فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI

 

Hakikadan adam ya daukaka da hankalinsa mai riska  cikin hikimar aubangiji kan dukkanin sauran  halittu, lalle hankali kyautar ubangiji ne ya sanya shi cikin mutum, don ya yi yawo cikin smaniyar falaloli da sasannin ilimai  ya daga ya kai ga kaba kausani ya kai kolloluwar kamala da girma ya kasance mazaharin sunayen Allah kyawawa da madaukakan siffofinsa, lalle shi duk sa'ilin da ya kara kamala da kyawuntaka lalle shi zai kasance mazharin ga sunan ubangiji har ya kai ga zuwa narkewa cikin Allah da zama mazharin jalaliya dukkanin sunayen ubangiji su yi tajalli cikinsa.

وَما رَمَيْتَ إذْ رَمَيْتَ وَلـكِنَّ اللهَ رَمى[1]

(( ba kayi jifa sa'ilin da kayi jifa sai dai cewa Allah ya yi jifan )

وَما يَنْطِقُ عَنِ الهَوى إنْ هُوَ إلّا وَحْيٌ يُوحى[2]

(( bai furruci da so zuciya dukkanin abin da ke furtawa wahayi ne da ake masa  ))

إنَّ الَّذينَ يُبايِعونَکَ إنَّما يُبايِعونَ الله[3]

(( lalle wadanda ke yi maka muba'a kadai dai suna yiwa Allah mubaya'a ne )

مَنْ يُطِعِ الرَّسولَ فَقَدْ أطاعَ الله[4]

 (( duk wanda ya yiwa manzo da'a hakika ya yiwa Allah da'a ))

Manzon mafi girama (saw) ya kai ga daukaka ta hanyar kamalarsa yay aye duhu da kyawunsa ya kasance mazhari mafi cika ga ubangiji wanda giramans ay girmama , jifan annabi jifan Allah ne kalaminsa kalamin Allah ne mubaya'a ga annabi mubaya'a ga Allah da'a gare shi da'a ga Allah, haka ba komai bane face ludufi daga Allah da kuma kamalar hankalinsa.

Girman mutum da daukakarsa da fifikonsa kan ragowar halittu da azurtar gida biyu kadai dai sakamakon hankalinsa ne, hankali shi e abin nan da aka bautawa ubangiji mai rahama da shi aka samu aljanna da shi ya na dakarunsa, daga cikinsu akwai kyawuntar ladabi  kamar yadda shi ma jahilci na da dakaru, daga cikindakarunsa munana ladabi, ma'abocin hankali na kasancewa mai ladabi mai ladabtarwa mai koyar da ladubba cikin sulukinsa da zantukansa da da dukkanin motsinsa da shirunsa.

ويقول أمير المؤمنين علي  7: الأدب كمال الرجل

Sarkin muminai ali (as) na cewa: ladabi shi ne kammalar da namiji.

وقال : الأدب أحسن السجيّة ، أفضل الشرف الأدب

 ladabi shi ne mafi kyawun hali, mafi daukakar daraja  ladabi.

وقال  7: خير ما ورّث الآباء الأبناء الأدب ، حسن الأدب خير مؤازرٍ وأفضل قرين

Ali (as) : mafi alherin abin da iyaye suka barwa `ya`yansu ladabi shi ne mafi alherin mai taimako mafi falalar abokin zama.

Wannan na nufin mafi alherin wanda zai taimake ka da karfafarka da abokantaka cikin tsanani rayuwa da matsalolinta mafi alherin guzuri cikin rayuwar duniya shi ne ladabi.

وقد قال الأمير  7: طالب الأدب أحزم من طالب الذهب ، ومن لم يكن أفضل خلاله أدبه كان أهون أحواله عطبه ، وإنّک مقوّم بأدبک فزيّنه بالحلم ، يا مؤمن إنّ هذا العلم والأدب ثمن نفسک فاجتهد في تعلّمها، فما يزيد من علمک وأدبک يزيد في ثمنک وقدرک

Hakika sarkin muminai ali (as) ya ce: mai neman ladabi ya fi tsanantawa daga mai neman zinariya, duk wanda bai kasance mafi falala cikinsa shi ne ladabinsa to halakarsa za ta zama mafi saukaka lalle kai mai daidaita ne da ladabinka ka kyawunta shi da yin hakuri, ya kai mumini shi wannan ilimi da ladabi shi ne jarin zuciyarka ka yi kokari cikin koyonta , duk abin da ya karu cikin iliminka da ladabinka darajarka da kimarka za su karu.

Na'am kimar kowanne mutum shi ne abin da ya ke aikatawa, ladabinsa shi ne jarinsa.

sarkin muminai ali (as) ya ce: ladabi shi ne kamalar da namiji, a wani wajen y ace : hankalinmutum tsarinsa, ladabinsa daidaitonsa, hakika bukatuwar mutane zuwa ga mutum salihi ma'abocin ladabi ta fi bukatuwarsu zuwa zinariya da azurfa, abubuwa uku babu kari kansu kansu: kyawuntar ladabi, kauracewa kokwanto, da kamewa daga haramun.

Yayin da annabi ya aika mu'azu dan jabal kasar yaman ya ce masa: ya mu'azu ka koyar da su littafin Allah ka kyawunta ladubbansu kan nagartattun halaye.

Ta yiwu mutum ya kasance mai daraja cikin matsayinsa  amma saboda munanar ladabinsa sai ya fadi daga daga idanuwan mutane, sau da yawa zaka kaskantacce cikin danginsa  sai dai cewa ya na daukaka ya shuagabanci mutane sakamakon kyawuntar ladabinsa.

ويقول أمير المؤمنين علي  7: الأدب أحد الحسبين ، وأشرف حسب حسن أدب ، وأكرم حسب حسن أدب ، وحسن الأدب أفضل نسب وأشرف سبب ، وطلب الأدب جمال الحسب ، وعليكم بالأدب فإنّه زين الحسب ، وقليل الأدب خير من كثير النسب ، وحسن الأدب ينوب عن الحسب ، ولا حسب أنفع من الأدب ، وكلّ الحسب متناهٍ إلّا العقل والأدب ، وحسن الأدب يستر قبيح النسب ، وفسد حسب من ليس له أدب

Sarkin muminai ali (as) ya na cewa: ladabi daya daga cikin matsayi biyu ne, ma fi girman darajar matsayi kyawuntar ladabi , mafi karamcin matsayi kyawun ladabi, kyawuntar ladabi shi ne mafi falala nasaba da daukakar sababi, neman ladabi shi ne kyawuntar matsayi, na hore ku da ladabi lalle shi adon matsayi ne , mai karanci ladabi ya fi alheri kan mai yawan dangi , kyawuntar ladabi na maye gurbin matsayi , babu wani matsayi da ya fi amfani daga kadabi, duk wani matsayi mai karewa ne face hankali da ladabi, kyawun ladabina suturce munanar nasaba , matsayi idan babu ladabi ya na gurbata. ladabi kan saruta ne da ke gadar da girma da shugabanci

sarkin muminai ali (as) :  babu wani ado da ya wuce ladabi, babu kaya cancada ado kamar ladaubba, ladabi kayan ado ne sababbi, ilimi gado ne na karamci, ladabi kayan ado ne masu sabunta .   

daga cikin bayyanannen al'amari shine cewa mutum na asarar girmansa da matsayinsa sakamakon munanar labinsa

sarkin muminai ali (as) babu girma tare da munanar ladabi , duk wanda ladabinsa ya karanta miyagun ayyukansa zasu yawaita, duk wanda munanar ladabinsa ta kaskantar da shi girmansa da matsayinsa ba u iya daukaka shi , Allah wadarn nasaba tare da munanar ladabi, babu ladabi ga mai mummunan kalami.

ya zamo dole a zage dantse wajen neman ladabi lalle ya zo cikin hadisi daga iyalan annabi (as) cewa an halicci rai kan munana ladabi, bawa kuma an umarce shi da lazaimtar kyawuntar ladabi, iata rain a sukuwa fagen sabo, shi kuma bawa na dagewa ya gay a dawo da ita daga barin sabo duk sanda bawa ya sakar mata ragama to shi ma ya yi tarayya cikin barnarta, duk wanda ya taimakawa son arnasa hakika ya yi tarayya cikin halaka kansa.

hankali duk da kasntuwarrsa kyauta daga Allah matsarkaka sai dai cewa ba'a wadatuwa da shi kadai a rayuwance dole nea cudanya shi da ladabi.

hakika sarkin muminai ali (as) na cewa: madalla da ladabi abokin cudanyar hankali, gyaruwar hankali ladabi , kowanne abu na bukatuwa da hankali amma shi hankali ya na bukatuwa da ladabi , hankali ba zai amfanar ba idan babuu hankali , ladabi shi ne ciyar da kwakwale shi ne ribar hankula, lalleshi ladabi shi ne surar hankali lalle shi cikin mutum kamar bishiya ne hankali tushenta, kyawuntar hankali ado, babu ladabi ga wanda bai da hankali, lalle ladabi da addini ribar hankali ne, mafi falalar hankali ladabi , ladaubban malamai na yawaitar hankalinsu, lalle ma'abota hankula na da bukata zuwa ladabi kamar yadda shuka ke bukatar ruwan sama, duk wanda ladabinsa ya fifici hankalinsa shi kamar makiyayi ne tsakanin dabbobi masu tarin yawa.

wanan na nufin ladabi tu farkonsa wabatawa ne da kallafawa kai, sai dai bayan haka zai waya gari matsayin dabi'a da dan adam zaii dinga amfana da ita  cikin rayuwa da bayan mutuwarsa, lalle shi ladabi shi ne mafi alherin gadon da aka barwa al'ummun da za su zo daga baya.

na hudu: ilimi, hakika muslunci ya himmatu da da shi matukar himmatuwa , ta fuskanin zamani ya zama tilas ka ne mi ilimi tsaahon rayuwa daga ranar farko zuwa karshne numfashinka (( ku nemi ilimi tun daga zanin haihuwa zuwa kabari )) ta fuskanin wuri ka nemi a kowanne bigire cikin kasa kai hatta mafi nisa daga jazirar larabawa (( ku nemi ilimi ko kuwa a kasar sin (cana ) lalle shi ilimi farilla ne kan dukkanin musulmi da musulma.

( Allah na daukaka darajar wadanda sukayi imani daga cikinku da wadanda aka baiwa ilimi.

( shin wadanada suke da ilimi za su daidaita da wadanda bas u da shi.

shi ma'abocin hankali bai gajiya da kosawa cikin neman ilimi, mahandama biyu basa koshi mai neman ilimi da mai neman duniya, dole a nemi ilimi dare da rana, lalle shi Allah masani ne mai tarin sani ya na son ilimi da malamai nagargaru masu neman ilimi, lalle su mahari ne daga mazharorin iliminsa na azal madawwami, shi ilimi na taimakon mutum cikin samun ladabi da kyawawan dabi'u.

sarkin muminai ali (as) na cewa: idan ilimin mutum ya karu ladabinsa zai karu, tsoran allansa zai ninka.

imam sadik (as) ya ce : lalle mafi alherin abin da iyaye suka barwa 'ya'yansu shi ne ladabi ba dukiya ba, lalle ita dukiya na kareawa ladabi kuwa ya na wanzuwa.

daga cikin ribar ladabi kaifin basira, mutum sai ya zage dantse ya shirya neman ilimi fiye da waninsa.

sarkin muminai ali (as) ya na cewa: da ladabi a ke wasa basira, ka kara basirarka da kaifin kwakwalwarka don ka samu taimako da ita wajen neman ilimi da aiki da ladabi.

na biyar : tsoro , daga cikin ribar ilimi mai amafani shine tsoron Allah matsarkaki , lalle shi malami kowanne hali ya na tsakanin tsoro da fata , ya na tsorata aga zunubansa ya na fatan ubangijinsa , duk sanda ya karu cikin ilimi mai amfani sai kaga ya kru da tsoro ( kadan masu tsoron Allah daga bayinsa sune malamai ).                                    ilimi na haifar da tsoro.

hakika Allah ya cewa isa (as) : ka ladabtar da zuciyarka da tsoro .

wannan na nuni da cewa kowacce gaba jikin mutumna da ke bantattu ladubba, ladubban idanu kame su daga kallon haramun, harshe kama daga yin karya da alfasha da gulma da kafirci da dai misalinsu, ladabin kunne kamewa daga jin haramun, ladabin hannu da kafafu kayi tattaki da su cikin da'ar Allah, mutum bisa halayyarsa yana da ladubba kebantattu, ladubbansa tare da ubangijinsa  sun saba da ladubbansa da mutane, ya kamace ya kiyaye ladubban iayali da karamar al'umma zuwa babba, kamar ladabinsa cikin mahalllin iliminsa kamar makaranta da wurin aiki da dai makamantansu , majalisi n agama gari na da ladubbansa kebatattu, haka kebantacce majalisi shi ya na da nasa ladubban da ya kebanta da su, kowacce al'umma na da ladubbanta da sunnoninta da wayewarta kebance, duk wanda ke son ya zauna da wata kungiya to ya zama tilas ya kiyaye ladubbansu, kowanne abu bisa yadda ya ke, amma ladabin zuciya wadda it ace sarauniya kan jiki, idan ta gyaru ragowar gabobi zasu gyaru idan ta lalace za su lalace, idan malami ya lalace duniya sai ta lalace shi ne ma'anar fadin : iadan zuciya ta lalace duniya za ta lalace, gyaranta da ladabinta shi ne tsoron Allah matsrakaki, saboda haka ka ladabtar da zuciyarka da tsoron Allah.

na shida : zma da malamai, lalle muslunci ya umarce mu da mu zauna da malamai hatta mu cadanye su cikin neman ilimi, ka matsi malamai da gwiwowinka fadin lukmanu ga dansa, lalle zama da malamai na kawo tsira da azurta cikin gida biyu, wajen neman ilimi sarkin muminai ali (as) na cewa: ka zauna wajen malamai iliminka zai karu ladabinka zai kyawunta, abin nufi da malami anan shi ne wanda kallo zuwa gare shi ya kasance ibada shi ne wanda aikinsa ke gasgata fadinsa, idan ya umarce mutane daalheri to za a ganshi kai da farko lalle shi zai far aik da shi kafin umartar mutane, idan yayi hani da barin mummuna za a fara samunsa ya kwabu daga barinsa kafin ya umarci wasu, shi malamin da furucinsa ke kara maka ilimi ya kwadaitar da kai lahira kallonsa ya tunatar da kai Allah, shi ne wanda aka umarce mu da neman ilimi daga gare shi, idan bai da wadannan siffofi to ina.

idan kuka ga malami na neman duniya ku tuhume shi ka da k nemi addinku daga gare shi, lalle shi ya na cikin barayin kan hanya da addini ( mutum ya yi duba ya zuwa abincinsa ) 

imam bakir (as) ya na cewa: ma'ana ilimnsa daga wanda zai karbe shi

na bakwai : fahimta , da yawa ita fahimta ta fi kebanta daga ilimi ya zma tilsa mutum ya fahimci rayuwa ya riski sirrikanta don ya san kimarsa , da abin da ake nema daga gare shi da kan abin da ka halicce shi da manufar halittarsa ? ya zama tilas mu ladabtar da kawukanmu da fahimta

mu nemi taimakon ubangiji kan haka mu roke shi kamar yaddda iama zainul abiding (as) ka cewa Allah mu na rokonka ka sanya m daga cikin wadanda suka yi riko da igiyar ilimi suka ladabtar da kawukansu da fahimta.

 

 [1] Anfal:17

[2] Annajmu:3

[3] Fathu:10

[4] Nisa'i:80