فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

ADO

 

daga cikin hakkin miji kan matarsa, shi ne ta cancada masa ado wani lokaci da yin adon da zai kwana biyu bai tafi ba kamar yin kunshi da lalle, wani lokacin kuma da adon dare, cikin kowannne gari da lokaci ya na da ladubbansa na musammam, abin da aka nufa shi ne cancada ado da dukkanin taken da ke amsa sunan ado, duk da cewa shi ado na biye da al'adun kowacce al'umma  da kabila na da na ta adon.

misali farkon muslunci ado ga mace shi ne ta cancadawa hannayenta ado, mustahabbaccin yin haka na cigaba har ya zuwa ranar kiyama. hakika abin da muslunci ya zo da shi na dacewa da halayyar dan adam, matukar akwai lafiyayyen hankali da dabi'a, to za a samu hukunce hukuncen muslunci da dokokinsa, muslunci na tafiya da dukkanin gari da zamani, shi addini ne na har abada da Allah ya nufi dukkanin al'ummu  har zuwa ranar kiyama.

وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الإسْلامِ دِيناً فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْه[1]   

duk wanda ya nemi wani addini sabanin muslunci to ba za'a karba daga gare shi ba.

عن جعفر بن محمّد ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : رخّص رسول الله (صلى الله عليه وآله)للمرأة أن تخضب رأسها بالسواد ، قال  : وأمر رسول الله (صلى الله عليه وآله) النساء بالخضاب ـ  ذات البعل وغير ذات البعل  ـ أمّا ذات البعل ـ  أي من لها زوج  ـ فتتزيّن لزوجها ، وأمّا غير ذات البعل فلا تشبه يدها يد الرجال

32 – an karbo daga jafar dan muhammadu (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya saukakawa mata yiwa gashinsu kunshi da launin baki, ya ce : manzon Allah (saw) ya umarci mata da yin kunshi,masu aure cikinsu da wadanda basu da aure, wacce ke da aure sai ta cancada ado don mijinta, wadda kuma ba ta da aure ka da ta kamanta hannunta da da na maza.

عن محمّد بن مسلم ، عن أحدهما ـ  الباقر أو الصادق (عليهما السلام)  ـ قال  : لا ينبغي للمرأة أن تدع يدها من الخضاب ، ولو تمسحها بالحناء مسحاً ، ولو كانت مسنّة .

33 – an karbo daga muhammadu dan muslim daga sadik (as) ya ce: bai kamata mace ta bar hannayenta ba tare da ta yi musu kunshi ba  ko da kuwa ta tsufa.

Wannan na ishara da hatta tsohuwa mustahabbi ne ta yi kunshi.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : الحنّاء سيّد ريحان أهل الجنّة ، النائم في الحنّاء كالمتشحط في سبيل الله

34 – manzon Allah (saw) ya ce: lalle shugaban furen `yan aljanna shi ne wanda ya yi barci cikin lalle, misalin mai jihadi cikin tafarkin Allah.

 قال (عليه السلام)  : إنّي لاُبغض من النساء السلتاء والمرهاء ، فالسلتاء التي لا تختضب ، والمرهاء التي لا تكتحل

35 – manzon Allah (saw) ya ce: lalle ni ina kin macen da bata ado da sanya kwalli da wace ba ta yin kunshi.

عن أبي بصير ، قال  : سألته عن قصّ النواصي ـ  تريد به المرأة الزينة لزوجها  ـ وعن الحفّ ـ  إصلاح الشعر وحفّت المرأة وجهها من الشعر أن زيّنته  ـ والقرامل ـ  جمع قرمل كزبرج  : ما تشدّ المرأة على رأسها من الصوف والخيوط وما شابه  ـ والصوف وما أشبه ذلك  ؟ قال  : لا بأس بذلك كلّه ، قال محمّد  : قال يونس  : يعني لا بأس بالقرامل إذا كانت من صوف ، وأمّا الشعر فلا يوصل الشعر بالشعر لأنّ الشعر ميّت

36 – an karbo daga baban basiru, ya ce: na tambayi baban Abdullah (saw) kan yanke gashin goshi don yiwa miji ado da lullube fuska da gashin kai shi ma don ado, da daure kai da cancada masa ado, sai ya ce: babu laifi kan aikata dukkanin wadannan abubuwa.

daga cikin abubuwan da ke bayyana ado ga `ya mace sanya zinariya da azurfa da cancada ado da awarwaro:

عن محمّد بن مسلم ، عن أحدهما (عليهما السلام) ، وسئل عن حليّ الذهب للنساء  ؟ فقال  : ليس به بأس ولا ينبغي للمرأة أن تعطّل نفسها ولو أن تعلّق في رقبتها قلادة ، ولا ينبغي لها أن تدع يدها من الخضاب ولو أن تمسّحها بالحنّا مسحاً ولو كانت مسنّة

37- an karbo daga muhammadu dan muslim daga jafar sadik (as)  an tamabaye shin mata zasu iya ado da zinariya  ? sai ya ce : bai kamata mace ta hana ma kanta ado ko do kuwa da sanya sarkar wuya, bai kamaceta ta bar hannayenta haka ba tare da kunshi ba, ko da dai shafa musu lalle ne, ko da kuwa ta tsufa.

daga cikin abubuwan da ke bayyana ado sanya tufafi mai kyawu:

عن أبى عبد الله ، عن أبيه ، عن عليّ (عليهم السلام) ، قال  : الدهن يظهر الغنى ، والثياب تظهر الجمال ، وحسن الملكة يكبت الأعداء

38 – an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce:  shafa mai na bayyana wadata, tufafi na bayyana kyawu, kyawunta mu'amala na bakantawa makiya.

cikin wannan babu banbanci cikin maza da mata .

Allah madaukaki na cewa:

قُلْ مَنْ حَرَّمَ زِينَةَ اللهِ الَّتِي أخْرَجَ لِعِبَادِهِ وَالطَّيِّبَاتِ مِنَ الرِّزْقِ[2] 

  Ka ce waye ya haramta adon Allah wanda ya fitar da shi don bayinsa da kyawawa daga arziki.

 kayi ado ka sanya tufafi mai kyawu, lalle shi Allah kyakkyawa ne ya na son kyawu, saboda haka ya na da kyau shi kyawun ya kasance daga halaliya, wanda ke da wadata ka da ya yi barna wajen sayen kaya barkatai, lalle Allah madaukaki sarki na cewa:

لِـيُـنفِقْ ذُو سَعَة مِنْ سَعَتِه[3] 

mayalwaci ya ciyar daga yalwarsa.

 ma'ana gwargwadon ikonsa.

daga cikin abin da ke tabbatar da cewa ado na tafiya da zamani da muhalli abin da ya zo daga hadisi mai daraja:

عن سفيان الثوري ، قال  : قلت لأبي عبد الله (عليه السلام)  : أنت تروي أنّ عليّ بن أبي طالب (عليه السلام) كان يلبس الخشن وأنت تلبس القوهي ( ثياب بيض ينسب إلى قوهستان أو قوها كورة بين نيسابور وهرات ) ـ  أي من الألبسة الخارجية آنذاك  ـ والمروي قال  : ويحك إنّ عليّ بن أبي طالب كان في زمان ضيق ، فإذا اتّسع الزمان فأبرار الزمان أولى به

39 – an karbo daga sufyanu assauri, ya ce: na cewa baban Abdullah (as) kai kana rawaito cewa aliyu dan abi dalibi (as) ya kasance ya na sanya kausasan tufafi, amma kai kuma kana sa farare kaya na kasar waje, sai imam ya ce: Allah wadaranka lalle aliyu dan abi dalibi ya sanya wannan tufafi ne zamanin da ya ke cikin kuncin rayuwa, idan zamani ya yalwata bayin Allah rabautattu sune suka fi cancanta da shi.

عن أمير المؤمنين (عليه السلام) ، قال  : ليتزيّن أحدكم لأخيه إذا أتاه كما يتزيّن للغريب الذي يحبّ أن يراه في أحسن الهيئة

40 – an karbo daga sarkin muminai ali (as) : dayanku ya yi ado saboda ziyarar dan'uwansa kamar yadda ya ke yin ado saboda ziyarar bako da ya ke kaunar ya ganshi cikin mafi kyawun shiga.

bisa la'akari sai mu ce mafi cancanta da cancadawa juna ado su ne miji da matarsa.

عن إسحاق بن عمّـار ، قال  : قلت لأبي عبد الله (عليه السلام)  : يكون للمؤمن عشرة أقمصة  ؟ قال  : نعم . قلت  : عشرين  ؟ قال  : نعم ، وليس ذلك من السرف ، إنّما السرف أن يجعل ثوب صونك ثوب بذلتك

41 – an karbo daga is'hak dan ammar, ya ce: na cewa baban abdullah (as) tufafi goma na kasancewa ga mumini ? ya ce: na'am, sai na ce: ishirin fa: ya ce

: na'am hakan ba barna ba ne, barna shi ne sanya tufafi ado da kwalliya a muhallin da bai da ce ba.

عن أبي عبد الله (عليه السلام)  : أدنى الإسراف هراقة فضل الإناء وابتذال ثوب الصون وإلقاء النوى  

42 – an karbo daga baban abdullah (as) mafi karancin barna zubar da abin da ya rage cikin kwarya da sanya tufafi ado a muhallin kazanta  da

Sannan tufafi da sanya su na da ladubba na musammam wadanda suka zo cikin littafan akhlak, kamar yadda mace ta ke da kayan da suka kebanta da ita, haka namiji ke da kayan da suka kebance shi, ka da dayansu ya yi ganganci kamanceceniyya da daya.

عن أبي عبد الله ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : كان رسول الله (صلى الله عليه وآله) يزجر الرجل يتشبّه بالنساء ، وينهى المرأة أن تتشبّه بالرجال في لباسها .

43 – an karbo daga baban Abdullah (as) daga babanninsa (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya kasance ya na hani da tsawatarwa kan namiji ya yi kamanceceniya da mata, haka ya na hana mace yin kamanceceniya da maza cikin sanya tufafinta.

Sannan ya kamata miji ya yalwata iyalinsa , hakika hakan na daga azurtar duniya  kamar yadda ya zo cikin hadisai masu yawa.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : من السعادة سعة المنزل

44 - an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce:ya na daga azurta yalwatar gida.

وقال (عليه السلام)  : للمؤمن راحة في سعة المنزل

45 – imam (as) ya ce: mumini na da hutu cikin yalwatar gida.

وسئل أبو الحسن (عليه السلام) عن أفضل عيش في الدنيا  ؟ قال  : سعة المنزل وكثرة المحبّين

46 – an tambayi baban hassan (as) kan mafificiyar rayuwa cikin duniya ? sai ya ce: yalwar gida  da yawan masoya.

ـ قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : من سعادة المرء المرأة الصالحة والمسكن الواسع والمركب البهي والولد الصالح

47 – manzon Allah (saw) ya ce: daga cikin azurta shi ne samun mace saliha da gida yalwatacce da abin hawa na alfarma da da nagari.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : أربع من السعادة وأربع من الشقاوة ، فالأربع التي من السعادة  : المرأة الصالحة والمسكن الواسع والجار الصالح والمركب البهي ، والأربع التي من الشقاوة  : الجار السوء والمرأة السوء والمسكن الضيّق والمركب السوء

48 – imam (as) ya ce: abubuwa hudu na daga azurta, abubuwa hudu na daga tsiyata, abubuwa hudu da suke daga arziki shi ne mace saliha,  gida mayalwaci, makoci nagari, abin hawa na alfarma.  abubuwa hudu da suke daga tsiyata sune: makoci mugu, kuntataccen gida, muguwar mata, abin hawa mara kyawu.

ba boye ya ke kan cewa gida na da iyaka a muslunci, ya zama dole gida ka da ya wuce bakin bukatuwa.

فقد ورد عن أبي عبد الله (عليه السلام)  : كلّ بناء ليس بكفاف فهو وبال على صاحبه

49 - hadisi ya zo daga baban abdullah (as) duk gidan da ya wuce bukata to azaba ne kan ma'abocinsa.

cancada ado cikin kowanne irin hali abune mai kyawu ga mace idan ta kasance ta nayin wannan ado saboda mijinta  dukkanin azaba ta tabbata ga matar da ke yin ado ga wani wanda ba mijinta ba, mai ya fi muni daga mijinta da ke fito da matarsa waje halin ta cancada ado ga kuma kamshin turare na tashi, wannan miji ya tabbata shashasha mara kishi, misalinsa kamar alade da matarsa ke jingina da jikinsa don wani aladen ya samu damar zakke mata, saboda haka nema aka haramta cin naman alade, saboda duk wanda ke cin namansa zai zama mara kishi.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : وأيّما رجل تتزيّن امرأته وتخرج من باب دارها فهو ديّوث ، ولا يأثم من يسمّيه ديوثاً ، والمرأة إذا خرجت من باب دارها متعطّرة والزوج بذلك راض ، يُبنى لزوجها بكلّ قدم بيت في النار .

50 – manzon Allah (saw) ya ce: duk mutumin da matarsa ke cancada ado ta fito ta kofar gidansa halin kamshin turare na tashi, tabbas wannan mutumin bai da kishi,  sannan za 'a gina mata a wuta kan dukkanin taki daya da ta tattaka.

Ado  na halasta da zama abin yabo idan ya kasance anyi shi don miji lalle mutum cikin dabi'arsa ya na son kyawu da tsafta da ado, sau da yawa miji sun rabu da matarsa sakamakon kazantarta, da kuma kasantuwar fuskarta bushe ba tare da ta tsufa ba kamar yadda ya zo cikin hadisi:

عن أمير المؤمنين (عليه السلام) ، أنّ النبيّ (صلى الله عليه وآله) قال  : مرّ أخي عيسى بمدينة وفيها رجل وامرأة يتصايحان ، فقال  : ما شأنكما  ؟ قال  : يا نبيّ الله ، هذه امرأتي وليس بها بأس ، صالحة ، ولكنّي اُحبّ فراقها . قال  : فأخبرني على كلّ حال ما  شأنها  ؟ قال  : هي خلقة الوجه من غير كبر ، قال لها  : يا امرأة ، أتحبّين أن يعود ماء وجهكِ طريّاً  ؟ قالت  : نعم . قال لها  : إذا أكلتِ فإيّاكِ أن تشبعي ، لأنّ الطعام إذا تكاثر على الصدر فزاد في القدر ، ذهب ماء الوجه ، ففعلت ذلك فعاود وجهها طريّا[4]ً

51 – an karbo daga sarkin muminai ali (as) cewa annabi (saw) ya ce: dan'uwana isa (as) ya wuce ta cikin wani gari sai ya hadu da wata mata da mijinta suna cece kuce, sai ya tambaye su ya ce: mai ya faru da ku ? sai mijin ya ce: ya annabin Allah wannan mata ba ta da matsala mace ce saliha, sai dai cewa ni ina son rabuwa da ita, sai isa (as) ya ce masa: ka bani labarin dukkanin abin da ya faru game da ita  sai ya ce : fuskarta ta tsufa ba tare da girma ba ko tsufa, sai isa (as) ya ce mata: shin kina son ruwan fuskarki ya dawo sabo danye ? sai ta ce na'am, sai ya ce: idan kika ci abinci ka da ki koshi, saboda shi abinci idan ya cika kirji ya wuce gwargwado ya na tafiya da ruwan fuska, sai wannan mata ta aikata haka ruwan fuskarta ya dawo danye.

 [1] Ali Imran:85

[2] A'araf:32

[3] Addalak:7

[4] Ilalul shara'I:497