda wani kwadayi cikin abin da babana ya aikata.

Abin da za mu fuskanta daga wannan riwaya mai daraja cikin wannan babi shi ne cewa bazawara za ta iya aurar da kanta ba tare da izinin walaiyyita ba, amma budurwa ko dai an aura da ita da izinin waliyyanta sai dai cewa dole ne a nemi izininta domin shi ne asasi cikin asalin aurenta, tana hakkin yarda da kin yarda da auren da ka daura mata, bai inganta a tilasatata kan auren ( ana neman iznin budurwa da waninta ba'a aurar da ita face da izininta ) idan kuwa aka aurar da ita babu izininta auren bai inganta  ba.

shari'ar muslunci itace farkon shari'a da ta daukaka mace ta samarmata da tsari da ta kaita ga kololuwar matsayi  cikin al'umma ta tabbatar mata da dukkanin hakkokinta da wajibai, haka al'amari ya ke ga namiji , dole ga saurayi ya zamanto ya na da kwadyi ya zuwa ga aure ya zama kwadayinsa kan asalin aure kamar yadda yak e kwadayi kan macen da zai aura, ta yiwu wannan kwadayi da yake ya dace da abin da iyaye ke so, madalla da abin da ake kwadayi kansa  daga nan komai zai kasance kamar yanda ake bukatarsa, sai dai cewa cikin su iyalai akan samu sabani tsakanin zabin iyaye da zabin dansu,  iri wannan waje wanne za'a gabatar ?

عن ابن أبي يعفور ، عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : قلت  : إنّي أردت أن أتزوّج امرأة وإنّ أبوي أرادا غيرها ، قال  : تزوّج الذي هويت ودع التي هوى أبواك

 

4-daga dan abi ya'afur daga sadik (as) ya ce: na ce : hakika ni nayi niyyar auren wata mata sai mahaifana suka zaba mini wata daban, sai imam (as) ya ce : ka auri wacce kake so ka kyale wacce mahaifanka ke so,

haka na nufi da da keson rayuwa tare da matarsa zabinsa shi ne abin gabatarwa, sai da cewa ba kowanne lokaci ake gabatar da zabins ba, tayiwu wani lokaci ya rudu da soyayyar karya ta bata  idonsa ya makance ya gaza ganin hakikar al'amarin wacce ke son aura, ta yiwu kyawunta na zahiri ya yaudare shi ya ji ya na sonta halin gafala da cewa ita daga tushe mara kyawu take, manzon Allah (saw) na cewa: na haneku da furen juji, aka tambaye shi me ye furen juji ? sai ya ce: kyakkyawar mace daga mummunan tushe.

a iri wannan wuri iyaye na da hakkin sabawa wannan aure saboda kare abin da zai cutar da dansu, saboda sun san jiya sunfi shi ilimi cikin wannan kwazazzabo, saboda  haka ya kamata shi dan a irin wannan wuri ya karbi shawarar iyaye  idan ta kasance ta yi daidai da hankali, ka da ya biye ma son zuciyarsa  hakika zai bata kan hanya madaidaiciya cikin rauywarsa ta aure ya kuma rasa babbar garkuwa da jigo cikin zamantakewarsa da manyan al'amudi biyu wanda sune uwa da uba.ya zama wajibi yin shawara ta gaskiya da lura da sanya lafiyayyen hankali.

 

 

 

 

 

 

 [1] Wasa'ilul shi'a m 7 sh 206