فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

TAIMAKO DA TALLAFAWA

 

قال (عليه السلام)  : تعين زوجها على دهره وتساعده على دنياه وآخرته ولا تعين الدهر عليه ... أعانت زوجها على الحجّ والجهاد أو طلب العلم أعطاها الله من الثواب ما يعطي امرأة أيوب (عليه السلام) من الثواب والأجر وجنّات عرضها السماوات والأرض

9 – imam (as) mai tallafawa mijinta kan zamaninsa mai taimkaon kan duniyarsa da lahirarsa , ba mai tallafawa zamanin kan gallaza ma sa ba , duk matar da taimakawa mijinta kan aikin hajji ko neman ilimi , Allah zai bata ladan da ya baiwa matar annabi ayub (as) da aljanna wacce fadinta misalin fadin sama da kasa ne.

 kamar yadda yak e cewa miji ya kamata ya dnga taimakawa matarsa hatta kan batutuwan gida da rayuwar da ta kebanta da

mata , hakika hadisi mai daraja ya tabbata cewa:

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله) لأمير المؤمنين (عليه السلام) بعدما رآه في البيت ينقّي العدس ، وفاطمة (عليها السلام) جالسة عند القدر  : اسمع منّي يا أبا الحسن ، وما أقول إلاّ من أمر ربّي  : ما من رجل يعين امرأته في بيتها إلاّ كان بكلّ شعرة على بدنه عبادة سنة صيام نهارها وقيام ليلها ، وأعطاه الله من الثواب مثل ما أعطاه الصابرين وداود النبي ويعقوب وعيسى (عليهم السلام) . يا علي ، من كان في خدمة العيال ولم يأنف ، كتب الله اسمه في ديوان الشهداء ، وكتب له بكلّ يوم وليلة ثواب ألف شهيد . والحديث طويل وأخاف على المطالع أن أذكر ما فيه من الثواب والأجر ، وممّا جاء فيه  : يا عليّ ، ساعة في خدمة البيت خير من عبادة ألف سنة وألف ... ولا يخرج من الدنيا حتّى يرى مكانه في الجنّة . يا عليّ ، من لم يأنف من خدمة العيال دخل الجنّة بغير حساب . يا عليّ ، خدمة العيال كفّارة للكبائر وتطفئ غضب الربّ ومهور حور العين وتزيد في الحسنات والدرجات . يا عليّ لا يخدم العيال إلاّ صدّيق أو شهيد أو رجل يريد الله به خير الدنيا والآخرة[1]   

10 – manzon Allah (saw) ya cewa sarkin muminai ali (as) bayan ya ganshi ya na taya fatima (as) aikin gida ya na tsince mata kwayar tsabar adas ita kuma fatima na zaune gindin tukunya: sai ya ce: saurare ni ya baban hassan ka ji mai zance daga al'amarin ubangijina: babu wani namiji da zai taimaki matarsa cikin ayyukan gida face ladan ibadar shekara da azumin yininta da tsayuwar darenta  ya kasance ga dukkanin silin gashin jikinsa, sannan kuma Allah ya bashi misalin ladan da ya ke baiwa masu hakuri daga annabi dauda da yakub da isa (as) ya ali duk wanda ya kasance cikin hidimar iyalinsa sannan kuma bai nuna kyama ba, Allah zai rubuta sunansa cikin diwanin shahidai, ya rubuta masa ladan shahidi dubu kan dukkanin yininsa darensa, ya ali sadaukar da lokaci kankani cikin hidimar iyali ya fi alheri daga ibadar shekara dubu sau dubu, sannan  mutum ba zai fita daga duniya har sai ya ga muhallinsa a aljanna, matukar bai nuna kyama cikin hidimtawa iyali zai shiga aljanna ba tare da hisabi ba, ya ali hidimtawa iyali kaffara ne ga manyan zunubai sannan ya na kashe fushin ubangiji, kuma sadakin  matan aljanna ce da kuma kara kyawawan ayyuka da daukakar daraja, ya ali babu mai hidimtawa iyali sai shahidi ko siddiki ko mutumin da Allah ke sonsa da alherin duniya da lahira.[1]Jama'ul sa'adat m 2 sh 142