فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

ASALAN LADUBBA

                       

Ya zama dole  akiyaye wadannan asalai wajen neman ladabi da tabbatar da shi:

Na farko:  kamewa daga miyagun siffofi da munanan dabi'u ko da kuawa hakan ya zamanto ta hanyar wa'azantuwar da waninka, hakika.

فإنّ أمير المؤمنين علي  7 يقول : (إذا رأيت في غيرک خلقآ ذميمآ فتجنّب من نفسک أمثاله

 sarkin muminai ali (as) ya na cewa : idan ka ga mummunar dabi'a daga waninka ka kaurace ma irinta daga cikin kanki kanka.

Wannan muhimmin asali daga ladabi.

لا تنهَ عن خُلُقٍ وتأتي مثله         عارٌ عليکَ إذا فعلتَ عظيمُ

Ka da kayi hani daga wata dabi'a amma kai kuma ka zakke ma irinta  abin kunya yak e kanka idan ka aikata wannan aiki mai girma.

Ya ishi mutum wa'azi ya wa'azantu da waninsa lalle shi mai hanakali shi ne wanda ya fadaka da wa'azantuwa daga waninsa, idan ya ga wani munkari daga waninsa to sai ya kauracewa shigensa cikin kankin kansa, ya tsiwirwiri ladubban da bai da su daga waninsa.

Lalle wannan ma'ana ta zo cikin kariin maganar farisawa: lalle ni na koyi ladabi daga wurin wanda bai da shi.

قيل لعيسى بن مريم  8: مَن أدّبک ؟ قال : ما أدّبني أحد، رأيت قبح الجهل

[1] فجانبته

An tambayi isa (as) waye ya ladabtar da kai ? sai ya ce: babu mutum guda da yay i mini ladabi, kadai nag a munin jahailci sai na kaurace masa.

وقال أمير المؤمنين علي  7: (كفاک أدبآ بنفسک اجتناب ما تكرهه من غيرک[2]

Sarkin muminai ali (as) ya ishe ka ladabi ga kanaka kauracema abin kake ki  daga waninka.

Na biyu: hakuri asasin kyawawan dabi'u cikin dukkanin marhalolinta uku: kauracewa daga siffofi munana, yin ado da kyawawan dabi'u, hakuri shi ne tajalli kuma shi sinadari ne na farko cikin ilimin kyawawan dabi'u daga nan kuma ladubba.

يقول أمير المؤمنين علي  7: (ليس شيء أحمد عاقبةً ، ولا ألذّ مغبّةً ، ولا أدفع لسوء الأدب ، ولا أعون على درک المطلب من الصبر).

Sarkin muminai ali (as) na cewa: babu wani mai kyakkyawan karshe da dadin abin nema da tunkude munana ladubba da mafi taimakawa kan cimma bukata kamar hakuri.

Na uku : bincike , lalle duk wamda ya nemi wani abu dole ne ya ne meshi da zage dantse har zuwa samunsa, ladubba na daga cikin ababen nemada himmatuwa da su.

قال الإمام علي  7: (لا يستعان على الدهر إلّا بالعقل ، ولا على الأدب إلّا بالبحث

Sarkin mumainai ali (as) ba a neman taimako kan zamani da komai face da hankali haka kan ladabi face da bincike.

وقال لقمان الحكيم : (مَن عني بالأدب اهتمّ به ، ومن اهتمّ به تكلّف علمه ، ومن تكلّف علمه اشتدّ طلبه ، ومن اشتدّ له طلبه ، أدرک منفعته فاتّخذه عادة ، فإنّک تخلف في سلفک وتنفع به من خلفک[3]

Lukmanu hakim ya ce: ( duk wanda ya damu da ladabi zai himmatu kansa, duk wanda ya himmatu da shi zai kallafawa kansa saninsa, duk wanda ya kallafawa kansa saninsa zai zage dantse kan nemansa,  duk wanda ya zage dantse nemansa zai riski amfaninsa ya rike shi al'ada, lalle kai z aka bar ma magadanka shi wadanda za su daga baya za su amfana da shi.

Na hudu:ilimi, hakika muslunci ya himmatu da batun ililmi matukar himmatuwa.

Ta fu bangaren lokaci ya zama dole mutum ya nemi ilimi tsawon rayuwarsa  tun dag ranar farko har zuwa karshen rayuwarsa, kamar yadda ya zo a hadisi: ku nemi ilimi tun dag shimfidar haihuwa har zuwa kabari, ta bangaren mahlli kuma to ka neme shi a kowanne bigire ka neme shi daga mafi nisan bigireb wanda shine jazirar larabawa(ku nemi ilimi ko da kuwa zuwa kasar sin ne) lalle shi ili,I wajibi kan dukkanin musulmi da musulma.

يَرْفَعِ اللهُ الَّذينَ آمَنوا منكُم وَالَّذينَ اُوتوا العِلْمَ دَرَجاتٍ )[4] ، و(هَلْ يَسْتَوي الَّذينَ يَعْلَمونَ وَالَّذينَ لا يَعْلَمونَ[5]

 Allah ya na daukaka wadanda suka yi imani cikinku da wadanda aka baiwa ilimi darajoji, shin yanzu masu ilimi za su daidaita da wadanda ba su da shi.
mutum mai hankali bai kosawa da neman ilimi bai gajiya, masu nema biyu basu koshi su ne mai neman ilimi da mai neman duniya.
Ya zama dole a zage dantse a nemi ilimi dare da rana, lalle ubangiji masani mai yawan sani ya na son ilimi da malamai nagargaru ma su neman ilimi, lalle su mabayyana ne daga mabayyanun iliminsa azali sarmadi.

Lalle ilimi na taimakon mutum kan neman ladabi da kyawawan halaye.

يقول أمير المؤمنين علي  7: (إذا زاد علم الرجل زاد أدبه ، وتضاعفت خشيته لربّه

Sarkin muminai Ali(as) ya ce: idan ilimin mutum ya karu sai ladabinsa ya karu. Tsoron Allah ya ninninka.

قال الإمام الصادق  7: (إنّ خير ما ورّث الآباء لأبنائهم الأدب لا المال ، فإنّ المال يذهب والأدب يبقى )، قال مسعدة : يعني بالأدب : العلم

Imam sadik(as) ya na cewa: mafi alherin abin da iyaye sukar barwa `ya`yayensu shi ne ladabi ba dukiya ba, lalle ita dukiya tana tafiya ta kare, ladabi kuma ya wanzu.

Daga cikin ribar ladabi kaifafa kwakwalwa, mutum ya damarar neman ilimi fiye da komai.

أمير المؤمنين  7: (بالأدب تُشحذ الفِطَن ، فزد في فطانتک وذكائک لتستعين بهما على طلب العلم والعمل به بالأدب

Sarkin muminai Ali(as) ka yi kari cikin basirarka da kaifafarka don ka samu taimako da su wajen samun ilimi da yin aiki da shi.

Na biyar:ganin girman ubangiji, lalle daga cikin ribar ilimi mai amfanihi ne ganin girman ubangiji da tsoronsa. Lalle shi malami ya na rayuwa tsakanin tsoro da fata, ma'ana ya tsorata daga zunubin da ya aikata ya na kuma fatan rahamar ubangiji , duk sa'ilin da ya karu da ilimi da aiki na nagari sai ya karu cikin tsoron Allah.

إنَّما يَخْشى اللهَ مِنْ عِبادِهِ العُلَماء[6]ُ

Kadai masu tsoron Allah da ganin girmansa daga bayinsa sune malamai.

Shi ilimi ya na haifar da ganin girman ubangiji da tsoronsa.

وقد قال الله تعالى لعيسى : أدّب قلبک بالخشية

Hakika Allah madaukaki ya cewa da isa (as) ka ladabtar da zuciyarka da tsoro

Wannan na nuni da cewa kowacce gaba ta na da kebantattun ladubbanta. Ladabin idaniya shi ne ka da ta kalli abin da Allah ya haramta, ladabin harshe ka da ya yi karya ka da ya furta alfasha ka ya  yi gulma ka da yay i kalmarn kafirci da dai sauransu…

Ladabin hannuwa da kafafuwa shi ne suyi kai kawao cikin da'ar Allah, kamar yadda mutum ya na da kebantattun laduba gwargawadon halinsa. Ladabinsa tare da ubangijinsa  ya banbanta daladabinsa tare da ragowar mutane , wajibi kansa ya kiyaye ladubban iyali da jama'a karama zuwa babba, kamar misalign ladabinsa cikin muhallin iliminsa kamar makaranta wajen aiki ma'aikata da dai sauransu…

Majalisin game gari na da ladabinsa a kebance, haka kebantacce majalisi na da ladabinsa , kowacce al'umma na da al'adunta da wayewarta, wanda ke son zama da wta kungiya ko wani aboki dole ya kiyaye ladubbansu, kowanne abu gwargwadon yadda ya ke, amma ladabin zuciya wadda ita zuciya it ace sarauniya ganagar jiki, idan ta gyaru ragowar gabobi za su gyaru, idan kuma ta lalace dukanin gabobi sun lalace, iadan malami ya lalce duniya za ta lalace, saboda haka gyaranta da ladabinta shi en jin tsoron Allah matsarkaki, ka ladabtar da zuciyarka da jin tsoron Allah.

Na shida:zama da malamai., lalle muslunci a wurare da dama ya umarce muda mu zauna da malamai mu matse su- ku masti malamai da gwiwowinku, kamar yadda luykmanu yak e fadawa dansa sa'ilin da yake masa nasiha – lalle zama da malamaina kawo stira da azurta a cikin gida biyu, game da neman ladubba:

يقول أمير المؤمنين علي  7: (جالس العلماء يزدد علمک ويحسن أدبک

Sarkin muminai Ali(as) na cewa: ka zauna da malamai iliminka zai karu ladabinka zai kyawunta.

Abin da ake nufi da malami wanda kallonsa ibada ne shi ne wanda zancensa ke gasgata aikinsa, aikinsa ya gasgata zancensa. Idan yay i umarni da aiki to shi za a fara samu kan gaba cikin wannan aiki haka idan yay i hna da barin mummuna aiki shi za'a fara samu ya bari, shi ne malamin furucinsa ke kara maka ilimi, aikinsa ya kara maka kwadayin lahira, ganinsa ya tunatar da kai Allah, shui ne wanda aka umarce mu da tsiwirwirar ilimi daga gare shi, iadan bah aka to iadan kuka ga malami ya fiye kwadayin duniyarsa bai aiki da iliminsa ku tuhume shi, ka da ku karbi addininku daga gare shi, lalle shi ya na daga cikin barayin masu tare hanya barawon addini,

فَلْيَنْظُرِ الإنْسانُ إلى طَعامِه[7]

mutum ya yi duba zuwa ga abincinsa.

Imam bakir(as) ya ce: ai yay i duba wajen wa zai dauki ilimi.

Malami mai takawa mai tsantseni wanda da z aka zauna da shi lalle ba makawa iliminka zai karu ladabinka ya karu.

Na bkwai:fahimta, da yawan lokuta fahimta tafi kebanta daga ilimi wani lokacin kuma ta kawance shi ta biyo bayansa, dole mutum ya ahimci rayuwarsa ya riski sirrikanta don ya ya san kimar kansa, ya kuma son mai ake nema daga gare shi don me aka halicci shi, mai manufar halittarsa,mu ne mi taimakon Allah mu roki Allah kamar yadda imam zainul abidin dan husaini(as) ya yi

اللّهم ... اجعلنا من الذين تمسّكوا بعروة العلم وأدّبوا أنفسهم بالفهم[8]

Allah ina rokonka ka sanya mu daga cikin wadanda suka yi riko da igiyarka suka ladabtar da kawukansu da fahimta.

Wanna na nufin mutum ba zai wadatu kadai da neman ladabi da ilimi da hakuri da kusantar malamai ba tilas sai ya cudanya da addu'a da tawassali da Allah, shi motsi daga mutum ya ke albarka kuma na wurin ubangiji, dole a samu wnai hannu na gaibu da zai dinga tallafawa mutum cikin motsinsa da tafiyarsa zuwa ga Allah matsarkaki da ado da falala da dabi'u masu karamci, muna rokon Allah ya sanya daga cikin wadanda suka yi riko da igiyar ilimi cikin dukkanin ayyukansu da zantukansu, suka ladabtar da kawukansu da fahimta da risker abubuwa da hakikani:

اللهمّ أرني الحقائق كما هي 

( Allah ka nuna mini hakikanin abubuwa kamar yadda suke )

na takwas : daga cikin alamomin mumii ya kasance mai gaskiya cikin maganganunsa da iliminsa tare da kansa da waninsa, lalle ita karya na daga cikin alamar munafiki, tushenta kuma kafirci, saboda haka ta yiwu mumini ya yi sata da zina sai dai cewa ba ya karya, Allah mai gaskiya kuma ya na tare da masu gaskiya, an umarce mu da mu kasance tare da masu gaskiya da kyawuntar dabi'u.

يقول أمير المؤمنين علي  7: (تحرّى الصدق وتجنّب الكذب ، أجمل شيمة وأفضل أدب

sarkin muminai ali (as) ya na cewa :ka yi bakin kokari kan bin gaskiya ka kauracea karya shi ne mafi kyawun hali da falalar ladabi.

ya kamace mu mu ladabtar da kawukanmu da gaskiya shi mumini karya ba fita daga bakinsa ko da sau daya.

na tara : tsare rai , lalle ita rai na umarni da mummuna kuma iata tana dabi'a irinta wuta duk sand aka bata abin da ta ke kwadayi ka biye ma sha'awarta sai ta nemi kari ta ce:

هل من مزيد[9]

 ( shin akwai kari )

 ya zama tilas mutum ya yiwa zuciyarsa iyaka ya ladabtar da ita da sanya mata linzami yayin kwadayinta, sarkin muminai ali (as) ya ce: iyakance zuciya yayin kwadayi da tsoro na daga cikin mafifitan ladubba.

na goma : kamewa daga aikata haramun, ita zuciya ba ta wadatuwa da halaliya  , lalle shaidani da miyagun abokai da duniya mai rudarwa suna jan mutum zuwa halaka da aikata haramun, mumini ma'abocin hankali ya zama dole ya ladabtar da kansa da kamewa daga haramun.

قال أمير المؤمنين علي  7: (ضبط النفس عند الرغب والرهب من أفضل الأدب

 lalle sarkin muminai ali (as) ya na cewa: mafi kyawun ladabi shi ne wanda ya kameka daga haramun.

وَأمَّا مَنْ خافَ مَقامَ رَبِّهِ وَنَهى النَّفْسَ عَنِ الهَوى فَإنَّ الجَنَّةَ هِيَ المَأوى[10]

(amma wanda ya ji tsoran tsayuwa gaban ubangijinsa ya hani zuciyarsa daga barin biyewa son rai lalle aljanna ce makomarsa )

وَأمَّا الَّذينَ سعدوا فَفي الجَنَّةِ خالدين فيه[11]ا

amma wadanda sukayi arziki suna aljanna suna masu dawwama ciknta.

Na sha daya : tsayawa bakin iyaka  daga cikin karin magana da ya shahara: kowanne abu idan ya wuce iyakarsa zai juya ya  zama kishiya

Ma'abocin hanakali ka aje abu a muhallinsa ba tare da wuce goda da iri ba ko takaitawa, kun kasance matsakaiciyar al'umma mafi alheri al'amura matsakaitanta, ya zama tilas kowa ya ladabci kansa ya tsaya iyakarsa ka da ya shallake ta ka da ya ketare iyakokin ubangiji ya zalunci kansa da waninsa , farin ciki ga wanda ya san mtumcinsa bai shallake iyakarsa ba.

المؤمنين علي  7: (أفضل الأدب أن يقف الإنسان عند حدّه ولا يتعدّى قدره ).

 sarkin muminai ali (as) ya na cewa: mafificin ladabi shi ne mutum ya tasaya bakin iyakarsa ka da ya ketare  iyakarsa .

Na sha biyu : watsi da abota da miyagun abokai, mutum cikin gaggawa yak e dabi'antuwa da dabi'un waninsa, idan ya zauna da mutanen kirki lalle zai samu alheri da kyawunta da daukaka halinsa ya gyaru , amma idan ya zauna da mutanen banza lalle zai tasirantu da da su ya zama abin tuhuma, lalle ka kauracewa wuraren tuhuma a na sanin mutum ta hanyar abokinsa, fada mini da wane ne ka ke abota ? zan fada maka wane ne kai, kan wannan

الإمام الصادق  7: (أدّبني أبي بثلاث . قال لي : يا بني ، من يصحب صاحب السوء لا يسلم ، ومن لا يقيّد ألفاظه يندم ، ومن يدخل مداخل السوء يتّهم[12] )[

 imam sadik (as) ke cewa : babana ya bani ladabi da abubuwa uku: ya ce mini: ya kai dana duk wanda ke abota da mugun aboki ba zai kubuta ba , duk wanda baiwa bakinsa linzami zai nadama, duk wanda ke kai kansa miyagun wurare za a tuhume shi.

وما أروع ما قاله الإمام الباقر  7، فإنّ المؤمن ملجم لا يتكلّم إلّا بما يرضي الله سبحانه من الذكر وقول الحقّ والنصيحة والموعظة وإرشاد الناس إلى الخير والصلاح والفلاح ، ومن الطبيعي أنّ مَن يدخل مواضع التهم ومداخل السوء أن يتّهمه الناس ، كما إنّ مَن عاشر أهل السوء والمنكر والفحشاء لا يسلم على نفسه ودينه وأهله وسمعته ، فلا بدّ أن نؤدّب أنفسنا بمثل هذه الآداب الإسلامية ونتجنّب مداخل السوء، ونقيّد ألفاظنا، ونجترّ الكلمات ولا نسرع ، فكثيرآ ما يندم الإنسان

 على كلامه ، ولا يندم على سكوته ، فإنّه إن كان الكلام من فضّة فالسكوت من ذهب ، وقد أفلح التقيّ الصموت . يقول أمير المؤمنين علي  7: (إذا فاتک الأدب فالزم الصمت [13]

Me ya fi kyawunta daga abin da imam bakir (as) ke fadi, lalle shi mumini cikin linzami yak e bai Magana sai cikin abin da Allah ya yarda daga zikiri da fadin gaskiya da nasiha da wa'azi da shiryara da mutane zuwa alheri da gyara da rabauta.

A dabi'ance duk wanda ya kai kansa miyagun wurare lalle muatne za su tuhume shi, haka duk wanda ya zauna da mutanen banza da munkari ma'abota alfasha ba zai kubutar da kansa da addininsa da mutuncinsa ba, ya zama tilas mu ladabtar da kawukan mu da ladubban muslunci mu kauracewa zakkewa miyagun wurare ababen tuhuma, muyi bakunan mu linzami, mu san mu zamu dinga cewa mu daina gaggawa da yawa mutum na nadama kana bin da ke fadi, amma bai nadama bisa yin shiru, lalle idan har zance daga azurfa ya ke to shiru zinariya ne, lalle ma'abocin takawa mai yawaita shiru ya rabauta.

 sarkin muminai ali (as) ya na cewa: idan ladabi ya fauce maka to lazimci shiru.

Na sha uku: himmatuwa da wajibai, kamar yadda wurgi da aikata haramun na daga cikin ladabi haka sauke wajibai babu banbanci cikin kasantuwarsu na shari'a ko al'adu, ita rayuwar mutum na tsakanin korewa da tabbatarwa cikin Kalmar tauhidi, babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, ita wannan Kalmar ta tattaro watsi da dukkanin abubuwan bautar ta kuma tabbatar da bautar Allah daya rak mabuwayi, daga cikin ladabin mutum kiyayewa da himmatauwa da sauke wajibai ka da ya dinga sakaci da ko in kula da abin da yak e larura ne kansa, kamar yadda

قال أمير المؤمنين علي  7: (ومن أدبه ـأي أدب الإنسان ـ أن لا يترک ما لا بدّ منه[14]

sarkin muminai ali (as) ke fadi: daga cikin ladabin mutum bai ya sakaci da abin da ya zame masa tilas.

Na sha hudu: tsarkake dabi'u, lalle ya na daga cikin ilimi mai amfani abin da ke wajabta tsarkake zukata da dabi'u kamar yadda

قال أمير المؤمنين علي  7: (سبب تزكية الأخلاق حسن الأدب

 sarkin muminai ali (as)  ya fadi : sababin tsarkakar dabi'u kyawuntar ladabi.

Akwai lazimci da alaka karfaffa ta yiwu ma ya kai ga kasantuwarsa cikakkiyar  illa da ta ke hukunci tsakanin tsarkake dabi'a da kyawuntar ladabi, wanda bai tsarkake dabi;unsa ta kaka ladabinsa zai zama ya kyawunta ? kadai dai mutum na samu tsira da fuffuka cikin sasannin karamci da daukaka da fuffuke biyu: fuffuken tsarkake zuciya da fuffuken kyawuntar ladabi.

Na sha biyar: kyawunta zamatakewa zamatakeawa na da na ta ladubban kebance, abin da ke tattara cikinta shi ne kyawuntar ladabi sakin fuska da dadada kalami da kyawunta ganawa cikin fagen abokantaka da kauna da makamantansu.

Hakikani shi ne kowanne daya daga cikinsu na da nasa ladubban a kebance kadai dai mu ambaci muhimmansu da asalnsu na farko da jiga -jigai, amma juz'ansu da masadik zamu fawwala hukunce hukuncnsu ga mai karatu zai iya fito da su daga abubuwan da muka ambata a baya wadanda suka dace da yanayinsa da inda ya ke rayuwa da al'ummarsa tare da wanda yak e mu'amala da shi, daga cikin muhimman ladubban zamatakewa  shi ne abin da

عن الشعبي قال : تكلّم أمير المؤمنين  7 بتسع كلمات ارتجلهنّ ارتجالا، فقأنَ عيون البلاغة وأيتمن جواهر الحكمة وقطعن جميع الأنام عن اللحاق بواحدة منهنّ ، ثلاث منها في المناجاة ، وثلاث منها في الحكمة ، وثلاث منها في الأدب 

 sarkin muminai ali (as) ya ce:

Daga sha'abi ya ce: sarkin muminai ali (as) ya fadi kalmomo tara take wadanada da su ya gutsure idaniyar balaga gwagwalan hikima sukai marici dukkanin mutane suka gaza risker daya daga cikinsu, uku daga cikin kalmomin munajati da ubangiji, uku daga ciki hikima, uku daga ciki ladabi:

 

(إلهي كفى بي عزّآ أن أكون لک عبدآ، وكفى بي فخرآ أن تكون لي ربّآ، أنت كما اُحبّ فاجعلني كما تحبّ ).

Amma wadanda ke ishara zuwa munajati ya na cewa: ubangijina ya ishene izza ace na kasance bawanka, ya ishe ni alfahari ka kasance ubangiji na , kai kamar yadda na ke so ka sanya ni kamar yadda ka ke so.

(قيمة كل امرئ ما يحسنه ، وما هلک امرؤ عرف قدره ، والمرء مخبوء تحت لسانه ).

 Ammma masu ishara ga hikima:

Kimar kowanne mutum abin da ke aikatawa, babu wani mtum da zai halaka matukar ya san iyakarsa, mutum na boye karkashin harshensa.

اُمنن على من شئت تكن أميره ، واحتج إلى من شئت تكن أسيره ، واستغنِ

[15] عمّن شئت تكن نظيره

Amma wadanda ke ishara ga ladabi kayi ni'ima ga wanda ka so zaka kasance sarkinsu, ka kafa hujja kan wanda ka so zaka zama daurarrensa, ka wadatu ga barin wanda ka so zaka zama  misalinsa.

an ce ladabi ya kasu kashi biyu : ladabin ruhi ladabin darasi, ladabin ruhi ya fi dauka kan na darasi kamar daukakar ruhi kan gangar jiki , saboda shi ladabin darasi ya na amfanarwa bai cutarwa , ladabin darasi ba tare da na ruhi ba baya kasancewa daga hankali kadai dai ya na gudana magudanar misalin tarbiyar da kewa dabbobi irinsu biri da giwa.

Jahadin zuciya na daga mafi girman jihadi

وَالَّذِينَ جَاهَدُوا فِينَا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَـنَ[16]ا

 ( wadanda su kayi kokari cikin neman yardarmu lalle za mu shiryar da su hanyoyinmu)

 

 

 

 [1] Biharul anwar m 14 sh 326

[2] Masdarin da ya gabata m 70 sh 573

[3] Biharul anwar m 13 sh 411

[4] Mujadala:11

[5] Zumar:9

[6] Fadir:28

[7] Abasa:24

[8] Biharul anwar m 94 sh 127

[9] Kaf:30

[10] Annazi'at:40

[11] Hudu:108

[12] Biharul anwar m 78 sh 261

[13] Biharul anwar m 71 sh 293

[14] Biharul anwar m 78 sh 400

[15] Biharul anwar m 77 sh 400

[16] Ankabut:69