فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

ADALCI TSAKANIN `YA`YA

 

Adalci shi ne ajiye abu a muhallinsa dabaiwa ma'abocin hakki hakkinsa kamar yadda hankali da ma'bocinsa ya fassara da haka, duk mai hankali adali ne duk adali ma'abocin hankali ne, ta yiwu ya zama daga cikin ma'anar adalci shi ne daidaito tsakanin mutane da abubuwa muslunci ya himmatu da batun adalci matukar himmatu, musammam ma mabiya mazhabar ahlul baiti (as) sun tafi kan cewa daga cikin asalan addini akwai imani da adalcin Allah matsarkaki, sabanin ragowar mazhabobin musulmi misalin ash'arawa kamar yaddda aka ambace shi cikin littafansu na ilimin tauhidi (kalam).

Daga cikin abubuwa da ke bayyanar da adalcin ubangiji shi ne: adalci cikin zamantakewa daga cikinta shi ne ya zamanto duk wani muslmi da musulma sun siffantu da adalci saboda kishiyarsa shi ne fasikanci ko dai mutum ya zamanto adali ko kuma fasiki , wannan ma'ana ta zo cikin ilimin fikihu da usul, kamar yadda ta zo cikin alkur'ani:

 [1] إنْ جَاءَكُمْ فَاسِقٌ بِنَبَأ فَـتَـبَـيَّـنُوا 

  idan fasiki ya zo muku da labara ku bincika.

 Ana kafa hujja da wannan kan hujjiyar mutum sika wanda bai karya da ma'anar idan adali ya zo muku da labari ka da ku yi bincike, wani lokacin azzalumu na zama kishiyar adali ko fasiki.

Wajibi ga iyaye su kiayae adalci tsakanin `ya`yayensu.

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : اعدلوا بين أولادكم ( في السرّ ) كما تحبّون أن يعدلوا بينكم في البرّ واللطف

1 – manzon Allah (saw) ya ce: kuyi adalci tsakanin `ya`yanku kamar yadda ku ke so su yi muku adalci cikin kyakkyawan aiki da ludufi.

Daga cikin adalci shi ne cika alkawali da soyayya da tausayi.

عن النبيّ (صلى الله عليه وآله) ، قال  : أحبّوا الصبيان وارحموهم ، فإذا وعدتموهم ففوا لهم ، فإنّهم لا يرون إلاّ أ نّكم ترزقونهم

2 – an karbo daga annabi (saw) ya ce: ku nuna soyayya ga kananan yara ku tausaya musu, idan ku ka yi musu alkawali ku cika lalle su babu abin da suke gani face cewa dai kuna azurta su.

عن رفاعة ، قال  : سألت أبا الحسن (عليه السلام) عن الرجل يكون له بنون واُمّهم  ليست بواحدة ، أيفضّل أحدهم على الآخر  ؟ قال  : نعم ، لا بأس به ، قد كان أبي (عليه السلام) يفضّلني على أخي عبد الله

3 – an karbo daga rafa'atu, ya ce: na tambayi baban hassan (as) kan mutumin da ya ke da `ya`ya amma uwayensu daban-daban, shin zai fifita daya  kan dayan? sai ya ce: babu laifi cikin yin haka, hakika babana ya kasance ya na fifitani kan dan'uwana abdullah.

fifiko na kasancewa da ilimi da kyawawan dabi'u da ayyuka nagari kamar yadda ya ke bayyane, ba da abubuwa marasa daraja ba wadanada basu da asali cikin addini da mutumtaka, kamar misali ace dayansu ya fi tsayi, sai a fifita shi kan dan'uwansa saboda tsayinsa,  ire iren wadannan ma'aunai basu da wata kima basu bubbugo daga lafiyayyen hankali da shari'a tsarkakka.

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : من دخل السوق فاشترى تحفة فحملها إلى عياله ، كان كحامل صدقة إلى قوم محاويج ، وليبدأ بالإناث قبل الذكور ، فإنّ من فرّح ابنته فكأ نّما أعتق رقبة من ولد إسماعيل ، ومن أقرّ عين ابن فكأ نّما بكى من خشية الله ، ومن بكى من خشية الله أدخله الله جنّات النعيم

4 – manzon Allah (saw) ya ce: duk wanda ya shiga kasuwa ya sayo hadaya ya kaiwa iyalinsa, zai kasance kamar wanda ya dauki sadaka ya kaita ga mabukata, ya fara baiwa mata gabanin maza, lalle duk wanda ya farantawa `yarsa mace kamar misalin wanda ya `yanta baiwa  daga `ya`yan isma'il, duk wanda ya sanyaya idaniyar da namiji  kamar misalin  wanda ya yi kuka saboda tsoron Allah duk wanda ya zubar da hawaye sakamkon tsoron Allah zai shigar da shi aljanna mani'imciya.

 

 

 [1] Hujrat:6