فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

HAKKOKIN MACE

 

mace abokiyar rayuwa ta na hakki kan mijinta kamar yanda shi ya ke da hakki kanta, wajibi kan miji ya kiyaye  hakkokinta har ya zamanto igiyar alakarsu ta aure ta samu karfafa, duk wanda ya ketare iyaka zai koma kishiya sai ya lazimta kishinyanta tsakanin mutane biyu da ke rayuwa karkashin rufi guda,  nauyi ya hau kan wuyansu na kiyaye tsarinsu da na tarbiyar iyali, kowanne daya daga ckinsu idan ya shallake iyakarsa ya ki aiki da abin da ya hau kansa daga kula da hakkin dan'uwan tarayyarsa a aure, lalle babu shakka zai kai ga lalacewar rayuwarsu ta tarayya, sannan ya zama sunyi asarar `ya`yansu, da afkar da radadi ga kawukansu kai har ma da makusantansu, ta yiwu ya kai ga zubar da jini  da keta alfarma  da rushewar al'umma da lalacewarta,

da farko ya zama wajibi miji ya yi mu'amala da matarsa da iyalinsa cikin kauna  da tausasawa, sannan ya kiyaye hakkokin matarsa cikin kyautatawa da tausasawa, ya   yi koyi da annabawan Allah da cika makinsu manzon Allah (saw) da zuriyarsa tsarkaka.

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : خيركم خيركم لأهله ، وأنا خيركم لأهلي

manzon Allah (saw) ya ce: mafi alheri cikinku shi ne wanda ya kasance alheri ga iyalansa, ni ne mafi alherin cikinku saboda kasantuwa alheri ga iyalina.

haka na nufin  cewa miji  ya kamata ya kasance daga ma'abot alheri,   ayyukan suna da yawn gaske alheri, dukkanin mai hankali bai jahilce su ba, sannan mafi kusa da jibantawa alheri su ne makusantanka, mafi kusa gareka sune mahaifanka sannan matarka.

manzon Allah (saw) ya buga mafi kyawun misali cikin rayuwarsa a wannan babi, haka imamai tsarkaka  (as) hakika rayuwarsu fitila ce mai haske  cikin hanyar arziki  da rayuwa mani'imciya, kalmominsu na haske da ke dauke da ilimi da wayewa ga wanda ke son ya rayu cikin arziki da mutuwa cikin arziki, hakika sun yi bayanin hakkoki da iyakoki  cikin kowanne abu, me ya fi kyawu daga abin da imam sajjad (as) ya fadi : cikin risalarsa ta hakkoki: mutum tare da ubangijinsa, tare da kansa, tare da waninsa.

وفي حقّ الزوجة يقول (عليه السلام) بما هو الجامع والأساس لكلّ الحقوق الزوجية  : وأمّا حقّ الزوجة  : فأن تعلم أنّ الله عزّ وجلّ جعلها لك سكناً واُنساً ، فتعلم أنّ ذلك نعمة من الله عليك ، فتكرمها وترفق بها ، وإن كان حقّك عليها أوجب فإنّ لها عليك أن ترحمها لأ نّها أسيرك وتطعمها وتسقيها وتكسوها ، وإذا جهلت عفوت عنها .

1- imam sajjad (as) ya na cewa: kan hakkin matarka, amma hakkin matarka : shi ne ka san cewa lalle Allah mai girma da daukaka ya sanya ta nutsuwa da debe haso gareka, ka san cewa hakan ni'ima ce kanka, sai ka girmamata ka tausaya mata, duk da cewa hakkinka da ke kanta yafi zama wajabi, lalle ta na hakki kanka da ka tausaya mata saboda ta zama daurarriyarka wajibi ka ciyar da ita ka shayar da ita  ka kuma tufatar da ita, idan ta zoma da jahilci kayi mata afuwa.

me ya fi kyawu daga wadannan ka'idoji da asalai na farin cikin rayuwar aure: da farko kasancewa Allah madaukaki ya sanya ta nutsuwa gareka, haka na nufin ka samu yakini kan cewa manufar aure  shi ne samun nutsuwa  da hutu, hakan na tabbatuwa ta hanyar kusantuwa da matarka, kamar yadda mutum ke samun hutu da nutsuwa cikin gidan da ya ka zaune, to wajibi kansa ya yi kai kawo wajen gyara shi  da gina shi da yi masa ado, to haka al'amarin ya ke cikin matar da ka ke aure,  ya zama dole ka lallabata  ka kaucewa dukkanin abin da zai bata mata rai, ka yi kai kawo wajen gyaranta  da abin da ya ke maslaha gareta.

na biyu: debe haso: ta yiwu ka samu wanda ka ke nutsuwa da shi amma ba ka samun debe haso ta hanyarsa, sai imam (as) ya jinginawa nutsuwa debe haso na jiki da ruhi kamar yadda Allah ya jinginawa sanyi da aminci cikin wutar namarudu  ga ibarhim (as) ba da ban lafiya ta kasance ba ta yiwu sanyin ya kasance mai tsanani wanda zai iya kaiwa ga halaka, ubangiji na cewa:

كُونِي بَرْداً وَسَلاما[1] 

 ya ke wuta ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahim.

na uku : kasan cewa hakan ni'ima ce daga Allah gareka, macen da ka ke samun nutsuwa ya zuwa gareta da debe haso da ita da samun kaunarta wannan ni'ima ce daga Allah, haka al'amarin ya ke dangane ga mace hakika miji nagari na daga cikin ni'imar Allah gareta, hakkin ni'ima shi ne nuna godiya.

na hudu: ka karammata: imam ya bayyana cewa godiya kan wannan ni'imar shi ne  ka karrama matarka da dukkanin abin da ke daukar ma'anar karramawa, daga karramawa shi ne tausasawa da nuna kauna  da kyawunta mu'amala tsakaninka da ita.

na biyar: tausayi: tausaya mata cikin kalami da yafiya da soyayya, ka zama abokinta mai tausaya mata cikin tafiya da  zamanka gida sai ka kiyaye ladubban abokantaka da makwabtaka ka da ka dinga tabo dukkanin abin da zai jawo bacin ranta.

na shida: duk da cewa hakkinka ya fi zama wajibi  kanta yayin da ka ke amfani da wadannan hanyoyi da dabaru da tausasawa ka da kayi tunanin cewa hakkinta ya fi na ka yawa, namiji ya fi mace yawan hakkoki, sai dai cewa yawan hakkoki  da ba'arin  fifiko  na cikin al'umma bisa la'akari da kasantuwarsa namiji bai nufi cewa namiji ya takewa mace hakkinta da yin alfahari kanta, abin da zai iya kaiwa ga munanawa da rigima, ya kuma sanya ta neman hakkinta daga gare shi, duk da cewa ka fita yawan hakkoki bai nufin ka kauracewa tausasa mata, saboda mace na hakkin kan namiji da ya tausaya mata, hujja kan haka shi ne ita daurarriyar gidanka ce tana cikin igiyar aurenka, kuma wanda aka daure ya na bukatar binsa sannu a hankali  da tausasawa  har ya kai ga ka farauci zuciyarsa, amma ta fuskanin tattalin arziki da batutuwan zahiri, to daga hakkokinta  kanka:

na bakwai ciyarwa, shayarwa, tufatarwa,  wadannan al'amura  na karkashin abin da ake kira nafaka (ciyarwa ) yayin da ciyar da ita ke wajaba kan mijinta da abin da ya da ce da ita  cikin gidan da tabaro na mahaifana, wajibi kan mijinta ya kiyaye wannan al'amari.

na takwas : idan ta zo maka da jahilci ka yi mata afuwa:  babu shakka idan afuwa da kau da kai ta shiga cikin rayuwar aure ba makawa rayuwa za ta kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali, jahilci ya canja zuwa ilimi, kiyayya ta juya zuwa abota da kauna.

abin mamaki duk da kasantuwa karya ta haramta ta kuma kasance cikin munana siffofi, sai dai cewa saboda kare tsarin iyali wani lokaci mace kan neman abin da mijinta bai da iko kai, to a irin wannan lokaci ya halasta ya yi mata alkawari zai saya mataabin da ta bukata, amma idan ya dawo gida kawai saiya nuna ya manta da wancan alkawari.

الإمام الصادق عن آبائه ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : ثلاثة يحسن فيهن الكذب  : المكيدة في الحرب ، وعدتك زوجتك ، والإصلاح بين الناس[2]

hakika ya zo cikin hadisi daga imam sadik (as) daga babanninsa, ya ce : manzon Allah (saw) ya ce :  karya ta kyawunta cikin abubuwa uku : shirya kaidi cikin yaki , cikin alkawarin da kayiwa matarka  , cikin sulhunta tsakanin mutane.

hakkokinta cikin abubuwan da za su zo kamar haka:

mijinta ya yafe mata  yayin da ta aikata masa kuskure, ta yiwu saboda karancin gogewa ko duhun kai da jahilci ya sanya ta ke cutar da mijinta, shi kuma ya kamata ya yi mata afuwa musammam idan ta nemi hakan.

سأل إسحاق بن عمّـار أبا عبد الله (عليه السلام) عن حقّ المرأة على زوجها  ؟ قال  : يشبع بطنها ، ويكسو جثّتها ، وإن جهلت غفر لها ـ  أي عليها أوّلا أن لا تجهل

5 – is'hak dan ammar ya tambayi baban Abdullah (as) kan hakkin mace kan mijinta ? sai ya ce: ya kosar da cikinta, ya tufatar da jikinta idan ta zo masa da jahilci ya gafarta mata, sannan ita kuma ta kauracewa aikata jahilcin.

إنّ إبراهيم خليل الرحمن (عليه السلام) شكا إلى الله عزّ وجلّ خُلق سارة ، فأوحى الله إليه أنّ مثل المرأة مثل الضلع ، إن أقمته انكسر ، وإن تركته استمتعت به ، قلت  : من قال هذا  ؟ فغضب ، ثمّ قال  : هذا والله قول رسول الله (صلى الله عليه وآله) ، وعنه قال  : كان لأبي  عبد الله (عليه السلام) امرأة وكانت تؤذيه فكان يغفر لها

6 hakika annabi Ibrahim (as) ya kaiwa Allah kukan halayyar matasra saratu, sai Allah ya yi wahayi zuwa gare shi cewa misalin mace misalin kashin awaga ne, idan ka ce sai ka mikar da shi sai ya karye, idan kuma ka kyaleshi sai ka ji dadinka da shi, sai na ce waye ya fadi haka ? sai imam ya fusata,  ya ce wallahi fadin manzon Allah (saw) haka ma an karbo daga gare shi ya ce: baban abdullah ya kasance ya na da wata kuyanga ta na cutar da shi amma kuma shi ya na gafarta mata.

daga cikin kyawawan siffofi, bari ma ana kidaita shi  cikin jagaba kyawawan dabi'u,  asasin dukkanin dabi'a shi ne hakuri , mumini shi ne mai yawan hakuri da natsuwa yayin musibu masu girgizarwa, hakurin  mumini nayin tajalli tare da matarsa  ko da kuwa ta kasance ma'abociyar miyagun halayya, lalle shi ya na gafarta mata sakamakon jahilcinta, kai ya na jurewa cutarwarta musammam cikin munanan kalmarnta da mu'amalarta mara kyawu, mai ya fi girma daga ladan wanda ya rungumi wannan hakuri.

قال (عليه السلام)  : من احتمل من امرأته ولو كلمة واحدة ، أعتق الله رقبته من النار ، وأوجب له الجنّة ، وكتب له مائتي ألف حسنة ، ومحا عنه مئتي ألف سيّئة ، ورفع له مائتي ألف درجة ، وكتب الله عزّ وجلّ له بكلّ شعرة على بدنه عبادة سنة

7 Imam (as) ya ce: duk wanda ya jurewa wani abu mara kyawu daga matarsa ko da kuwa kalma ce guda daya, Allah zai `yanta wuyansa dga wuta, ya bashi aljanna, ya rubuta masa kywawan ayyuka dubu dari biyu , ya goge masa munana ayyuka dubu dari biyu, ya daga masa daraja dubu dari biyu, ya rubuta masa lbadar shekara ga dukkanin silin gashin jikinsa.

da misalin wannan lada mai girma ta kaka mumini ba zai jurewa cutarwa matarsa ba  , ta kaka rayuwarsa ba za ta kasance cikin arziki da farin ciki ba, duk yadda mace takai cikin jahilci ta na da hankali da tausayi  , idan ta fahimci yadda mijinta ke hakuri da ita , to wata rana za ta gane cewa abubuwan da ta ke bai da ce kuma kuskure ne , sannan za ta yi kokarin ganin ba maimaita haka nan gaba , za ta canja da yi masa mu'amala da kyautatawa ta kame daga cutar da shi , za ta fuskanci kimar miji mai hakuri da jurewa ba za ta nemi sauyinsa da duniya da abin da ke cikinta ba.[1]anbiya:69

[2]Biharul anwar m 100 sh 242