فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

HAKKOKIN MIJI

                              

amma hakkokin miji kan matarsa:

1- tsantsar biyayya: lalle ya zama tilas mace ta yi biyayya ga mijinta matukar bai umarceta da aikata haramun ba, kamar barin sallar wajibi  ko shangiya da dai misalin haka, duk da cewar kurewar biyayya shi ne sujjada, saboda haka ne ma bai inganta yin sujjada ga wanin Allah, sai dai cewa ya zo a hadisi cewa:

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : إنّ قوماً أتوا رسول الله (صلى الله عليه وآله) فقالوا  : يا رسول الله ، إنّا رأينا اُناساً يسجد بعضهم لبعض ، فقال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : لو كنت آمر أحداً أن يسجد لأحد لأمرت المرأة أن تسجد لزوجها

1 an karbo daga imam sadik (as) ya ce: wasu mutane sun zo wajen manzon Allah (saw) sai suka ce masa munga wasu mutane sashensu na yiwa daya sashen sujjada, sai manzon Allah (saw) ya ce: da na kasance ina umarta wani ya yiwa wani sujjada da na umarci mace  ta yiwa mijinta sujjada.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : لو أنّ امرأة وضعت إحدى ثدييها طبيخة ـ  كناية عن غاية الفداء والتضحية  ـ والآخر مشوية ، ما أدّت حقّ زوجها ، ولو أ نّها عصت مع ذلك زوجها طرفة عين اُلقيت في الدرك الأسفل من النار ، إلاّ أن تتوب وترجع

2 – a wani wajen kuma ya ce: da ace mace za ta dafa nononta daya ta gasa dayan, don sadukarwa ga mijnta da haryanzu ba ta iya sauken nauyin mijinta ba, da kuma tare da haka za ta sabawa mijinta ko da kuwa gwargwadon kiftawar ido ne  da an wurga ta cikin kasan wuta, har sai idan ta tuba ta koma gare shi.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : حقّ الزوج على الزوجة  : ... أن تطيعه ولا تعصيه  

3 – hakkin miji kan matarsa shi ne ta yi masa biyayya ka da ta saba masa.

وقالت خولة ـ  وخولة جماعة من الصحابيات تسمّى بهذا الاسم ، ولعلّ المراد بها هنا هي خولة بنت عاصم زوجة هلال بن اُميّة التي لاعنها ففرّق النبيّ بينهما  ـ  ، قالت لرسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إنّي أتعطّر لزوجي كأ نّي عروس اُزفّ إليه ـ  وهذا يدلّ أنّ على المرأة أن تتعطّر دائماً لزوجها لا سيّما في الليل  ـ فآتيه في لحافه فيولّي عنّي ، ثمّ آتيه من قبل وجهه فيولّي عنّي ، فأراه قد أبغضني يا رسول الله  ؟ فماذا تأمرني  ؟ قال  : اتّقي الله وأطيعي زوجكِ

4 – kaulatu ta cewa manzon Allah (saw) lalle ni ina sanyawa mijina turare kai kace sabuwar amarya da za akai dakin miji, sai inje masa cikin mayafinsa na lulluba sai ya juya mini baya sai inje masa ta barin fuskarsa nan ma ya juya mini baya, sai na ke tsammani ko dai kina ya ke ya manzon Allah ? me kake umarta ta ? sai ya ce mata: kiji tsoron Allah ka da ki sabawa mijinki.

عن عليّ ، عن الإمام الكاظم (عليه السلام) ، قال  : سألته عن المرأة العاصية لزوجها هل لها صلاة وما حالها  ؟ قال  : لا تزال عاصية حتّى يرضى عنها[1]

5- an karbo daga aliyu, daga imam kazim (as) ya ce: na tambaye shi kan matar da ke sabawa mijinta, shin ta na da sallah ya sallarta ta ke ? sai ya ce ba ta gushewa mai sabo har sai mijinta ya yarda da ita.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : ملعونة ملعونة امرأة تؤذي زوجها وتغمّه ، وسعيدة سعيدة امرأة تكرم زوجها ولا تؤذيه ، وتطيعه في جميع أحواله[2]

 6 – an karbo daga baba abdullah (as) ya ce: tsinanniya tsinanniya itace matar da ke cutar da mijinta da bakanta masa, mai arziki mai arziki itace matar da ta ke karrama mijinta sannan kuma ba ta cutar da shi ta na kuma yi masa biyayya cikin kowanne yanayi.

ـ الكافي بسنده عن أبي جعفر (عليه السلام) قال  : خرج رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) يوم النحر ـ  أي يوم عيد الأضحى  ـ إلى ظهر المدينة على جمل عاري الجسم فمرّ بالنساء  فوقف عليهن ، ثمّ قال  : يا معاشر النساء تصدّقن وأطعن أزواجكن فإنّ أكثركنّ في النار ، فلمّا سمعن ذلك بكين ، ثمّ قامت إليه امرأة منهنّ ، فقالت  : يا  رسول الله في النار مع الكفّار  ؟  ! والله ما نحن بكفّار فنكون من أهل النار ، فقال لها رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إنّكن كافرات بحقّ أزواجكن[3]

7 – alkafi da isnadinsa daga baba jafar (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya fito tsakiyar madina  ranar idin babbar sallah kan rakumi wandajikinsa ya kasance tsirara babu shimfida kansa , sai ya wuce ta gefen wasu mata  sai ya tsaya kansu, sannan ya ce: ya ku taron mata ku yi sadaka ku bi mazajenku, lalle mafi yawancinku `yan wuta ne, yayin da suka ji haka sai suka rushe da kuka, sai daya daga cikinsu ta mike ta ce: ya manzon Allah shin yanzu mafi yawa daga cikin mu na cikin wuta tare da kafirai ? wallahi mu ba kafirai ba ne da har za mu kasance daga `yan wuta, sai manzon Allah (saw) ya ce mata: lalle ku kun kafircewa hakkin mazajenku.

Kafirci yakan zuwa da ma'ana biyu: wani lokacin kafircin akida wanda ke kawo najastuwa ma'abocinsa da shiga wuta, wani kuma da ma'anar kafircewa cikin aiki  kamar mai barin sAllah ba ya yinta, ko wanda ya bar zuwa aikin hajji da gangan, matar da ba ta biyayya ga mijinta kafira ce kafircin aiki ba na akida ba.

الفقيه بسنده عن أبي بصير قال  : سمعت أبا عبد الله (عليه السلام) يقول  : خطب رسول الله (صلى الله عليه وآله) النساء فقال  : يا معاشر النساء تصدّقن ولو من حليتكن ولو بتمرة ولو بشقّ تمرة ، فإنّ أكثركنّ حطب جهنّم ، إنّكن تكثرن اللعن وتكفّرن العشير ـ  أي الزوج  ـ فقالت امرأة من بني سليم لها عقل ـ  أي ذكيّة وفاهمة وتعقل الاُمور جيّداً  ـ يا رسول الله أليس نحن الاُمّهات الحاملات المرضعات ، أليس منّا البنات القيّمات والأخوات المشفقات ، فرقّ لها رسول الله (صلى الله عليه وآله) فقال  : حاملات والدات مرضعات رحيمات ، لولا ما يأتين إلى بعولتهن ما دخلت مصلّية منهنّ النار

8 – alfakihu da isnadinsa an karbo daga babab basiru, ya ce: na ji baban Abdullah (as)  ya na cewa: manzon Allah (saw) ya yi wata huduba sai ya ce: yaku mata kuyi sadaka ko da kuwa da kayan adonku ne ko kuma da dabino ko da gutsirin dabino, lalle mafi yawanku makamashin jahannama ne, lalle ku dinnan kuna da yawan tsinuwa da kafircewa miji  - sai wata mata daga kabilar salim mai kaifin basira ta ce: ya manzon Allah (saw) ashe ba mune iyaye masu dauke da ciki da shayarwa ba, ashe cikin mu babu `ya`ya` mata  tsayayyu masu tausayi, sai manzon Allah (saw) ya tausaya mata ya ce: masu dauke da ciki da shayarwa masu nuna jin kai, ba don abin da suke yiwa mazajensu ba da babu wata mai sallah dga cikinsu da za ta shiga wuta.[1] Biharul anwar m 100 sh 244

[2] Biharul anwar m 100 sh 253

[3] Alkafi m 5 sh 514