sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • MAULIDIN IMAM HASSAN ASKARI
 • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
 • MUNA MIKA TA’AZIYA GA DAUKACIN GURGUZUN AL’UMMAR MUSULMI BISA SHAHADAR IMAM ALIYU IBN MUSA ARRIDA (A.S)
 • TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S
 • SABUWAR SHEKARAR MUSLUNCI 1441 TARE DA DAWOWA KARATU DAGA RANAR ASABAR 14 GA WATAN MUHARRAM
 • BAYANI DANGANE DA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAM SHEKARA TA 1441 H
 • BAYANI KAN MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAHAM SHEKARA 1441 H KASHI NA (2)
 • BAYANI NA FARKO (1) BISA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAMAN SHEKARA 1441 H
 • TASHAR KARBALA IRFAN ZASU WATSA LACCOCIN ASHURA NA SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Suldanul Nufus Aliyu bn Musa Arrida (as)
 • Makalar Hubbun Nisa’i fi Hadisun Nabawi ta fito- tare da Alkamalin Assayid Adil-Alawi
 • Makalar Annaji Bashar Mau’udul Muntazar ta fito tareda Alkalamin Assayid Adi
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jafar bn Muhammad
 • Makalar duba li mushatulArba’in tareda Alkalamin Assayid Adil-Alaw
 • Allah ya girmama ladan ku da na mu bisa musibar rashin Sarkin muminai Ali (as)
 • Tunawa da Ranar haihuwar Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin Amincin Allah ya tabbata a gare shi
 • Maulidin Abul Fadlul Abbas bn Ali (as) and akewa lakabi da Kamaru Banu Hashim mai shayar masu kishi a Karbala
 • Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
 • Ranar asabar 14 ga watan Rabi’u Awwal Assayid Adil-Alawi (h) zai cigaba da bada darasin bahasul karij
 • muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar da aka haifi Imam Hassan Askari (as)
 • Labarun da ba tsammani

  Labarai wanda akafi karantawa

  Muna daukaka mafi daukakar ayoyin taya murna da farin ciki zuwa ga mukamin manzon Allah (s.a.w) da Ahlin gidansa tsarkaka aminicin Allah ya kara tabbata a gare su baki dayansu dangane da munasabar mauludin imam Bakir (as)  Muna daukaka mafi daukakar ayoyin taya murna da farin ciki zuwa ga mukamin manzon Allah (s.a.w) da Ahlin gidansa tsarkaka aminicin Allah ya kara tabbata a gare su baki dayansu dangane da munasabar mauludin imam Bakir (as)


  Idan musibu sun tsananta kanka to ka dadada rayuwarka mara dadi da mai danne fushi Musa da Jawad muhammad, ya kai mai kudurin ziyara nufi yamma daga wadancan matsugunai domin kayi tuntube da aminta da aminci ka kwadaitar da ayari idan suna bukatar samun nasara, kayi dawafi mai yalwa ka ziyarce ta ka amsa kira ka yi sallama cikin zuciyarka da kan fatar bakinka ta haskakar ya yin da kira ya zo daga sama cewa har abada ba zakat aba ganina ba wancan wuta haske ne na Allah cikinta ka cire fadenka (takalmanka) biyu ka Kankan da kai idan kubbobi biyu suka bayyanu gabanka, na rantse da mai rike da rayuwarka karkashinwannan kubbobi guda biyu wutar Musa take da hasken Muhammad suna masu kusantar juna da makotaka da juna. و

  Muna daga mafi daukakar murna da taya farin ciki da murna ga mukamin manzo mafi girma (s.a.w) da Ahalin gidansa amincin Allah ya kara tabbata garesu haka ma ga mukamin bakiyatullah fi ardihi rayukanmu fansar takun kurar kafarsa haka ma ga baki dayan al'ummar musulmi da muminai mazansu da matansu ga malamanmu  masu girma dangane da munasabar zagayowar ranar haihuwar imam jawad amincin Allah ya kara tabbata gareshi.

  Daga cikin hikimomin imam Jawad (as)

  قال (عليه السلام ) :
  ((من وثق بالله أراه السرور ، ومن توكل عليه كفاه الأمور و الثقة بالله حصن لا يتحصن فيه إلا مؤمن أمين و التوكل على الله نجاة من كل سوء و حرز من كل عدو و الدين عز و العلم كنز و الصمت نور و غاية الزهد الورع و لا هدم للدين مثل البدع و لا أفسد للرجال من الطمع و بالراعي تصلح الرعية و بالدعاء تصرف البلية و من ركب مركب الصبر اهتدى إلى مضمار النصر و من عاب عيب و من شتم أجيب و من غرس أشجار التقى اجتنى ثمار المنى )) 

  Amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: (duk wanda ya yarda da Allah zai nuna masa farin ciki, duk wanda ya dogara da shi zai isar masa cikin al'amurra, shi yarda da Allah karfaffen shinge babu mai fakewa cikinsa sai mumini amintacce shi tawakkali da Allah tsira ne daga dukkanin mummuna hirji ne daga dukkanin makiyi addini kuma izza ce ilimu taskace yin shiru haske ne magaryar tukewar zuhudu tsantseni, babu abin da yake rushe kamar misalin bidi'oi, babu abin da ke lalata mazaje da gurbata su kamar misalin kwadayi, da shugaba ne mabiya ke gyaruwa, da addu'a musibu ke tunkudewa, dukkanin wanda ya hau dokin hakuri ya shiriya zuwa ga fagen sukuwa dukkanin wanda ya aibata shima ya aibatu dukkan wanda ya yi zagi an amsa masa, dukkanin wanda ya shuka bishiyar tsoran Allah zai tsoni kayan marmarin burace-burace.

   
  قال ( عليه السلام ) :

  (( من أمل إنسانا فقد هابه و من جهل شيئا عابه و الفرصة خلسة و من كثر همه سقم جسده و المؤمن لا يشتفي غيظه و عنوان صحيفة المؤمن حسن خلقه))

  شةهamincin Allah ya kara tabbata gareshi ya ce: ( dukkanin wanda ya yi fata daga mutum to hakika ya kwarjantar da shi dukkanin wanda ya jahilci wani abu ya aibata ita dama abu ne da yake boye yake zuwa ba zato ba tsammani, dukkanin wanda damuwarsa ta yawaita jikinsa zai rashin lafiya mumini fushinsa bai karewa, taken littafin mumini takardarsa kyawuntar halayensa.

   قال عليه السلام :
  (( العلماء غرباء لكثرة الجهال بينهم ))

  Amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: ( su malamai baki ne sakamakon yawaitar jahilai tsakankaninsu)


  قال عليه السلام :
  ((لو سكت الجاهل ما اختلف الناس )) . 

  Amincin Allah ya tabbata gareshi ya ce: ( da jahili zai yi shiru da mutane ba suyi sabani da juna ba)


  قال (عليه السلام )
  ((لا يفسدك الظن على صديق و قد أصلحك اليقين له و من وعظ أخاه سرا فقد زانه و من وعظه علانية فقد شانه استصلاح الأخيار بإكرامهم و الأشرار بتأديبهم و المودة قرابة مستفادة و كفى بالأجل حرزا و لا يزال العقل و الحمق يتغالبان على الرجل إلى ثماني عشرة سنة فإذا بلغها غلب عليه أكثرهما فيه و ما أنعم الله عز و جل على عبد نعمة فعلم أنها من الله إلا كتب الله جل اسمه له شكرها قبل أن يحمده عليها و لا أذنب ذنبا فعلم أن الله مطلع عليه إن شاء عذبه و إن شاء غفر له إلا غفر الله له قبل أن يستغفره))

  Amincin Allah ya tabbata gareshi ya ce: (ka da zato ya lalataka kan aboki bacin yakini ya kyawuntaka gareshi, dukkan wanda ya yiwa dan'uwansa wa'azi a boye hakika ya yi mas ado dukkan wanda ya yi masa a bayyane hakika ya muzanta shi, mutanen kirki sun gyarantu ne da karamcinsu mutanen banza kuma sun gyaru ne ta hanyar ladabtar da su, kauna kusanci ce abar fa'idantuwa, Ajali ya isa zama hirzi, hankali da wauta basu gushe ba suna mubalaga da juna suna rigima da juna kan mutum har zuwa shekaru 18 idan ya kai wannan shekaru sai dayansu da yafi yawaita cikinsa ya yi galaba kansa, Allah bai taba ni'imta wani bawa da wata ni'ima sai bawan ya san cewa daga Allah take face Allah ya rubuta masa godiyarta gabanin ya gode masa kanta, bawa bai taba aikata wani zunubi ba sai ya san cewa Allah yana tsinkaya kansa kuma idan ya so zai iya yi masa azaba ko yafe masa face Allah ya gafarta masa gabanin neman gafarar Allah kan zunubin)

   قال (عليه السلام ) 
  (( الشريف كل الشريف من شرفه علمه و السؤدد حق السؤدد لمن اتقى الله ربه و الكريم من أكرم عن ذل النار وجهه )) 

  Amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: (madaukaki dukkan madaukaki shi ne wanda Iliminsa ya daukaka shi, shugabanci hakikar shugabanci na ga wanda yaji tsoran ubangijinsa karimi shi ne wanda ya karrama fuskarsa daga kaskancin wuta)