فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI

 

rayuwar aure ta banbanta da waninta  kasantuwar Allah matsarkaki ya sanya kauna da tausayi tsakanin mata da miji, wadannan abubuwa biyu jigo ne da asasi cikin ingantar iyali, da kamalar haduwar kai da fuskantar juna da gudanar al'amura kamar yadda ake bukata, da warwarewar matsaloli da galaba kan wahalhalu  dukkanin haka albarkacin kauna soyayya tare da biyayya da tausasawa.

rayuwar da soyayya da tausasawa ke shugbanta hakika wannen rayuwa ba komai bace face rayuwar aljanna, aljanna kuma gidan hutu ne ga muminai wacce rahamar ubangiji ke kewaye da ita  da kauna madawwamiya, cikinta  babu bakin ciki  ba wahala  babu cece kuce, haka kuma gida ne wanda turaren kauna da kamshi rahama ke ta shi cikinsa.

amma tare da haka Allah ya sanya hakkoki da su ka kebantu da mazaje, kamar yadda ya sanya hakkoki da su ka kebantu ga mata , saboda kowa ya san iyakarsa, kada ya yi gangan cin ketare wannan iyakoki  saboda dagawa da zalunci  da nuna isa, akwai dokoki da ke lazimtar miji da ya zama wajibi ya kiyaye su, kamar yadda su ke kan mata, sannan akwai wadanda kuma shi da ita su kayi tarayya ciki, zamu kawo kadan daga riwayoyi, gabanin kawo riwayoyi ya kamata muyi dan bayani kan ma'anar hakki, hakika Kalmar: الحق a harshen larabaci  ta na da ma'anar tabbatacen abu, sannan kuma suna daga sunayen Allah kyawawa kamar yadda ya zo cikin fadinsa:

سَنُرِيهِمْ آيَاتِنَا فِي الآ فَاقِ وَفِي أ نْفُسِهِمْ حَتَّى يَـتَبَـيَّنَ لَهُمْ أ نَّهُ الحَقّ[1]ُ 

  da sannu zamu nuna musu ayoyin mu cikin sasanni da kawunansu har ya bayyananr musu lalle cewa shi gaskiya ne.[2]

sannan Kalmar hakku a ma'anar isdilahi shi ne cewa: abin da ya tabbata ta hanyar hankali da shari'a.

sannan a fikihu ya na dan banbanta da kasancewa shi hakki shi ne abin da tabbatuwarsa ke hannun Allah matsarkaki, sai dai cewa watsi da shi wasu lokuta na komawa hannun ma'abocin hakki, misalign hakkin zabi cikin cinikin da a kayi a mahalllin da mai siya da mai sayarwa suke tare, mai siya yana iya zabar fasa sayen kayan matukar bai bar mahallin da ya saye kayan ba.

sannan hakkokin ma'aurata  wani lokaci sukan kasancewa na shari'a, kamar yanda ake cewa bai daga hakkin miji sanya matarsa wankin  tufafi da dafa abinci  kai hatta shayar da dansa in banda shayar farko yayin da ta haifeshi, ya halasta gareta ta karbi ladan shayar masa da da, shi ma kuma namiji na da hakkin auren mata hudu, saboda haka abin da ya fi kamata shi ne yin sulhu da sassautowa kowa ya hakura da wani kaso cikin hakkinsa, mace ta dauki nauyin ayyukan gida ta yi ma mijinta hidima da dukkanin abin da ya ke so, a gefe guda shi kuma ya hakura da karo aure wannan duka cikin misali.

abin da ake nufi daga bayanin hakkokin ma'aurata  wadanda suka yi tarayya ciki da wadanda kowanne dayansu ya kebantu da na shi cikin wannan fasali ba hakkoki na shari'a ne ba kadai har da na kyawawan dabi'u da tarbiyya da mu ka fito da su daga hadisai, amma hakkokin da suka yi tarayya kai daga cikinsu:[1] Fussilat:53

[2] Fussilat:53