فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA

 

dole ne da farko mai kula da gida ya zamato ya na da tarbiyya ya kasance mumini mai kula da addininsa mai riko da karfaffiya igiyar Allah, mai sauki farillansa na ibada da mu'amala, da kauracewa dukkanin abubuwan da suka haramta kai hatta makaruhi, misalin irin wannan uba da ya yi nasara zai iya kasance malami na farko cikin iyali, za a dinka karkata da koyi da kyawawan dabi'unsa a fade da aikace, kamar yadda zai zamanto mai nasiha da wa'azi, kowanne lokaci ya na mai yiwa matars da `ya`yansa nasiha da koyar da su littafi da hikima, da shiryar da su ya zuwa tafarki da hanya mikakka, tayiwu yanayi ya hana damar tabbatar da abin da ya ke son tabbatarwa, kamar yanda muhallin da ya ke zaune na da tasiri kan mata da `ya`ya, na daga abin da ke haifar da kuncin rayuwa da tsanani har ya kai ga mutum na gudun matarsa da `ya`yansa wani lokacin ya kai ga rasa hayyaci da hankula kaga mutum ya kauce ma hanyar shiriya, sai kaga ya na biyewa matarsa cikin sabon Allah, Allah ka tsaremu daga aikata haka , babbar musifa ma shi ne idan matar ta kasance saliha ko `ya`yanta shi kuma uban ya zama gurbatacce batacce daga hanyar shiriya, misali ya kasance matarsa ta na kula da ibada `ya`yansa na sAllah cikin jama'a da kula da dukkanin ibada  amma kuma shi uban ba ya sallah ya na kuma shan giya  da aikata manya manya zunubai, to a irin wannan lokaci ne matsala babba za ta afku cikin gida, rigima tayi tsanani tsakanin karya da gaskiya, da yawan lokuta za ka samu anyi asarar hakkoki al'amari ya rikice, Allah ne kadai wajen kai kuka.

19 an karbo daga baban abdullah (as) ya ce: yayin da wannan aya ta sauko:

يَا أ يُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا قُوا أنفُسَكُمْ وَأهْلِيكُمْ نَار[1]اً 

  ya ku wadanda suka yi imani ku ceci kawukanku da iyalinku daga wuta.

 sai wani daga cikin musulmi ya zauna ya dinga rusa kuka ya na cewa ni yanzu da gaza ceton kaina gashi kuma an kallafa mini ceton iyalina, sai manzon Allah (saw) ya ce: ya isar maka ka umarce su da abin da kake umartar kanka ka hane su da abin da ka ke hana kanka.

عن النبيّ (صلى الله عليه وآله) ، قال  : عظوهن بالمعروف قبل أن يأمرنكم بالمنكر

 annabi (saw) ya ce: ku yi musu wa'azi da alheri gabanin su fara umartarku da munkari

daga cikin alheri shi ne ku hana fajircin da ke gidajenku kamar yadda ya zo cikin hadisi:

‏‏قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : أيّما رجل رأى في منزله شيئاً من الفجور فلم يغيّر بعث الله تعالى طيراً أبيض يظلّ عليه أربعين صباحاً فيقول كلّما دخل وخرج  : غيّر غيّر ، فإن غيّر وإلاّ مسح رأسه بجناحيه على عينيه ، فإن رأى حسناً لم يستحسنه ، وإن يرى قبيحاً لم ينكره[2] . فيكون بحكم الأنعام بل أضلّ سبيلا .

20 manzon Allah (saw) ya ce: duk mutumin da ya ga wani abu daga fajirci cikin gidansa bai canja shi ba Allah zai aiko da wani tsuntsu fari a kansa ya wanzu har tsawon asubahi arba'in, duk sanda wannan mutumin ya fito daga gida ko ya shiga sai tsuntsun ya dinga cewa ka canja ka canja, idan ya canja idan kuma bai canja ba sai ya dinga shafa fuffukensa kan  idanun mutumin, idan ya ga kyakkyawa bai gani kyawunsa, idan ya ga mummuna ba zai inkarinsa ba.

 sai ya zamanto cikin hukuncin dabbobi ko ma ya fi dabbobi batan hanya.

mahaifi da mahifiya haka suke suna umartar `ya`yayensu da alheri da hana su  mummuna, kamar yadda ubangiji ke fadi:

وَأمُرْ أهْلَكَ بِالصَّلاة[3]   

ka umarci iyalinka da sallah.

 [1] Tahrim:

[2] Bihar anwar m 100 sh 251

[3] Daha:123