فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA

 

 

mafi darajar tarihin tarbiyyar iyali shi ne tarihin rayuwar ali (as) da matarsa Fatima (as) hakika tarihin rayuwarsu tarihin rayuwa ne na ma'asumai biyu wadanda zancensu da ayyukansu da abubuwan da suka zartar  dukkaninsu na daga cikin sunna mai daraja, ba zaka taba samun iyali da suke dauke da ismar zati da dukkanin sasanninta da bangarorinta sai gidan ali da fatima (as) rayuwarsu ta aure ita ce mafi alherin misali da kasantuwa abar kwaikawayo, cikin rayuwarsu akwai wani abin tsintuwa da ke yada haske da kyawu da rayuwa da nishadi, za mu koyi yanda ya kamata mu rayu kaka zamu dinga tunani a matsayinmu na ma'aurata da sukayi sa'a cikin rayuwar aure da duniyar iyali da tarbiyya da koyarwa.

daga cikin ababen tsinta:

yayin da abubakar da umar suka yi niyyar ziyartar fatima (as) lokacin rashin lafiyarta sun nemi izinin ali (as) sai ya shiga wajenta ya ce mata: ya ke `yantacciya hakika wane da wane suna kofar gida suna jira suna son gaishe ki amma me kika gani ? sai tace gida gidanka ne sannan `yantacciya taka ce matarka ce, kana iya yin yadda ka so.

wannan tsintuwa na da matukar kayatarwa cikin rayuwar aure, lalle wannan tsintuwa na ishara ga ma'aurata ta yaya fuskantar juna zai kasance tsakaninsu da kuma yanda za su yi mu'amala da juna, ga wanda ya nufi shigar da bako cikin gida kan wani batu na siyasa  ya kamata ya nemi izinin matarsa ya bata labari ya ji ra'ayinta kan batun saboda ta na da hakki kan gida da abin da ke gudana cikinsa, sannan ita kuma ya kamata ta girmama matakin da zai dauka ka da ta kalli kanta bakin komai gaban mijinta, ta ce masa gidanka ne ni kuma mallakarka ce ka aikata dukkanin abin da ka ga ya dace,

daga cikin kyawawan tsintuwa daga gidan ali da Fatima {as} shi ne abin da ya zo cikin wasiyyar zahara (as) lalle ita ta bayyana rukunan asasi cikin rayuwar aure ta koyar da dukkanin mutane da matan duniya yaya mace za ta kasance cikin gidan mijinta da menene aikinta a addinnance da mutunce, lalle da mace za ta yi ado da wadanan siffofi da ta rayu cikin arziki ta mutu cikinsa da soyayya kauna da tausasawa sun zama jagaba cikin rayuwarta, rabuwa da ita ya girmama wajen mijinta.

lokacin da Fatima ta yi rashin lafiya mai tsanan  ta zauna tsawon kwanaki arba'ain cikin rashin lafiya, yayin da ta debe tsammani daga rayuwa, sai ta cewa da ali (as) ya dan baffana lalle raina ya sanar da ni mutuwa ta, lalle ni ina ganin babu abin da ya rage gareni face riskar babana cikin kowanne lokaci, ina maka wasiyya da wasu abubuwa da ke cikin zuciyata, sai ali (as) ya ce mata: kiyi wasiyya da dukkanin abin da ki ke so ya `yar manzon Allah (saw) sai ya zauna kusada kanta ya fitar da mutanen da suke cikin gidan, sannan ta ce: ya dan baffana ba ka sameni makaryaciya ko maha'inciya tun lokacin da ka aureni, sai ali (as) ya ce muna neman tsarin ubangiji daga haka  lalle ke kimfi kowa sanin daga Allah da biyayya da karamci da tsananin tsoron Allah daga kasantuwar ace na zargeki da saba mini, lalle rabuwa da rashinki na da tsanani gareni sai dai cewa al'amari ne da babu makawa daga gare shi, wallahi musibar zafin rabuwa da manzon Allah (saw) ta kara sabunta gareni hakika rashinki da rabuwa da ke ya girmaa gareni, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un daga musiba me ya fita girma da radadi da zartuwa da bakin ciki, wannan wallahi wata musiba ce da ba ta ta'aziyyarta, sai suka fashe da kuka zuwa dani wani  lokaci.

hakika Fatima (as) ta tattare rayuwar aure cikin wannan tattaunawa ta malakutiyya zuwa rukunai uku:

1 – rashin karya 2 – rashin ha'inci 2 – rashin sabawa miji.

sai ta tunatar da sarkin muminai ali (as) da'arta da tsarkakarta da sallamawarta ga mijinta, shi kuma imam (as) ya yi godiya ga kiyaye alkawarinta  ya kuma yi yabo kan tsarkakarta da juriyarta da takawarta, ya bayyana mata soyayyarsa da kaunarsa da ratayarsa gareta, hakaia kalmominsa gareta kalmomine da suke motsa  soyayya da girmama ga matarsa wacce babu wata mace kamar ta dukkanin fadin duniya.

bayan sun gama kuka sai ali (as) ya kama kanta ya sanya shi kan kirjinsa ya rungume sannan ya ce: kiyi mini wasiyya da dukkanin abin da ki ke so, tabbas za ki sameni mai zartar da wasiyyarki kamar yanda ki ka umarce ni, ki zabi al'amarinki kan al'amarina.

na'am haka rayuwar aure azurtacce ta ke ka ga miji ya zabi fifita abin da matarsa ke so kan abin da zuciyarsa ke so matukar matarsa na tsoran Allah, kamar yadda zaka samu mace ta na fifita abin da mijinta ke so kan abin da ta ke so matukar mijin na ta mai da'a ne ga Allah  mai tsarkake niyya, zuwa misalin wannan rayuwar ma'aurata muke kiran baki dayan mutane tabbas za su samu arzikin gida biyu duniya da lahira.