فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI

 

Daga cikin abubuwan da ke lazimtar biyayya  shi ne kasancewa ta na neman izinin mijinta cikinta dukkaninta motsinta da ayyukanta hatta ibada idan ta kasance ta mustahabbi, lalle yardar Allah na cikin yardarm miji, idan ya zamanto bai yardar mata ayyukan mustahabbi ba to sun haramta gareta.

روى الحسن بن محبوب ، عن مالك بن عطية ، عن محمّد بن مسلم ، عن الباقر (عليه السلام) ، قال  : جاءت امرأة إلى رسول الله (صلى الله عليه وآله) فقالت  : يا رسول الله ، ما حقّ الزوج على المرأة  ؟ فقال لها  : أن تطيعه ولا تعصيه ، ولا تتصدّق من بيتها بشيء إلاّ بإذنه ، ولا تصوم تطوّعاً إلاّ بإذنه ، ولا تمنعه نفسها وإن كانت على ظهر قتب ـ  أي الراحلة وهذا كناية عن شدّة استجابتها لطلب زوجها المقاربة والعمل الجنسي  ـ ولا تخرج من بيتها إلاّ بإذنه ، فإن خرجت بغير إذنه لعنتها ملائكة السماء وملائكة الأرض وملائكة الغضب وملائكة الرحمة حتّى ترجع إلى بيتها ، فقالت  : يا رسول الله ، من أعظم الناس حقّاً على الرجل  ؟ قال  : والداه ، قالت  : فمن أعظم الناس حقّاً على المرأة  ؟ قال  : زوجها ، وقالت  : فما لي عليه من الحقّ مثل ما له عليّ  ؟ قال  : لا ، ولا من كلّ مائة واحدة . فقالت  : والذي بعثك بالحقّ لا يملك رقبتي رجل أبداً

9 – hassan dan mahbub ya rawaito daga malik  dan adiyyatu  daga muhammadu dan muslim daga bakir (as) ya ce: wata mata ta je wajen manzon Allah (saw) sai ta ce masa: ya manzon Allah (saw) me ye hakkin miji kan matarsa ? sai ya ce mata: ta yi biyayya gare shi ka da ta saba masa, sannan ka da ta sake ta yi sadakar wani abu daga gidanta face da izininsa, ka da ta yi azumin mustahabbi face da izininsa, ka da ta yi masa rowar kanta koda kuwa ta na kan gadon bayan rakumi, ka da ta fita daga gida face da izininsa, idan ta fita babu izininsa mala'lkun sama da kasa da mala'ikun fushi da mala'ikun rahama za suyi ta tsine mata har ta dawo gida, sai ta ce: waye ya fi girman hakki cikin mutane kan namiji ? sai ya ce: iyayensa   sai ta kara cewa waye ya fi girman hakki cikin mutane kan mace ? sai ya ce: mijinta, sai ta ce: wanne hakki na ke da shi kansa misalin wanda ya ke da shi a kaina?   sai ya ce: babu ko da kuwa guda daya daga cikin dukkanin dari, sai ta ce: na rantse da wanda ya aiko ka da gaskiya namiji ba zai taba mallakar wuyana ba har abada.

Wannan ishara ce zuwa ga rashin ikon kan sauke wadannan hakkoki sai ta ga abin da ya fiye mata alheri ta kyale yin aure, sai dai cewa wannan hakkoki ana iya sarayar da su, da ace mace mai tsarkin niyya za ta kuduri cewa za ta yiwa mijinta biyayya cikin kowanne irin hali lalle ubangiji zai taimake kan sauke hakkin mijinta. duk sanda ta aikata wani abu da ya sosa zuciyar mijinta to cikin gaggawa ta je ta nemi uzuri gurinsa, shi kuma mijin sai ya duba ya yiwa Allah godiya kan samun irin wannan mata, wacce ake kidaya ta daga ni'imomin Allah masu girma da ya yi masa.

كما ورد في قوله تعالى  : (  رَبَّـنَا آتِنَا فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِي الآخِرَةِ حَسَنَةً وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ[1]   ، عن أمير المؤمنين (عليه السلام)

)  : الحسنة في الدنيا المرأة الصالحة المطيعة ، وعذاب النار المرأة سيّئة الخلق

10- kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki:

 

 ubangijinmu ka bamu kyakkyawa cikin duniya da lahira ka tseratar da mu daga azabar wuta.2

 kyakkyawa cikin duniya ita ce mace saliha kamar yadda sarkin muminai ali (as) ya fadi.

 عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : أ يّما امرأة خرجت من  بيتها بغير إذن زوجها فلا نفقة لها حتّى ترجع ـ  أي تكون المرأة ناشزاً حينئذ ولا يجب على الزوج نفقتها كما أفتى بذلك الفقهاء 

11-an karbo daga sadik (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: dukkanin matar da ta fito daga gida ba tare da izinin mijinta ba, ba ta da hakkin ciyarwa har sai ta dawo gida, ma'ana za kirga daga masu bijirewa miji, kan haka ne malaman fikihu suka yi fatawa kan rashin wajabcin ciyar da ita.

وفي رواية عن أنس ، قال  : خرج رجل غازياً في سبيل الله ، وأوصى امرأته أن لا تنزل من فوق بيته إلى حين يقدم ، وكان والدها في الأسفل فاشتكى ـ  أي مرض والدها وهو في الحجرة التحتانية ، فبين البنت والوالد سقف كما هو الظاهر  ـ فأرسلت إلى رسول الله (صلى الله عليه وآله) تخبره وتستأمره ـ  أي ماذا يأمرها النبيّ  ـ فأرسل إليها أن اتّقِ الله وأطيعي زوجك  

12 – daga anas ya ce: wani mutum ya fito yaki cikin tafarkin Allah,  ya yiwa matarsa wasiyya da ka da ta sauko kasa daga saman gidansa har sai ya dawo, babanta ya kasance kasan gidan sai rashin lafiya ta kama shi, sai ta aika wajen manzon Allah (saw) ta na neman umarninsa kan wanne mataki zata dauka cikin wannan hali, sai manzon Allah (saw) ya aiko mata da cewa ta ji tsoron Allah ta bi umarnin mijinta.

وعنه (صلى الله عليه وآله) ، قال  : إنّ رجلا من الأنصار على عهد رسول الله (صلى الله عليه وآله) خرج في بعض حوائجه وعهد إلى امرأته عهداً أن لا تخرج من بيتها حتّى يقدم ، قال  : وإن أباها مرض ، فبعثت المرأة إلى رسول الله (صلى الله عليه وآله) فقالت  : إنّ زوجي خرج وعهد  إليّ أن لا أخرج من بيتي حتّى يقدم ، وإنّ أبي مرض أفتأمرني أن أعوده  ؟ فقال (صلى الله عليه وآله)  : لا ، اجلسي في بيتكِ وأطيعي زوجكِ . قال  : فمات ، فبعثت إليه فقالت  : يا رسول الله ، إنّ أبي قد مات فتأمرني أن أحضره  ؟ فقال (صلى الله عليه وآله)  : لا ، اجلسي في بيتك وأطيعي زوجكِ ، قال  : فدفن الرجل  فبعث إليها رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إنّ الله تبارك وتعالى قد غفر لك ولأبيكِ بطاعتكِ لزوج

13 -  imam (as) ya ce: wani mutum daga matanen madina a zamanin manzon Allah (saw) ya fito saboda wasu bukatunsa ya kuma ga yawa matarsa ka da ta sake ta fito daga gidanta har sai ya dawo, ya ce : sai babanta ya kamu da rashin lafiya, sai ta aikawa manzon Allah (saw) ta na ma ice masa babana bai da lafiya gashi mijina ya dora mini alkawali da ka da insake in fita hai sai ya dawo, shin ka bani umarni da in fita in ziyarci mahaifina ? sai manzon Allah (saw) ya ce: a'a ki zauna gida ki bi mijinki, sai wannan mahaifin na ta ya mutu, sai ta kara aikawa manzon Allah (saw) ta namai cewa babana ya  mutu, shin ka na umarta ta da halartar jana'izarsa ? sai manzon Allah (saw) ya ce : a'a ki zauna gida ki bi mijinki, sai aka binnne wannan mahaifi na ta, sai manzon Allah (saw) ya aika mata  da cewa lalle Allah madaukaki ya yiwa mahifinki gafara albarkacin biyyyarki ga mijinki.

في حديث ، سألت خولة رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : فما حقّه ـ  الزوج  ـ عليّ  ؟ قال  : حقّه عليكِ أن لا تخرجي من بيته إلاّ بإذنه ، ولا تصومي تطوّعاً إلاّ بإذنه ، ولا تتصدّقي من بيته إلاّ بإذنه ، وإن دعاكِ على ظهر قتب تجيبه

 14 – cikin wani hadisi kaulatu ta tambayi manzon Allah (saw) me ye hakkin miji kaina ? sai ya ce : hakkinsa kanki shi ne ka da ki fita daga gida face da izininsa, ka da kiyi azumin mustahabbi face da izininsa, ka da kiyi sadaka daga gidanki face izininsa, idan ya bukace ki ko da kuwa ki na kan doki to ki amsa masa.

ونهى النبيّ (صلى الله عليه وآله) أن تخرج المرأة من بيتها بغير إذن زوجها ، فإن خرجت لعنها كلّ ملك في السماء وكلّ شيء تمرّ عليه من الجنّ والإنس حتّى ترجع إلى بيتها  

manzon Allah (saw) ya hana mace fita daga gida ba tare da izinin mijinta ba, idan kuma ta fita mala'ikun sama da na kasa da mutane da aljannu za suyi ta tsine mata har sai ta dawo gida.

sannan ya hana mace yin ado ga wanin mijinta, idan ko ta yi Allah na da hakkin konata da wuta.

haka ma ya hana mace yin magana da wanda ba mijinta ba kuma ba muharraminta ba fiye da kalmomi biyar idan yin maganar da shi ya kasance larura.

 Sai dai cewa abin da ake nufi hani  anan ma'anar shi ne karhanci.

قال رسول الله  : أربعة لا تقبل لهم صلاة  : ... والمرأة تخرج من بيت زوجها بغير إذنه

15 – manzon Allah (saw) ya ce: mutane hudu ba'a karbar sallarsu daya daga cikinsu ita ce matar da ke fita daga gidan mijinta babu izininsa.

سأل عليّ بن جعفر أخاه موسى بن جعفر (عليه السلام)  : عن المرأة لها أن تخرج من بيت زوجها بغير إذنه . قال  : لا . وسأله عن المرأة هل لها أن تعطي من بيت زوجها بغير إذنه  ؟ قال  : لا إلاّ أن يحلّها

16 – aliyu dan jafar ya tamabayi dan uwansa musa dan jafar (as) gameda cewa shin mace na da hakkin fita daga gidn mijinta ba tare da izininsa ba, sai ya ce: a'a sai dai idan ya halasta mata hakan.

Mace ba ta da hakkin amfani da kudin mijinta cikin abin da bai yarda ba, sai dai cewa idan ta san cewa ba zai hana ta ba daga gwargwadon da tayi amfani da su to ya halasta gareta ta yi sadaka.

 [1] Bakara: 201.  Tafsir Abdullah shubbar