فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

JIMA'I

 

yayin da mu ke komawa ga ayoyi da riwayoyi masu daraja zamu samu karfafawa kan batun jima'i da ladubbansa, lalle ne cewa jima'I na daga rukunai na tushe cikin rayuwar aure daga abin da ke garemu daga hikimomi cikin wannan babi, daga wanzuwa nau'in dan adam , da kyawuntar duniyar iyali da kosar da halittar jinsi da dai wasu bukatu daban.

kai ka ce anfi kallon bangaren mazantaka fiye da bangaren mata cikin wannan fage, mai yiwa saboda namiji shi ke dauke da maniyyi da kuma kasantuwar ya fi budewa kan mace kasantuwar tsananin kunyarta, namiji na iya neman kusanta matarsa  cikin kowanne lokaci da kowanne hali face kwanakin jinin haila, kai hatta lokutan haila na iya kusantarta sai dai banda shiga farjinta.

yayin da mu ke duban harshen riwaya mutum zai sha mamaki kan wajabci gaggawar amsawa bukatarsa kan matarsa, ba ta da hakkin kin amsawa bukatarsa ko da kuwa ta na kan rakumi, ko kuma jirgin kasa da mota matukar wani ba zai gansu ba.

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : إنّ امرأةً أتت رسول الله (صلى الله عليه وآله) لبعض الحاجة ، فقال لها  : لعلّك من المسوّفات ـ  وكأ نّما النبيّ هو يتعرّض بها ليعلّمها ما يجب عليها  ـ فقالت  : يا رسول الله ، وما المسوّفات  ؟ فقال  : المرأة يدعوها زوجها لبعض الحاجة فلا تزال تسوّفه حتّى تنقضي حاجة زوجها فينام ، فتلك لا تزال الملائكة تلعنها حتّى يستيقظ زوجه

21 – an karbo daga imam sadik (as) ya ce: wata mata ta zo wajen manzon Allah (saw) kan sashen bukatarta, sai ya ce mata: me yiwuwa ke kina cikin mata masu yanga ? sai tace wadanne mata ne masu yanga ? sai ya ce : macen da mijinta ke kiranta kan wata bukatarsa ba zata gushe ba ta na ja masa rai da yanga har sai sha'awarsa ta tafi ya yi barci, to wannan mata mala'iku ba za su gushe ba suna tsine mata har zuwa lokacin da mijinta ya tashi daga barci.

عن رسول الله (صلى الله عليه وآله) في حديث  : من حقّ الزوج ... وإن دعاكِ على قتب ـ  ظهر الجمل  ـ تجيبيه

22 –  manzon Allah (saw) daga cikin hakkin miji kan matarsa idan ya kirata ta amsa masa ko da kuwa ta na kan rakumi

23 – daga cikin nauyi da ya hau kan mace cikin daren da mijinta zai kusanceta shi ne ta aikata abin da manzon Allah (saw) ya sunnata mata cikin fadinsa: bai halasta ga mace ba ta yi barci har sai ta bijiro da kanta ga mijinta, ta kwabe tufafinta ta shiga mayafinsa ta jingina fatarta da fatarsa, idan ta aikata haka to tabbas ta bijiro masa da kanta.

Sananne ala'amari ne cewa jingina fata da fata na kawo dumamar jiki sai ka ga ya haifar da motsawar sha'awa, ma'ana mace ya kamata ta tsokano mijinta don ya kaimata hari ya samu abin da maza ke samu daga mata, kamar yadda tsuntsuwar tattabara ke yiwa mijinta, ya ya kuma idan shi mijinnne da kansa ya nemi hakan, shin ya halasta ta ja masa rai da yanga har ya kai ga ya hakura ya yi barci ?

wannan dangane da mace kenan, amma namiji lalle hadisi mi daraja  ya yi ishara da cewa, yawan jima'i na daga cikin sunnonin annabawa

wannan na nuni kan mustahabbancin yawan kusantar iyali, sai dai cewa wani hadisin ya tabbatr da cewa: shi mumini sha'awarsa a mace ta ke, idan aka hada waccan hadisin da wannan sai mu ce: shi mumini ba ya na yin jima'i ba don bukatar kansa kadai ba sai don ya farantawa matarsa  da kuma kashe zafin sha'awarta, lalle ita tafi shi sha'awa  kamar yadda hadisi ya tabatar da haka.

 an karbo daga manzon Allah (saw) cewa : shi jima'I na daga misdakin sadaka, har ya kai ga wanda ya ji wannan magana ya yi mamaki daga haka ya ce : ashe ba ka sanya ta farin ciki ba ? .

saboda haka kusantar da mumini zuwa ga matarsa ya na yi ne saboda Allah matsarkaki, saboda in ba don haka ba ita sha'awar mumini a mace ta ke, da shagaltar da zuciyarsa da abin da ya fi ye masa muhimmaci, ya na kasa yininsa da darensa zuwa kashi uku:  kashi daya barci kashi daya rayuwa kashi daya ibada.

a wani hadisi kuma shi mumini kebanta da iyalansa cikin halali.

ثمّ ورد عن الإمام الرضا (عليه السلام)  : لا تجامع إلاّ من شَبَق ( أي مع اشتداد الشهوة وشدّة الميل إلى الجماع

24 – ya zo daga imam rida (as) cewa: ka da ka kusanci iyalinka face kana cikin tsananin sha'awa.

الكافي  : قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : خلق الله الشهوة عشرة أجزاء ، فجعل تسعة أجزاء في النساء وجزءاً واحداً في الرجال ، ولولا ما جعل الله فيهن من الحياء على قدر أجزاء الشهوة لكان لكلّ رجل تسع نسوة متعلّقات به

25 – alkafi : sarkin muminai ali (as) ya ce: Allah ya halicci sha'awa zuwa kashi goma, ya sanya kashi tara ga mata, kashi daya ga maza, ba don Allah ya sanyawa mata kunya gwargwadon sha'awarsu ba, da dukkanin namiji ya kasance da mata tara rataye da shi.

قال أبو عبد الله (عليه السلام)  : إنّ الله جعل للمرأة صبر عشرة رجال ، فإذا هاجت لها كانت لها قوّة شهوة عشرة رجال

26 – baban Abdullah (as) ya ce:  Allah ya sanyawa mace hakurin maza goma, idan kwadayinta ya motsa to sai ya kasance ta na sha'awar mazaje goma.

عن ضريس عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : سمعته يقول  : إنّ النساء اُعطين بُضع اثنى عشر وصبر اثنى عشر . ( البُضع ) بالضمّ الجماع .

27 – an karbo daga daris daga baban abdullah (as) ya ce: an bawa mata jima'in mazaje shabiyu an kuma basu hakurin mutum shabiyu.

28 – an karbo daga baban basiru ya ce: na ji baban abdullah (as) mace ta fifita cikin dadi kan namiji da kashi casa'in da tara cikin dari, sai dai cewa Allah ya sanya mata kunya.

عن أبي بصير قال  : سمعت أبا عبد الله (عليه السلام) يقول  : فضّلت المرأة على الرجل بتسعة وتسعين من اللذّة ولكنّ الله ألقى عليهنّ الحياء

29 daga baban basir yae: na ji baban Abdullah{as} ya na cewa: an fifita mace da kasha casa'in ckin daga jin dadi sai dai ewa Allah ya sanya mata jin kunya.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : إنّ الله جلّ وعزّ جعل للمرأة أن تصبر صبر عشرة رجال ، فإذا حملت ـ  أي الشهوة  ـ زادها قوّة عشرة رجال .

29 – an karbo daga baban abdullah (as) Allah mai girma da daukaka ya sanyawa mace hakurin mazaje goma, idan sha'awarta ta motsa – sai ya kara mata karfin mazaje goma.

Kebancewa ya zo kan wannan riwaya mai daraja :

 الفقيه بسنده عن أبي جعفر (عليه السلام) قال  : إنّ الله تعالى خلق الشهوة عشرة أجزاء تسعة في الرجال وواحدة في النساء وذلك لبني هاشم وشيعتهم ، وفي نساء بني اُميّة وشيعتهم الشهوة عشرة أجزاء ، في النساء تسعة وفي الرجال واحدة

30 – alfakihu da isnadinsa daga baban jafar (as) ya ce: Allah ya halicci sha'awa zuwa kashi goma, kashi tara ga maza, kashi daya ga mata wannan duka cikin banu hashim da shai'arsu, amma cikin matan banu umayya da shi'arsu kashi tara ga mata kashi daya ga mazajensu.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : إنّ الله تعالى نزع الشهوة من رجال بني اُميّة وجعلها في نسائهم وكذلك فعل بشيعتهم ، وإنّ الله تعالى نزع الشهوة من نساء بني  هاشم وجعلها في رجالهم وكذلك فعل بشيعتهم

31- an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce: Allah ya cire sha'awar mazajen banu umayya ya sanya ta cikin matayensu, haka ya aikata kan shi'arsu.