فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA

 

A dabi'ace uban na son ya ga dansa ya yi kama da shi cikin surarsa, don ya zama da zarar matne sun ganshi sai su tuna da babansa, mutum zai dinga jin cewa kamar ta hakan zai zama ya samu wanzuwa kenan, ya kuma cika nakastuwarsa ta rashin kasantuwarsa wanzazze ko da kuwa cikin wahami ne saboda dan adam a dabi'ance na son wanzuwa wadda daya ce daga halittarsa.

Ya zo a riwaya cewa kamanceceniya da mahaifi siffa ce mai kyawu, sai dai cewa rashinta ba ya nufin nakastuwa ga da, gaskiya ne cewa duk wanda ya yi kama da mahaifinsa bai yi laifi ba, sai hakan bay a nufin cewa wanda bai yi kama da mahaifinsa ba ya yi laifi  , babu wani lazimci cikin haka, saboda tabbatar da haka ne muka samu riwaya mai daraja na nassanta al'amura biyu, kamanceceniya duk da kasantuwarta abu mai kyawu sai dai rashinta bai nuni ga muni ko ha'inci da dai makamantansu.

عن الصادق (عليه السلام)  : من نِعَم الله عزّ وجلّ على الرجل أن يشبهه ولده

1 – sadik (as) daga cikin ni'imar Allah ga mutum dansa ya yi kama da shi.

وعنه (عليه السلام) ، قال  : إنّ الله تبارك وتعالى إذا أراد أن يخلق خلقاً جمع كلّ صورة بينه وبين آدم ، ثمّ خلقه على صورة إحداهن ، فلا يقولن أحد لولده هذا لا يشبهني ولا يشبه شيئاً من آبائي

2 – daga gare shi (as) ya ce: Allah madaukaki idan ya yi nufin halittar halitta sai ya tattara  dukkanin sura tsakaninsa da tsakanin adam, sai ya halicce shi kan sura daya daga ciki, ka da wani ya sake ya cewa dansa wannan bai kama da ni bai dauko kamar komai daga iyayena.

وسأل رجل عن النبيّ (صلى الله عليه وآله) فقال  : ما لنا نجد بأولادنا ما لا يجدون بنا  ؟ قال  : لأ نّهم منكم ولستم منهم

3 – wani mutum ya tambayi annabi (saw) me ya sa muke samun daga `ya`yan mu abin da su ba sa samu cikin mu ? sai ya ce masa: saboda su daga gareku suke amma ku ba daga garesu kuke ba.

من كتاب المحاسن ، عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : من سعادة الرجل أن يكون الولد يعرف بشبهه وخَلقه وخُلقه وشمائله ـ  وهذا يعني أنّ الوالد لا بدّ أن يكون متخلّقاً أوّلا بأخلاق الإسلام وله شمائل أهل الخير والصلاح 

4 – daga littafin almahasin, daga imam sadik (as) ya ce: daga cikin azurtar mutum ya zma dansa ya yi kama da shi cikin halittarsa da dabi'unsa.

Wannan na nufin kenan ya zama dole uba ya yi ado da kyawawan dabi'u.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : إنّ الله عزّ وجلّ خلق للرحم أربعة أوعية فما  كان في الأوّل فللأب وما كان في الثاني فللاُم ، وما كان في الثالث فللعمومة ، وما كان في الرابع فلخؤولة                                  

5- an karbo daga baban Abdullah  (as)  Allah mai girma da daukaka ya halicci wurare hudu cikin mahaifar mace, na farko zai zama ga uba, na biyu uwa, na uku ga baffanu, na hudu ga `yan 'uwan uwa.

ta yiwu abin da ake nufi da wadannan mazubai shi ne digon maniyyi idan ya zauna a matsuguni na farko to yaro zai kama da mahaifinsa, haka al'amarin ya ke ga ragowar.

عن أبي الحسن (عليه السلام) قال  : سمعته يقول  : سعد امرؤ لم يمت حتّى يرى خلفاً من نفسه

7 – daga baban hassan (as) ya ce: na ji shi ya na cewa: mutumin da ya ga magajinsa gabanin mutuwarsa ya azurta.