فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA

 

Babu shakka babu kokwanto cikin kasancewa ba banbanci tsakanin mace da namiji cikin asali halittarsu, lalle su duka biyun an haliccesu daga rai guda kamar yadda ya zo cikin fadin Allah madaukaki:

خلقكم من نفس واحدة وجعل منها زوجها

  ya halicce ku daga rai guda ya sanya mijinta daga gareta.

kamar yadda ya ke cewa babu banbanci tsakaninsu cikin asalin tarbiyya da koyarwa da ilimi da takawa da suluki zuwa ga Allah matsarkaki, sai dai cewa saboda sabanin da ke cikin tsarin halittarsu ta jiki, haka sabanin da ke cikin tausayi da so da hankaltar kowanne daya daga cikinsu, Allah ya sanyawa kowanne daya daga cikinsu dabi'u kebatantattu, ya kuma rattaba musu hukunce hukunce na al'ada da shari'a, sai ya sanya jagorantar al'umma da shari'a da marja'iyya hannun namiji, sai ya kasance shi ne mai tsayuwa kan mace,  bisa la'akari da haka ne mazaje suka fifita kan mata, wannan ba ya nufin fifita ta zati ba cikin kowanne hali, kadai dai sakamkon nauyin da ka dorawa namji na zamantakewa wadda bai dacewa da dab'iar taushi da tausayi na halittar `ya mace, duk da cewa an rufe kofar annabta ga mata sai dai cewa a bude musu babbar kofa itace kofar waliyintaka, lalle mace na iya zama babbar waliyiya daga waliyyan Allah, ta zama ma'abociyar karamomi da madaukakan mukamai, kamar yanda aka bude mata kofofin ilimi da ma'arifa da ayyuka nagargaru da takawa da dukkanin kyawawan dabi'u, don ta zama abar buga misali cikin dukkanin wadannan fagage, daga nan Allah ya buga misali ga muminai maza cikin littafin mai girma  da matar fir'auna asiya `yar muzahim, wanna na ishara da irin girman da mace ke da shi, kamar yanda idan kur'ani ya ambaci mazaje masu tuba sai ya kawo mata masu tuba, haka al'amarin yake cikin dukkanin kyawawan siffofi, maza na tarayya da mata cikin wadannan falaloli, duk da cewa akwai wasu siffofi da maza suka kebanta da su sabanin mata kamar jarumtaka girma da kyauta, saboda kare mace daga asara sai ake rinjayar mata tsoro da rowa da rashin jin girma kamar yanda ya zo cikin hadisai masu daraja, Allah matsarkaki shi ne mafi sani zahiri da badinin bayinsa dukkanin abin da ya fada ya yi hukunci da shi ne hakikanin hakika, bisa haskensa ne batutuwa da  matsaloli ke warwarewa cikin rayuwa, saboda idan ya zamanto ya fifita mazaje kan mata to tabbas ya aikata hakan bisa hikima, kamar yanda ya fifita sashen annabawa kan sashe.

MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA KAN MATA

خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْس وَاحِدَة وَجَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَ[1]

 Kamar ya da  ya kasance babu banbanci tsakanin mace da miji cikin asalin tarbiyya da ta'alim da ilimi da takawa  da suluki zuwa ga Allah matsarkaki, sai daci cewa  sakamakon banbancin tsarin ginin halittarsu ta gangar jiki hakada banbantarsu cikin hankali da tausayi, sai ubangiji ya sanyawa kowanne daya cikinsu kebantattun dabi'u ya kuma dora hukunce hukuncen shari'a da al'ada kai, ya sanya limantar sallar jam'I da alkalanci da marja'iyanci ga `ya`ya maza. Ta wanne fuskani namiji shi ne mai tsayuwa kan mata  da wannan la'akari ne maza suka fifita kan mata , sai dai hakan bai nufin fifiko na zati cikin kowanne hali, bari dai haka ya takaitu cikin wani ba'arin mas'uliyar zamantakewar yau da gobe wadda mat aba za su iya yin wannan ayyuka ba sakamakon taushin dabi'arsu [2] amma duk da cewa an rufe diya mace kofar zama annabiya ko imamiya sai dai cewa an bude mata kofofin wilayar mai girma, lalle mace na iya zama waliyiya daga waliyyan Allah ta zamanto ma'abociayr karamomi da darajoji madaukaka, kamar yadda aka bude mata kofofin imani da aiki nagari da ilimi da ma'arifa da takawa da kyawawan halaye har ta jsance misali cikin kowanne fage, daga nan Allah ke buga misali ga muminai maza cikin littafinsa mai daraja misalign kuwa shin he matar fir'auna asiya diyar mazahim, wannan na nuni kan girman mace da  matsayinta  madaukaki. Kmara yadda kur'ani ke ambaton  maza masu tuba haka ke ambaton mata wadanda suka tuba, cikin kyawawan siffofi daban, maza na yin tarayya da mata cikin wadannan faloli, duk da cewa akwai kyawawan siffofi da mazaje suka kebanta da su koma bayan mata , kamar misalign jarumta  da girman da kyauta, amma saboda kiyaye mata daga lalacewa sai aka rinjayar musu da siffofin tsoro da rowa da rashin girma. Kamar yadda ya zo cikin hadisai masu daraja,  shi ubangiji shi ne mafi sanin halittarsa da kuma ruhiyar mazaje  da mata , dukkanin abin da y ace da dukkanin abin da ya hukunta shi ne gaskiaya, kan haskensa ake fassara abubuwa ake kuma warware matsaloli cikin rayuwa. Idan ubangiji ya fifita mazaje kan mata to yayi hakan ne kan hikima , kamar yadda ya fifita annabawa wasu kan wasu.

Ubangiji matsarkaki na cewa:

الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْض وَبِمَا أنفَقُوا مِنْ أمْوَالِهِمْ فَالصَّالِحَاتُ قَانِتَاتٌ حَافِظَاتٌ لِلْغَيْبِ بِمَا حَفِظَ الل[3]ه

mazaje sune masu tsayuwa kan mata da abin da Allah ya fifita sashensu kan sashe da kuma abin da suka ciyar daga kudadensu mataye salihai masu biyayya masu kiyaye gaibu daga abin da Allah ya kiyaye.

kasantuwar an bawa mazaje tsayuwa koma bayan mata, bai kasance al'amari mara hikima da manufa ba daga ubangiji cikin fifita sashe kan sashe, kadai dai hakan ya faru ne sakamakon zurfafawa da hikima cikin tsara al'amuran dan adam wadda suka ginu kan ilimin Allah, larurar mika tsayuwa ga mazaje koma bayan mata shi ne cewa lalle su maza  ne suke daukar nauyi iyali wajen ciyarwa da kai kawo cikin sanyi da zafi don sama musu abin da za su rayu, da sadaukar da dukkanin kokarinsu don ganin hakan ya tabbata, su ne suka fi kowa sanin ya ya za'a tafiyar da sha'nin gida da warware dukkanin matsalolinsa, saboda haka tsayuwa ta zama hakkin namiji a dabi'ance hakama a hankalce, sannan kuma ita tsayuwar ta fi dacewa da halittar da namiji ta zahiri da badini, dalili kan haka a hankalce bai fita daga da'irar abubuwa hudu:

1-ko dai mace ta zamanto tana cin gashin kanta da kebanta da tsayuwa kan al'amuranta koma bayan maza, sai dai cewa ba'a rinjayar da hakan ba saboda rashin dacewar tsarin halittarta da hakan.

2 – ko kuma suyi tarayya cikin tsayuwa shi da ita, sai ya lazimta rashin tsari da doka da tabarewar rayuwar aure da yawan samun sabani da danne hakkoki.

3 – ko kuma ya zamanto shi da ita ba wanda zai tsaya kan wani kwata kwata, wannan kuma ya sabawa abin da dabi'a ta hukunta cikin tsara rayuwa zamantakewa da dan adamtaka.

4 – ko kuma dai namiji ya kebanta da tsayuwa kan al'amaurn mace koma bayan ita macen, wannan shi ne abin da dama muke nema, kamar yanda wahayi ya bayyana hakan:

الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْض

 ( maza sune masu tsayuwa kan mata ) lalle ya na dacewa da dabi'ar dukkaninsu, shi ne abin da zai lamunce rayuwa mafi daraja da natsuwa da kwanciyar hankali.

عن الحسن بن عليّ (عليهما السلام) ، قال  : جاء نفر من اليهود إلى رسول الله (صلى الله عليه وآله)فسأله عن مسائل فكان فيما سأله  : أخبرني ما فضل الرجال على النساء  ؟ قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : كفضل السماء على الأرض ، أو كفضل الماء على الأرض ، فبالماء تحيى الأرض ، وبالرجال تحيى النساء ، لولا الرجال ما خلق النساء ، لقول الله عزّ  وجلّ  : (  الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْض  ) ، قال اليهودي  : لأيّ شيء كان هكذا  ؟ قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : خلق الله عزّ وجلّ آدم من طين ، ومن فضلته وبقيّته خلقت حوّاء ، وأوّل من أطاع النساء آدم فأنزله الله من الجنّة ، وقد بيّن فضل الرجال على النساء في الدنيا ، ألا ترى إلى النساء كيف يحضن ولا يمكنهنّ العبادة من القذارة ، والرجال لا يصيبهم شيء من الطمث ، قال اليهودي[4]  : صدقت يا محمّد

1-An karbo daga hassan dan ali (as) ya ce: wasu mutune daga yahudawa sun je wajen manzon Allah (saw) sai suka tambayi manzon Allah (saw) cikin abin da dayansu yay i tambaya: ka bani labari game da fifikon maza kan mata ? sai manzon Allah ya ce: fifikon maza kan mata misalin fifikon sama kan kasa, haka ma kamar fifikon ruwa kan kasa, da ruwa ne kasa ke rayuwa, ba da ban maza ba da ba'a halicci mata ba, saboda fadin Allah: ( maza sune masu tsayuwa kan mata da abin da Allah ya fifita sashensu kan sashe ) sai wannan bayahude ya ce: saboda mai  ya zama haka ? sai annabi (saw) ya ce: yayin da Allah ya halicci adamu daga tabo daga ragowarsa ne Allah ya halicci hauwa'au, sannan farkon wanda ya biyewa mace shi ne adamu (as) sai Allah ya sauko da shi daga aljanna hakika ya bayyana fifikon maza kan mata cikin duniya, ashe ba ka ga cewa mata na yin jinin haila ba da bai basu damar yin ibada saboda kazantar da suke ciki, maza wani abu daga jinin haila bai shafarsu, sai wannan bayahude ya ce: kayi gaskiya ya muhammadu.

ya zo cikin tafsirin aliyu dan Ibrahim kummi:

الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْض وَبِمَا أنفَقُوا مِنْ أمْوَالِهِم

فَالصَّالِحَاتُ قَانِتَاتٌ حَافِظَاتٌ لِلْغَيْبِ بِمَا حَفِظَ اللهُ

( maza sune masu tsayuwa kan mata da abin da Allah ya fifita sashensu kan sashe da abin da suka ciyar daga dukiyoyinsu  ) ma'ana Allah ya farlantawa maza ciyarda mata, sannan kuma ya yabawa mata cikin fadinsa: (mata salihai masu biyayya masu tsare gaibi bisa abin da Allah ya tsare su )   ma'ana masu tsare kawukansu  idan mazajensu sun faku.

وفي رواية أبي الجارود عن أبي جعفر (عليه السلام) في قوله  : ( قانتات ) أي مطيعات

2-ya zo cikin riwayar abi jarud daga baban jafar(as) cikin fadin Allah mata masu ibada sai imam(as) ya ce ma'ana masu biyayya ga mazajensu.

Duk da kasantuwa fifikon namji sai dai cewa haka baya nufin cewa an gabatar da shi kan mace cikin kowanne hali, hakika mafi karamcin cikinku sune mafi takawar cikinku, saboda haka abin lura shi ne takawa, idan mace ta yi aiki da abin da Allah ya umarce ta, lalle itace mafi daraja daga namjin da bai aiki da nauyin da ka dora kan wuyansa ba, sannan wannan bai kore fifitar mazaje cikin kasantuwarsu masu tsayuwa kan mata.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : ما من رجل رديء إلاّ والمرأة الرديّة أردى منه ، ولا من امرأة صالحة إلاّ والرجل ( الصالح ) أفضل منها ، وما ساوى الله قط امرأة برجل إلاّ ما كان من تسوية الله فاطمة بعليّ (عليه السلام) وإلحاقها به وهي امرأة بأفضل رجال العالمين

3 – manzon Allah(saw) ya ce: babu wani lalatacce namiji face ka samu lalatacciyar mace tafi shi lalacewa, sannan babu wata mace saliha face ka samu namiji salihi da ya fificeta, Allah bai taba daidaita mace da namiji ba sai kan fatima da ali (as) da risakar da ita da shi, itace mafi daraja daga mazan dukkanin duniya.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : خير رجالكم من اُمّتي الذين لا يتطاولون على أهليهم ويحنون عليهم ولا يظلمونهم ، ثمّ قرأ  : (  الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا  فَضَّلَ اللهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْض  ) الآية

4-Manzon Allah (saw) ya ce : mafifit mazajenku cikin ala'ummata sune wadanda bas a nuna isa kan iyalansu , sun a tausasa musu bas a zaluntarsu, sannan ya karanta:

 

  maza masu tsayuwa kan mata da abin da Allah ya fifita sashensu kan sashe. 

Da tafsirin wannan aya ne zamu fuskanci cewa tsayuwar maza kan mata ba ya nufin nuna fin karfi da mulki fin karfi ga mazaje, bari dai ya zo da ma'anar tausayi da nuna kauna da rashin nuna isa da fin karfi kansu matan, da watsi da zaluntarsu da danne musu hakkoki, dole namiji ya kiyaye ya guji duk abin da zai kawo bacin ransu, ma'anar tsayuwa kan mata shine namiji ko da yaushe ya kansance b da lura da bukatunsu, hakika shi ne ubangijin gida, shi dama ubangijin gida shi ke kare gida, kamar yadda abdul mudallib ya gayawa abrahata yayin ya himmatu da kai hari kan dakin Allah, ya ce masa ni dai ni ne ubangijin rakuma na, shi kuma gida na da ubangiji kuma tabbas zai kareshi.

Saboda haka daga cikin abin da ubangidantaka ke hukuntawa shi ne kare gida da ahalinsa, ubangijin gida shi ne mai tsayuwa kan sha'anin gida.

Sannan ina mai kara maimaitawa cewa mai ya fi muni daga mazajen da ke dukan matansu.

Ya zo cikn littafin tahzibul ahkam cewa: yanzu bana baku labari da mafi alherin mazajenku ba ? sai mu ka ce na'am, lalle daga cikin mafi alherin mazajenku shi ne ma takawa mai tsarkin zuciya mai kyautar hannu, mai lafiyar geffa biyu, mai biyayya ga iyayensa, iyalansa ba sa neman mafaka da waninsa, sannan ya kara cewa: yanzu bana baku labari da sharrin mazajenku ? mu ka ce na'am, lalle daga cikin mafi sharrin mazajenku shi ne makagi mai yawan alfasha mai ci shi kadai, mai hanawa wanda suka ziyarce shi mai dukan matarsa da bawansa  wanda iyalnsa ke fakewa da waninsa, mai sabawa iyayensa[1] A'araf:189

[2] Hakika na tattara hankali na cikin wannan littafi kan wannan ma'ana na tayi maimaita bayani kanta wurare da yawa saboda haka zan kara ma yanzu don ma'anar ta zauna a kwakwaln masu karatu: lalle shi muslunci addeini ne madaidaici bai kuma banbanta mace da namiji ba cikin asalin halittabda mutumtaka ya halicce su daga rai guda kamar yadda kur'ani ya tabbata mana da hakan ya kuma kmsawa wannan rai fajircinta da takawarta, ya kuma lalle ya rabuata duk wanda ya tsarkake wannan rai daga namiji da mace. Babu banbanci tsakanin mace da miji cikin tushensu saboda dukkaninsu daga adamu da hauwa'u(as) suke kuma babu fifiko cikin nasabobi, babu fifiko face na tsoron Allah(lalle mafi karamcinku wajen Allah shine mafi jin tsoronsa) a wani wajen kuma ya ce kowanne rai ana jingina mata abin da ta aikata.

[3] Nisa'i:34

[4] Biharul anwar m 100 sh 241