sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • MAULIDIN IMAM HASSAN ASKARI
 • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
 • MUNA MIKA TA’AZIYA GA DAUKACIN GURGUZUN AL’UMMAR MUSULMI BISA SHAHADAR IMAM ALIYU IBN MUSA ARRIDA (A.S)
 • TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S
 • SABUWAR SHEKARAR MUSLUNCI 1441 TARE DA DAWOWA KARATU DAGA RANAR ASABAR 14 GA WATAN MUHARRAM
 • BAYANI DANGANE DA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAM SHEKARA TA 1441 H
 • BAYANI KAN MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAHAM SHEKARA 1441 H KASHI NA (2)
 • BAYANI NA FARKO (1) BISA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAMAN SHEKARA 1441 H
 • TASHAR KARBALA IRFAN ZASU WATSA LACCOCIN ASHURA NA SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Suldanul Nufus Aliyu bn Musa Arrida (as)
 • Makalar Hubbun Nisa’i fi Hadisun Nabawi ta fito- tare da Alkamalin Assayid Adil-Alawi
 • Makalar Annaji Bashar Mau’udul Muntazar ta fito tareda Alkalamin Assayid Adi
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jafar bn Muhammad
 • Makalar duba li mushatulArba’in tareda Alkalamin Assayid Adil-Alaw
 • Allah ya girmama ladan ku da na mu bisa musibar rashin Sarkin muminai Ali (as)
 • Tunawa da Ranar haihuwar Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin Amincin Allah ya tabbata a gare shi
 • Maulidin Abul Fadlul Abbas bn Ali (as) and akewa lakabi da Kamaru Banu Hashim mai shayar masu kishi a Karbala
 • Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
 • Ranar asabar 14 ga watan Rabi’u Awwal Assayid Adil-Alawi (h) zai cigaba da bada darasin bahasul karij
 • muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar da aka haifi Imam Hassan Askari (as)
 • Labarun da ba tsammani

  Labarai wanda akafi karantawa

  Tunawa da zaluncin da akaiwa Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata gareta wacce itace farko wacce ta fara riskar manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata gareshi tare da-alkalamin sayyid Adil-Alawi

   

  Lallai wannan madaukaki hadisi yana nuni kan zaluncin da akaiwa Ahlil-baiti kamar yadda yake nuni zuwa ga cewa kadai dai wanda zai zaluncesu yana daga mafi sharrin al’umma bayansa, lallai su sun juya bayansu duniya ta rude su, sun sayar da lahirarsu da mafi kaskantar farashi, sai sukai hasara biyu hasarar duniya da lahira lallai wancananka shine hasara mabayyaniya.

  Hakama ya nuni kan halascin kuka kan musibar da ta afku kan Ahlil-baiti (as) sannan ya nuna zuwa ga kebantacciyar daraja daga kebantattun darajojin sayyada Zahara (as) lallai itace ta farkon wacce zata fara riskar manzon Allah (s.a.w) a gidan lahira daga Ahlin gidansa. Ya zo cikin littafin bihar daga littafin dala’ailul imama na muhammadu bn jariri dabari dan imamiyya:

  عن أبي المفضّل الشيباني ، عن محمّد بن هاشم ، عن أحمد بن محمّد البرقي ، عن أحمد بن محمّد بن عيسى بسنده عن أبي بصير عن أبي عبد الله 7 قال : «ولدت فاطمة في جمادي الآخرة اليوم العشرين منها سنة خمس وأربعين من مولد النّبي  6، فأقامت بمكّة ثمان سنين وبالمدينة عشر سنين ، وبعد وفاة أبيها خمساً وسبعين يوماً، وقبضت في جمادي الآخرة يوم الثلاثاء لثلاث خلون منه سنة إحدى عشرة من الهجرة »[1

  Daga Mufaddal shaibani daga Muhammad bn Hashim daga Ahmad bn Muhammad Albaraki daga Ahmad bn Muhammad bn Isa da isnadinsa daga Abu basiru daga Abu Abdullah (as) ya ce: ana haifi Fatima ishirin ga watan jimada akhar shekara arba’in da biyar da haihuwar annabi (s.a.w) sai ta zauna a makka shekaru takwas a madina kuma shekaru goma, sannan ta rayu bayan babanta kwanaki saba’in, Allah ya karbi ranta ranar talata uku ga watan jimada akhar hijira nada shekaru goma sha daya

  A wani hadisin kuma ta rayu a bayansa kwanaki casa’in da biyar shi’ar masu karamci cikin wannan zamani suna tattara dukkanin zantuka biyu cikin tsayar da taron bikin makokin shahadarta suna raya uku daga sha ukun jimada ula da kuma kwanakin ukun farkon jimada sani.

  Allah ya saka musu da alheri lallai raya makoki yana daga ibadun Allah  

  ومن يعظّم شعائر الله فانّها من تقوى القلوب .

  Duk wanda ya raya ibadun Allah lallai ita tana daga takawar zuciya.

  Domin neman Karin bayani zaku iya komawa abin da samahatus sayyid Adil-Alawi (h) ya rubuta  mai taken kasa’isus fatimiyya ala dau’il saklaini.