فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

DA NAMIJI KO MACE

                       

al'umma ta kasance ta na karkata ga `ya`ya maza a zamanin jahiliya kafin zuwan muslunci don su kasance makomarsu a gobe kan yake yake da hare hare, sannan sun kasance suna binne `ya`ya mata halin suna raye saboda akidarsu kan cewa su `ya`ya mata abin kunya ne kansu, sannan suna zama ganimar abokan gaba a fagen yaki da dalilansu daban-daban.

Muslunci ya zo don daukaka matsayin `ya mace, sannan muslunci ya kasance ya na zargin ayyukan jahiliya da motsa zukatansu da alkur'ani:

  وَإذَا المَوْؤُدَةُ سُئِلَتْ * بِأيِّ ذَ نْب قُتِلَتْ[1] 

idan aka tambayi   wadda aka binne ta da ranta * da wanne laifa ne a kasheta.

Muslunci na zargin wadannan da suka kasance idan anyi musu bushara da `ya mace sai fusakensu su turbune  suyi baki suna halin danne bakin ciki kamar yanda kur'ani ya bamu labarin haka cikin fadinsa madaukaki:

وَإذَا بُشِّرَ أحَدُهُمْ بِالاُ نثَى ظَلَّ وَجْهُهُ مُسْوَدّاً وَهُوَ كَظِيم[2]ٌ 

  idan aka yiwa dayansu bushara da diya mace sai fuskarsa ta yini bakin kirin halin ya na cike da bakin ciki.

 annabin rahama ya zo don shelanta juyin juya halinsa na kawo gyara cikin munanan al'adu na jahiliya, ya ruguje gumakan bauta da karya kaidoji da sarkokin don `yantar da dan adam daga bautar kansa da bautar wanin ubangiji zuwa bautar ubangiji matsarkaki ya kuma shiryar da shi zuwa tafarkin shiriya da hanya mikakka, da bautawa Allah daya tal rak wanda bai haifa ba'a haife shi ba wani tsara bai kasance gare shi ba.

Muslunci ya zo da koyarwa don ya baiwa mace hakkinta da bayyana matsayinta madaukaki cikin al'ummar muslunci da iyali masu riko da addini.

Muslunci ya zo ya bayyana cewa manufar daukar ciki da haihuwa da abin da za'a haifa ya kasance da koshin lafiya shi da mahaifiyarsa, babu banbanci cikin kasantuwa abin da aka haifa mace ko namiji muhimmi shi ne nauyaya kan kasa da masu fadin kalmar la'ilaha illallah mace saliha ta fadi kalmar ko namiji salihi babu banbanci sune jigon tarbiyya ingantatta da hukumar addini da takawa da ayyuka nagari da ilimi mai alfanu cikin dangi da al'umma.

Cikin wannan ma'ana akwai nassosi masu tarin yawa zamu dan kawo kadan daga cikinsu don gudun tsawaitawa:

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : البنات حسنات والبنون نعمة ، والحسنات يثاب عليها ، والنعمة يُسأل عنها

1 – an karbo daga imam sadik (as) ya ce: su `ya`ya mata kyawawan ayyuka ne, su kuma maza ni'ima ne , kyawawan ayyuka ana bada lada kansu, ita kuma ni'ima ana tambaya kanta.

بُشّر النبيّ (صلى الله عليه وآله) بابنة ، فنظر في وجوه أصحابه فرأى الكراهية فيهم ، فقال  : ما لكم  ؟ ريحانة أشمّها ورزقها على الله

2 – an yiwa annabi (saw) bushara da `ya mace sai ya kalli fusaken sahabbansa sai ya ga ba sa son abin da aka yi masa bushara da shi, sai ya ce: me ya same ku ne ? fure ne da na ke shakar kamshinsa arzikinta na wurin Allah.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : نعم الولد البنات المخدّرات ، من كانت عنده واحدة جعلها ستراً له من النار ، ومن كانت عنده اثنتان أدخله الله بهما الجنّة ، وإن كنّ ثلاثاً أو مثلهن من الأخوات وضع عنه الجهاد والصدقة

3 – manzon Allah (saw) ya ce : madalla da `ya`ya mata masu suturce kansu, duk wanda ke da kwaya daya Allah zai sanya ta gare shi hijabi daga wuta, wanda kuma ya ke da biyu Allah zai shigar da shi aljanna albarkacinsu, idan sun kasance uku ko misalinsu daga `yan'uwa mata Allah zai dauke jihadi da sadaka daga kansa.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : خير أولادكم البنات

4 – manzon Allah (saw) ya ce : mafi alherin `ya`yayenku `ya`ya mata.

قال عمر بن يزيد للإمام الصادق (عليه السلام)  : إنّ لي بنات ، فقال له  : لعلّك تتمنّى موتهن ، أما إنّك لو تمنّيت موتهن ، ومتن لم تؤجر يوم القيامة ، ولقيت ربّك حين تلقاه وأنت عاص

5 – umar dan yazid ya cewa imam sadik (as) lalle ni ina da `ya`ya mata, sai imam ya ce masa: ta yiwu kana fatan mutuwarsu, idan suka mutu Allah ba zai baka lada ba ranar kiyama, sannan zaka gamu da ubangijinka alhalin ka na mai sabo.

وروي عن حمزة بن حمران ، بإسناده ، أ نّه أتى رجل النبيّ (صلى الله عليه وآله) وعنده رجل فأخبره بمولود له فتغيّر لون الرجل ، فقال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : ما لك  ؟ فقال  : خير . قال  : قل . قال  : خرجت والمرأة تمخض ـ  أي تريد وضع حملها  ـ فاُخبرت أ نّها

ولدت جارية ـ  أي بنتاً  ـ فقال له النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : الأرض تقلّها والسماء تظلّها والله يرزقها ، وهي ريحانة تشمّها ، ثمّ أقبل على أصحابه فقال  : من كانت له ابنة واحدة فهو مقروح ، ومن كان له ابنتان فيا غوثاه ، ومن كان له ثلاث بنات وضعه عنه الجهاد وكلّ مكروه ، ومن كان له أربع بنات فيا عباد الله أعينوه ، يا عباد الله أقرضوه ، يا عباد الله ارحموه

 

6 – an rawaito daga hamza dan hirana da isnadinsa, cewa wani mutum ya je wajen annabi (saw) dai dai lokacin da annabi (saw) ya ke tare da wani sai wannan wanda ya zo ya baiwa wanda ke zaune labarin haihuwar matarsa take fuskarsa ta turnuke ta canja, sai annabi (saw) ya tambaye shi me ya faru da kai ? sai ya ce babu komai, sai annabi (saw) ya ce masa ka fada, sai ya ce na fito alhalin mata ta tana nakuda to shi ne yanzu aka bani labarin cewa ta haifi mace, sai annabi (saw) ya ce: `ya mace kasa na daukarta sama na lullubeta da inuwa Allah na azurta ta, ita fure ce da zaka dinga shakar kamshinta, sai ya fuskanci sahabbansa ya ce: duk wanda ke `ya guda daya ya na da ciwo, wanda ya ke da guda biyu ya na bukatar tallafi da kawo masa dauki, wanda ke da guda uku an dauke masa jihadi da dukkanin abin ki, wanda kuma ya ke da guda hudu ya ku bayin Allah ku tausaya masa ku taimake shi ku bashi rance.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : من عال ثلاث بنات أو ثلاث أخوات وجبت له الجنّة ، قيل  : يا رسول الله واثنين  ؟ قال  : واثنين ، قيل  : يا رسول الله وواحدة  ؟ قال  : وواحدة

7 – a wani wajen kuma (saw)  ya ce: duk wanda ya ciyar da `ya`ya mata uku aljanna ta wajaba gare shi, sai aka ce ya manzon Allah wanda ya ke da guda biyu fa ? sai ya ce: shi ma ta wajaba gare shi, aka kara cewa wanda ke da guda daya fa ? ya ce: shi ma ta wajaba gare shi.

Wannan duka cikin falalar `ya`ya mata kenan, don a san cewa muhimmi bawai kasantuwar abin da ka Haifa ya zama na miji ba shi ne kawai abin bukata ba, muhimmi shi ne abin da ka Haifa ya zamanto cikin koshin lafiya kamar yanda ya zo cikin littafin almahasin:

كان عليّ بن الحسين زين العابدين (عليه السلام) إذا بُشّر بولد لم يسأل أذكر هو أم اُنثى ، بل يقول  : أسويّ  ؟ فإذا كان سويّاً ـ  أي لا عيب فيه ويخرج بسلامة  ـ قال  : « الحمد لله الذي لم يخلقه مشوّهاً

8 – ali dan husaini zainul abidin (as) ya kasance idan an yi masa bushara da abin haihuwa ba ya tambayar shin namiji ko mace ce, kadai dai ya na tamabayar shin ya na cikin koshin lafiya bai da wata nakasa? idan aka ce masa na'am, sai ya ce: godiya ta tabbata ga Allah wanda bai halicce shi da muni ba.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إنّ الله تعالى على الإناث أرأف منه على الذكور وما من رجل يدخل فرحة على امرأة بينه وبينها حرمة إلاّ فرّحه الله يوم القيامة

9 –  manzon Allah (saw) ya ce: lalle Allah madaukaki ya na tausayawa `ya`ya mata fiye da yadda ya ke tausayawa maza, babu wani namiji da zai farantawa mace wadda tsakaninsu akwai haramcin aure face Allah ya faranta masa ranar alkiyama.

الكافي  : عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : نِعمَ الولد البنات ملطفات مجهّزات ـ  أي مهيّات الاُمور  ـ مؤنسات مباركات مفليّات

10 -  alkafi : daga baban abdullah (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: madalla da `ya`ya mata masu tausayi, masu shirya al'amari, masu debe haso masu albarka.

عن الجارود بن المنذر قال  : قال لي أبو عبد الله (عليه السلام)  : بلغني أ نّه ولد لك ابنة فتسخطها ، وعليك منها ريحانة تشمّها وقد كفيت رزقها وقد كان رسول الله أبا بنات

11 – daga jarud dan munzir, ya ce: baban Abdullah (as) ya ce mini : labari ya iso mini cewa ka na da `ya mace amma ka na bakanta mata rai, ka na da fure daga gareta wanda zaka dinga shakar kamshinsa kuma hakika waninka ya dauke maka arzikinta hakika manzo Allah ya kasance uba ga `ya`ya mata.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : إنّ إبراهيم (عليه السلام) سأل ربّه أن يرزقه ابنة

تبكيه وتندبه بعد موته

12 – an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce: lalle Ibrahim (as) ya roki ubangijinsa da ya azurta shi da `ya mace wadda za ta dinga kukan rashinsa bayan mutuwarsa.

الكافي بنسده عن الكرخي عن ثقة من أصحابنا قال  : تزوّجت بالمدينة فقال لي أبو عبد الله (عليه السلام)  : كيف رأيت  ؟ قلت  : ما رأى رجل من خير في امرأة إلاّ وقد رأيته فيها ولكن خانتني ، فقال  : وما هو  ؟ قلت  : ولدت جارية ، قال  : لعلّك كرهتها إنّ الله تعالى يقول  : (  آباؤُكُمْ وَأبْناؤُكُمْ لا تَدْرونَ أ يّهُمْ أقْرَبُ لَكُمْ نَفْعا[3]ً

13 – alkafi da isnadinsa daga karaki daga yardaddu daga sahabban mu ya ce: na yi aure a madaina sai baban Abdullah (as) ya ce mini: ya ya ka gani ? sai n ace: banga wani alheri daga namiji face na ganshi cikin mace sai dai cewa ta ha'ince ni, sai imam ya ce: menene ? sai na ce ta haifi `ya mace, sai imam ya ce: ta yiwu kai baka sonta lalle Allah madukaki na cewa:

babanninku da `ya`yayenku ba ku san wadanda su ka fi kusa da  alfanu gareku ba.

 ma'ana iyayenku da `ya`yayenku ba ku san gwargwadon alfanunsu gareku ba kuma baku san cikinsu wane ne ya fi alfanu ba, haka al'amarin ya ke cikin `ya`ya maza da `ya`ya mata ta yiwu mace ta fi amfani ga iyayenta daga da namiji, ta yiwu da namji ya fi cutarwa ga iyayensa daga `ya mace, ya kamata miji da mata su yarda da abin da ubangiji ya zaba musu ya azurta su da shi mace ne ko namiji babu banbanci.

 الكافي بسنده عن الحسن بن سعيد اللحمي قال  : ولد لرجل من  أصحابنا جارية فدخل علي أبي عبد الله (عليه السلام) فرآه متسخّطاً فقال له أبو  عبد  الله (عليه السلام)  : أرأيت لو أنّ الله أوحى إليك أن أختار لك أو تختار لنفسك ما  كنت تقول  ؟ قال  : كنت أقول يا ربّ تختار لي ، قال  : فإنّ الله قد اختار لك ثمّ قال  : إنّ الغلام الذي قتله العالم الذي كان مع موسى (عليه السلام) وهو قول الله عزّ وجلّ  : (  فَأرَدْنَا أنْ يبدلهما ربّهما خيراً منهُ زكاةً وأقرب رُحماً  ) أبدلهما الله به جارية ولدت سبعين نبيّاً

14 – alkafi – da isnadinsa daga hassan dan said   ya ce: an haifarwa daya daga cikin sahabban mu `ya mace, sai ya shiga wajen  baban abdullah  (as) sai imam ya ganshi cikin fushi sai imam ya ce masa: shin da Allah zai aiko maka da wahayi kan ya zabar maka ko kuma kai ka zaba da kanka me za ka ce? sai ya ce: zance ya ubangiji ka zabar mini, imam ya ce: lalle yaro nan wanda wannan malami da  ke tare da annabi musa (as) cikin tafiyarsu ya kashe, cikin fadin Allah madaukaki:

sai mu ka nufi ubangijinsu ya sauya musu ga  mafi alheri daga gare shi da zai zama tsarkakuwa  da mafi kusanta da tausasawa.

 sai Allah ya sauya musu da `ya mace wacce ta haifi annabawa har guda saba'ain.

الفقيه عن الصادق (عليه السلام) قال  م من عال ابنتين أو اُختين أو عمّتين أو خالتين حجبتاه من النار ـ  من أعال أي أنفق وتكفّل بحياتهما المعيشيّة  ـ

15 – alfakihu  daga sadik (as) wanda ya ciyar da `ya`ya biyu mata ko `yan'uwansa mata biyu ko goggwaninsa biyu ko `yan'uwan mahaifiyarsa biyu za su yi masa hijabi daga wuta.

الفقيه  : قال (عليه السلام)  : إذا أصاب الرجل ابنة بعث الله عزّ وجلّ إليها ملكاً فأمرّ جناحه على رأسها وصدرها وقال  : ضعيفة خلقت من ضعف ، المنفق عليها مُعان[4]

16 – alfakihu sadik (as) ya ce: idan aka haifawa mutum `ya mace Allah ya na aiko da mala'ika zuwa gareta ya shafa fuffukensa kanta da kirjinta ya ce rarrauna an halicceta daga rauni, duk wanda ya ciyar da ita Allah zai taimake shi.[1] Takwir:9-8

[2] Annahl:58

[3] Bakara:216

[4] Alwafi m 12 sh 1306