sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • MAULIDIN IMAM HASSAN ASKARI
 • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
 • MUNA MIKA TA’AZIYA GA DAUKACIN GURGUZUN AL’UMMAR MUSULMI BISA SHAHADAR IMAM ALIYU IBN MUSA ARRIDA (A.S)
 • TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S
 • SABUWAR SHEKARAR MUSLUNCI 1441 TARE DA DAWOWA KARATU DAGA RANAR ASABAR 14 GA WATAN MUHARRAM
 • BAYANI DANGANE DA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAM SHEKARA TA 1441 H
 • BAYANI KAN MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAHAM SHEKARA 1441 H KASHI NA (2)
 • BAYANI NA FARKO (1) BISA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAMAN SHEKARA 1441 H
 • TASHAR KARBALA IRFAN ZASU WATSA LACCOCIN ASHURA NA SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Suldanul Nufus Aliyu bn Musa Arrida (as)
 • Makalar Hubbun Nisa’i fi Hadisun Nabawi ta fito- tare da Alkamalin Assayid Adil-Alawi
 • Makalar Annaji Bashar Mau’udul Muntazar ta fito tareda Alkalamin Assayid Adi
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jafar bn Muhammad
 • Makalar duba li mushatulArba’in tareda Alkalamin Assayid Adil-Alaw
 • Allah ya girmama ladan ku da na mu bisa musibar rashin Sarkin muminai Ali (as)
 • Tunawa da Ranar haihuwar Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin Amincin Allah ya tabbata a gare shi
 • Maulidin Abul Fadlul Abbas bn Ali (as) and akewa lakabi da Kamaru Banu Hashim mai shayar masu kishi a Karbala
 • Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
 • Ranar asabar 14 ga watan Rabi’u Awwal Assayid Adil-Alawi (h) zai cigaba da bada darasin bahasul karij
 • muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar da aka haifi Imam Hassan Askari (as)
 • Labarun da ba tsammani

  Labarai wanda akafi karantawa

  muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar da aka haifi Imam Hassan Askari (as)


     an haifi Imam Abu Muhammad Hassan Askari (as) 8 ga watan Rabi’u sani hijira na da shekara 232 a birnin mai Madina  wannan ra’ayi da akasarin malamamn tarihi suka tafi kai, ana kiran Imam Hassan da Imam Aliyu annakiyu (as) da lakabin Askariyaini sakamakon a nan ne mahallin da suka zauna cikin samarra, Ibn Sukaitu ya tambayi Imam Hadi sakamakon umarnin sarkin Mutawakkil yana mai fadin cewa: mene ne ya sanya Allah ya aiko Musa (as) da sanda, ya kuma aiko Ida da warkar da kutare da makafi da raya matattu, sannan ya aiko Muhammad da kur’ani da takobi?

  Sai Imam Hadi ya bashi amsa da fadin Allah madaukaki: ( Allah maduakaki ya aiko Musa da sanda da hannu mai haske da take bayyana ba tareda wahala a cikin zamanin sihiri yake kan tashensa a lokacin matsafa da masu sihiri sunyi matukar tasiri cikin kwakwalen mutane da tunaninsu lamarin da ya kai ga karkacewarsu daga barin hanyar Allah-hanyar gaskiya hanyar shiriya, sai Musa ya zo da abinda yake ruguje da’awowinsu shine sandarsa da ta kasance tana hadiye abinda suke kag, sannan cikin hujja ya tabbatar da abinda ya rushe da’awowinsu da karerayinsu, amma wazifar Isa ta saba da Musa saboda kasantuwar zamanin Musa abin da ya shahara shine cigaban likitanci, sai ya zo musu da mu’ujiza da ta gagare su ya tabbatar musu da gazawarsu, domin sun kasance suna warakar da mutane daga cututtuka sai dai tare da hakan sun gaza warakar da kuturu da makaho, sai Annabi Isa yayi musu kalubale, ta yand aya kasance ya na shafa kutare da makafi da hannunsa sai su warke da izinin Allah, sannan bugu da kari ya zo da abinda kowa da kowa ya gaza kansa shine raya matattu da izinin Allah, hakika ya kasance yana tashin matattu da umarnin Allah lokacin da yake addu’a lamarin da ya sanya shi zama mai nasara da galaba kan su cikin fagen munazara da jidali.

  Amma aiko da manzon Allah Muhammad (s.a.w) to shi a lokacinsa abinda yake tashe shine wake-wake da fasaha da kuma takobi don daukakar kai da izza da kabilanci da alfahari da karamci da al’adunsu, sai ya zo musu da mafi girman mu’ujiza, ya rusa dukkanin da’awowinsu da hujjojinsu da ayoyi manzanci bayyanannu, kuma balagar manzo da rawar da ya taka mai girma cikin isar da sako da nusantarwa. Kuraishawa sun bi hanyoyi daban-daban da dukkanin dabaru domin taka birki ga yaduwa sakonsa da bunkasarsa sai dia cewa ba su yi nasara ba yayin da kur’ani ya kalubalance su da su zo da surori ko kuma sura guda daya rak ko da kuwa zasu tallafi junansu cikin hak, lamarin da ya sanya su fagarniya cikin amfani da nuna karfi da cutarwa sai dia cewa hakan bai amfanar da komai ba, Allah madaukaki yana cewa:   

   [واللَّهُ مُتِمُّ نُورِهِ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ]

   

  Allah zai cika haskensa ko da kuwa kafirai basa so.