فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

MATAKAN TARBIYYYAR YARA

 

sakamakon kasantuwar mutum da gangar jiki da ruhi, hakika an sanyawa kowanne daya cikinsu wanda zai tarbiyantar da shi da kara masa girma da lura da shi, akwai wasu abubuwa da ke sanya  tarbiyya ga ruhi, haka akwai na gangar jiki, sannan ita kanta tarbiyya tare da dukkanin kasha kashenta ta na da lokaci n agama gari da kebantacce, sakamakon kasuwar ilimi zuwa kasha biyu: ilimin zukata (wanda ba ta koyo ake samunsa ba) da wanda ake tsiwirwira (koyo ) kashin farko shi ne wanda riwaya ke cewa: ilimi baI kasance daga yawan koyo ba, kadai dai ilimi haske ne da Allah ke sanya cikin zuciyar wanda ya so ya shiryar da shi.

Koyo da tarbiyya ta hanyar ilimin zuciya da ruhi kadai dai na kasancewa tsawon rayuwa ba ya kebanta da zamani koma bayan wani zamani ya na kasancewa tun daga zani shimfidarsa bayan haihuwa har zuwa kabari, amma ilimin koyo lalle koyansa ga yaro karami kamar zane ne kan dutse koyansa kuma bayan an rigaya an girma to kamar zane ne kan teku, akwai wasu sunnoni na musammam ga koyo da tarbiyyar ruhi da ta jiki kamar misalin wasannin motsa jiki, sannan waccan magana ta cewa karatun babba kamar zane kan teku hakan ba ya nufin cikin kowanne hali sai dai galibin lokuta haka al'amarin duk da cewa an samu wasu mutane da su kayi karatu a shekarunsu na karshen rayuwa sannan suka kai manya-manyan  mukaman ilimi.

malaman tarbiyyar ruhi sun ambaci wasu kebantattun daurori, shi mutum ana iya yi masa tarbiyya har zuwa kai wa shekaru arba'in, sannan ana far tarbiyyarsa tun ya na shekaru bakwai.

muslunci na batu da kebantacciyar mahanga kan haka , a bayyane yak e duk sanda wani abu ya yi karo da abin da muslunci ya zo da shi ana gabatar da abin da muslunici ya kawo kan wancan, lalle abin da wahayi ya zo da shi a fadake yak e da dukkanin sirrinka dan adama da badininsa, Allah ne ya halicce shi kuma ya san hakikaninsa da dukkanin abin da zai amfanar da shi da wanda zai cutar da shi da yadda ya kamata tarbiyyarsa da koyansa su kasance, annabi (saw) ya zo don ya tsarkake dan adam ya kuma koyar da shi littafi da hikima. sannan dangane da tarbiyyar yara hakika ya sanya marhaloli uku:

na farko: a kyale yaro ya dauki duk abin da yak e sha'awa matukar dai baza cuatar da shi ba domin shi yaro a daurar yarintarsa jin kansa kamar basarake, sai a dinga ba shi abin da dukkkanin ransa ke so matukar dai babu cutarwa da asara, ya zama tilas abar masa `yancinsa  ya yi yadda ya ke so, sannan  shi yaro idan ba'a bashi damar nuna mulkinsa ba da sannu cikin marhala mai zuwa zai nuna dagawarsa da ya boye cikin zuciyarsa.

ta biyu: da'a a ladabtarsa shi wannan lokaci ya zama ya na jin magana da da'a gadukkanin abin da aka sashi saboda a banshi dukkanin damar yin yadda ya so a marhalarsa ta farko yanzu kuma lokaci yay i shi da zai zama bawa ya kuma zama tilashinsa yay i da'a ga babban malamin sa mai yi msa tarbiya wato uba.

ta uku : wazirci bawa ya nade marhaloli biyu ya tsiwirwiri ilimi da gogewa kwakwalwarsa ta bude hankali ya girma, lalle zai zamanto cikin hukuncin waziri ga mahaifinsa, saboda haka kamata mahaifi ya dinga neman shawara daga gare shi cikinal'amuran rayuwar yau da gobe da batutuwan iyali, har da ya zma ya na dogaro da kankin kansa ya zma ya na jin knsa cikakken mutum  da cewa shi ma ya na da samuwa cikin iyalin da zma ana karbar shawararsa ta gari, da wannan wazirci zamu gane cewa rayuwa a wannan lokaci ta koma ryuwar demokaradiyya, ka da uba ya zama dan mulkin fin karfi da kama karya da nuna fin ikonsa cikin kowanne hali, bari dai kamat ya yi ya dinga shawartar iyalinsa misali idan ya nufi yin tafiya tare da iyali don shakatawa ko kuma wata ziyara to sai ya bijiro da batun garesu  ya ji ra'ayin kowa da ga cikinsu da yadda  ya kamata ace tafiya ta kasance da tsawo lokacin da zata ci da dukkanin abin da ya rataya da ita, wannan marhala ta wazirci da in shawara da iyali ba ta kore matsayinsa da tsayuwarsa kan mata kamar yadda bayanin haka ya gabata, hakan shine ma'ana tsayuwa kan mata da kula nauyin da yah au kansa daga iyali.

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : الولد سيّد سبع سنين ، وعبد سبع سنين ، ووزير سبع سنين . فإن رضيت أخلاقه لإحدى وعشرين ، وإلاّ فاضرب على جنبه ، فقد أعذرت إلى الله تعالى

1 – annabi (saw) ya ce: da shugaba ne na shekaru bakwai, bawan shekaru bakwai, wazirin shekaru bakwai, idan ka gamsu da dabi'unsa a shekaru ishirin da daya idan kuma ba ka gamsu ka doki kan kwibinsa, lalle ka sauke nauyin da ya hau kanka wurin Allah.

 ma'ana idan kayi aiki da abin da nauyin da ke kanka na tarbiyyarsa cikin wadannan shekar ishirin da daya cikin marhaloli uku ta kuma ka gamsu da kyawun dabi'arsa to madallah, idan kuma baka gamsu ba to dai ka riga ka sauke nauyin da yahau kanka wurin Allah.

عن الصادق (عليه السلام)  : دع ابنك يلعب سبع سنين ، ويؤدّب سبعاً ، وألزمه نفسك سبع سنين ، فإن فلح ، وإلاّ فلا خير فيه

2 – an karbo daga sadik (as) ka kyale danka ya yi wasa  zuwa  shekaru bakwai, a kuma ladabtar da shi shekaru bakwai, ka lazimce shi shekaru bakwai zai rabauta idan kuma bai rabuta ba to babu alheri cikinsa.

وقال (عليه السلام)  : احمل صبيّك حتّى يأتي عليه ستّ سنين ، ثمّ أدّبه في الكتاب ستّ سنين ، ثمّ ضمّه إليك سبع سنين فأدّبه بأدبك ، فإن قبل وصلح ، وإلاّ فخلّ عنه

3 – imam (as) : ka kyale danka zuwa shekaru bakwai, sannan ka ladabtar da shi cikin littafi shekaru shida, sannan ka jawo jiki shekaru bakwai ka ladabtar da shi da ladabinka, idan ya karbi ladabinka gyaru ya ladabtu  idan kuma bai ladabtu ba to kayi watsi da shi.

ورد في حديث أمير المؤمنين (عليه السلام)  : أدّبوا أولادكم بآداب زمانهم ، فإنّهم خلقوا لزمان غير زمانكم

4 – abin da aka rawaito daga sarki muminai al (as) bai buya ba cikin fadinsa: ku ladabtar da yaranku da ladubban zamaninsu, lalle su an halicce zamanin da  ba na ku ba.

 ita wannan riwaya ba kore yiwa yaro tarbiyya da da tarbiyyarka sai dai z aka yi masa ne gwargwadon yadda ta da ce da zmanin da yak e ciki, lalle ladubban muslunci tun daga zamanin annabi (saw) har zuwa ranar alkiyama ladubba ne guda daya, sune ladubban da tauhidi da sunnonin annabta ke tajalli ciki, yaro ya girmama babba na tsaye ya yiwa na zane sallam, a wanke hannuwa gabanin cin abinci da dai makamantan hakadaga ladubba da sunnonida halayyar annabta mai daraja, lalle it aba kebanta da wani zamani banda wani, na'am koyarwa a zamanin da ana yinta kan allo amma yanzu kan injin komfuta, tarbiyya da koyarwa sune cikin kowanne zamani sai dai hanyar koyar da su ta kan dan banbanta cikin kowanne zamani.

muslunci ya yi wasicci kan tarbiyyar yara matukar wasicci.

عن النبيّ (صلى الله عليه وآله) ، قال  : لأن يؤدّب أحدكم ولده خيرٌ له من أن يتصدّق بنصف صاع كلّ يوم

5 – annabi (saw) ya ce:  dayanku ya yiwa dansa tarbiyya shi ya fi alheri daga ya ciyar da rabin kwano cikin kowacce rana.

وعنه (عليه السلام)  : أكرموا أولادكم وأحسنوا أدبهم يغفر لكم

6 – daga gare shi (saw) : ku karrrama yaranku ku kyautata tarbiyyarsu Allah zai muku gafara.

عن الرضا (عليه السلام) ، قال  : قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : اغسلوا صبيانكم من الغَمَر ـ  زنخ اللحم وما يتعلّق باليد من دسومة  ـ فإنّ الشيطان يشمّ الغمر فيفزع الصبي في رقاده ـ  أي يؤذيه في نومه  ـ ويتأذّى به الكاتبان ـ  الملكان عن اليمين والشمال 

7 – ankarbo daga rida (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: ku wanke hannayen yaranku daga karnin nama, lalle shaidani na sansana ya dinga firgita yara yayin da suke barci. Sannanh mala'iku bbiyu masu rubuta sharrda Alherinsu na takuruwa.

 

Daga hadisai wadanda suka tattaro komai gameda tarbiyya har zuwa cika shekaru arba'in:

عن أمير المؤمنين عليّ (عليه السلام) ، قال  : يرخى الصبي سبعاً ـ  أي دعه يلعب واحمله وإنّه سيّد نفسه  ـ ويؤدّب سبعاً ـ  كما يؤدّب العبد  ـ ويستخدم سبعاً كوزير يستشار ويحمل قسماً من ثقل الاُسرة في المعاش وغيره ـ  وينتهي طوله في ثلاث وعشرين وعقله في خمس وثلاثين  ـ أي إلى هذا السن يستوعب العقل المعلومات الواردة ـ  وما كان بعد ذلك فبالتجارب  ـ والتجربة أكبر برهان وفوق العلم

8 – an karbo daga sarkin muminai alim (as) ya ce: a kyale yaro zuwashekaru bakwai ma'anaa barshi yay i wasa da nishadinsa, sannan a ladabtar da shi shekaru bakwai, sannan a sanya shi hidimakamar waziri shekaru bakwai ya zamanto ana shawartarsa a na dan dora masa nauyi daga bukatun iyali har shekarunsa sukai ishirin da uku, sannan hankalinsa zai kammala cikin shekaru talatin da hudu. sannan kadai dai zai dinga tarbiyyar dansa kan ayyukan kirki da da imanii da tauhidi tun farkon fitar faratansa.

عن أبي عبد الله أو أبي جعفر (عليهما السلام) ، قال  : سمعته يقول  : إذا بلغ الغلام ثلاث سنين فقل له سبع مرّات  : لا إله إلاّ الله  ، ثمّ يترك حتّى يبلغ ثلاث سنين وسبعة أشهر وعشرين يوماً ، ثمّ يقال له  : قل « محمّد رسول الله » ، سبع مرّات ، ويترك حتّى يتمّ له أربع سنين ثمّ يقال له سبع مرّات قل  : صلّى الله على محمّد وآل  محمّد ـ  أي في أوّل الأمر يعلّم التوحيد ثمّ النبوّة ثمّ الإمامة والولاية المتمثّلة بآل محمّد (عليهم السلام)  ـ ويترك حتّى يتمّ له خمس سنين ، ثمّ يقال له  : أ يّهما يمينك وأ يّهما شمالك ، فإذا عرف ذلك حوّل وجهه إلى القبلة ويقال له  : اسجد ثمّ يترك حتّى يتمّ له ستّ سنين ، فإذا تمّ له ستّ سنين قيل له  : صلّ وعُلّم الركوع والسجود حتّى يتمّ له سبع سنين ، فإذا تمّ له سبع سنين قيل له  : اغسل وجهك وكفّيك ، فإذا غسلهما قيل له  : صلّ ، ثمّ يترك حتّى يتمّ له تسع سنين ، فإذا تمّت له عُلّم الوضوء وضرب عليه ، واُمر بالصلاة وضُرب عليها ـ  فيما إذا أراد أن يتماهل أو يتكاسل فيها  ـ فإذا تعلّم الوضوء والصلاة غفر الله لوالديه إن شاء الله

9 – an karbo daga baban abdullah (as) ya ce: na ji shi yana fadin: idan yaro ya girma ya kai shekaru uku to a karanta masa(la'ilaha-  illAllah ) kafa bakwai har zuwa kaiwarsa shekaru uku da watanni bakwai da kwanaki ishirin, sannan akaranta masa  ( muhammadu rasulillah ) kafa bakwai sai a kyale shi har zuwa kammala shekaru hudu, sannan a karanta masa ( sallallahu a la muhammadu wa'ali muhammadu (as) sannan a sake kyale shi har zuwa kammala shekaru biyar, sai a tambaye shi wanne bangare ne damanka wanne bangare ne hagu, idan ya banbance sai a juya fuskarsa zuwa alkibla a ce masa: yi sujjada, idan ya kai shekaru shida sai ace masa:  sai a koya masa ruku'u da sujjada ace masa yi sAllah har ya zuwa cika shekaru bakwai iadan ya kammal shekaru bakwai sai ace masa: wanke fuskarka da tafin hannuwanka ka yi sallah, sai kyale shi har zuwa cika shekaru tara, bayan cika shekaru tara sai a koya masa alwala da taimama a uarce shi da yin sallah a kuma dake shi iadan ya barta, idan ya zamanto ya iya alwala da sallah ubangiji zai gafarta ma iyayensa da yardarsa.

وما أجمل ما يقوله الإمام السجّاد في رسالة الحقوق في بيان جملة من حقوق الولد ، فقال (عليه السلام)  : وأمّا حقّ ولدك ، فأن تعلم أ نّه منك ومضاف إليك في عاجل الدنيا بخيره وشرّه ، وأ نّه مسؤول عمّـا وليته به من حسن الأدب والدلالة على ربّه عزّ وجلّ والمعونة له على طاعته ، فاعمل في أمره عمل من يعلم أ نّه مثاب على الإحسان إليه ، معاقب على الإساءة إليه

10 – me ya fi kyawu daga abin da imam sajjad (as) ke cewa cikin wasikarsa ta hakkoki cikin bayanin jumlar hakkokin da ya na cewa: amma hakkin danka ka sani cewa shi daga gareka yak e gareka ake jingina shi cikin duniya sharrinsa da alherinsa, sannan abin tambaya ne kan abin da kajibanta masa daga kyawawan ladudda da shiryar da shi zuwa ga ubangijinsa da taimakonsa cikin biyayyarsa, ka yi aiki tukuru cikin al'amarinsa irin aikin wanda zai san cewa shi zai samu lada kan kyautatawar da ya yi zuwa gare shi, da ukuba kan munanawa zuwa gare shi.

Lalle idan aka zurfafa gani cikin ayoyin alkur'ani da hadisai masu daraja da suka zo daga annabi da iyalnsa (as) da kuma bincika tarihi da abin yau da gobe suka nuna dukkaninsu sun tabbatar da cewa uwa d uba na babbar gudummawa da tasiri kai tsaye cikin makomar rayuwar yaransu, munga tasirin da iyaye ke da shi kna mokomar rayuwar yaransu cikin marhaloli daban-daban tun daga haihuwarsu zuwa yarintarsu zuwa marhalar samartaka, babu banbanci cikin kasantuwar makomarsu ta tsiwirwiri launi arziki ko na tabewa, yayin da alkur'ani da hadisi ke karfafa kasantuwar iyaye sun lazimci ginshikan rayuwar muslunci da kasantuwa sun kula da yaransu da basu tarbiyya da kulawa ta musammam, kadai iyaye ke jagorantar makomar yaransu wadda ke ciki da haske da arziki, da sama musu ni'imtacciya rayuwa, amma iyayen suka kaucewa ginshikan addini rayuwar ke gudana cikin ko sakaci da ko in kula da kuma yin kasala wajen tarbiyyantar da yaransu kan koyarwar muslunci, lalle suna tasiri wajen gurbata makomar rayuwa yaransu, suna sanya su karan bara ga dukkanin karkacewa da bata daga hanyar gaskiya.

Hadisi ya zo daga annabi (saw) ya na cewa: mai arziki shi ne wanda ya azurta tun daga cikin mahaifiyarsa, matsiyaci shi ne wanda ya tsiyata tun daga cikin mahaifiyarsa.

A cikin wata riwayar wata ranamanzon Allah (saw) tare da wani adadi daga sahabbansa ya wuce ta gefen wasu yara suna wasa sai ya kale su y ace: ya ku yaran karshen zamani su waye iyayensu ? sai aka ce masa: daga cikin iyayensu akwai mushrikai, sai ya ce:  wadanda iyayensu suke muminai wadanda ba su koya musu komai daga farilla ba, idan yaransu  suka tafi koyon ilimi sunfi farin ciki su ga yaran suna neman dukiya duk da cewa abin da suke samu kadan ne bai tka kara ya karya ba, sai ya zamanto  yaran suna tsananin kin wadannan iyaye na su, sai ya ce: ni na barranta daga wadannan iyaye su ma sun barranta daga gareni.